Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ya Allah babu wata rayuwa sai rayuwar lahira, ka gafartawa Mutanen Madina da waɗanda suka yi hijira

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضيَ اللهُ عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ قَالَ: «اللهُمَّ لَا عَيْشَ إِلَّا عَيْشُ الْآخِرَهْ، فَاغْفِرْ لِلْأَنْصَارِ وَالْمُهَاجِرَهْ».
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ya Allah babu wata rayuwa sai rayuwar lahira, ka gafartawa Mutanen Madina da waɗanda suka yi hijira».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wata rayuwa ta haƙiƙa sai rayuwar lahira, a cikin yardar Allah da rahamarSa da kuma aljannarSa; domin rayuwar duniya mai gushewa ce, rayuwar lahira kuwa ita ce dawwamammiya mai wanzuwa, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'ar gafara da girmamawa da gyaruwa ga mutanen Madina waɗanda suka kawo ɗauki ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Muhajirun, suka taimakesu, suka raba musu dukiyoyinsu, kuma (ya yi addu'a) ga Muhajirun waɗanda suka bar gidajensu da dukiyoyinsu suna neman falala daga Allah da kuma yarda.

Fa’idoji
  1. Gudun duniyarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a duniya da kuma fuskantowarsa ga lahira.
  2. Gargaɗawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa a jin daɗin rayuwar duniya mai gushewa.
  3. Bayanin darajar Muhajirai da Ansar, inda suka rabauta da addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agareshi - garesu da gafara.
  4. Kada bawa ya yi farin ciki da abinda yake samu na duniya, ita mai saurin gushewa ce tare da abinda ke cikinta na gurɓacewa, kaɗai gidan tabbata shi ne gidan lahira.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 88) (6413). صحيح مسلم (3/ 1431) (1805). مرقاة المفاتيح، لعلي القاري (7/ 3016). فتح الباري شرح صحيح البخاري، لابن حجر (11/ 231). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 362). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (7/ 223). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 529). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 412).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ZARGIN SON DUNIYA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com