عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَكْثِرُوا ذِكْرَ هَادمِ اللَّذَّاتِ» يَعْنِي الْمَوْتَ.
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ku yawaita tina mai rushe jin daɗi". Yana nufin mutuwa.
Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah ne Suka Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan yawaita tinanin mutuwa, da tinaninta ne mutum yake tuna lahira, kuma soyayyarsa ga duniya ta rushe a cikin zuciyarsa, musammanma dai abubuwan da aka haramta.
Fa’idoji
- Mutuwa tana yanke jin daɗin duniya, sai dai a haƙƙin mumini tana dago shi zuwa jin daɗin lahira da jin daɗin aljanna da abinda yake faruwa a cikinta na alheri mai girma.
- Tina mutuwa da abinda ke bayanta yana daga sabubban tuba da barin laifi da kuma tanadi dan lahira.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 141) (2307). سنن النسائي (4/ 4) (1824). سنن ابن ماجه (5/ 326) (4258). ذخيرة العقبى في شرح المجتبى (18/ 219).