Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Ku saurara lallai cewa duniya tsinanniya ce, kuma abinda ke cikinta ma tsinanne ne, sai ambatan Allah da abinda ke jiɓintarsa da malami ko mai neman ilimi

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضيَ اللهُ عنهُ سمعتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يقولُ: «أَلاَ إِنَّ الدُّنْيَا مَلْعُونَةٌ، مَلْعُونٌ مَا فِيهَا، إِلاَّ ذِكْرُ اللهِ وَمَا وَالاَهُ وَعَالِمٌ أَوْ مُتَعَلِّمٌ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Ku saurara lallai cewa duniya tsinanniya ce, kuma abinda ke cikinta ma tsinanne ne, sai ambatan Allah da abinda ke jiɓintarsa da malami ko mai neman ilimi".
Tirmizi ne ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa duniya da abinda ke cikinta abin ƙine a wurin Allah abin zargi abin bari abin nisantarwa, kuma abinda ke cikinta abin bari ne ba abin yabo bane; dan kasancewarta da dukkan abinda ke cikinta yana shagaltarwa daga barin Allah, kuma yana nisantarwa daga gare shi, saidai ambatan Allah da abinda ya kusance shi ya zama yana da jinsi da shi, cikin abinda Allah Ya so shi, ko masanin ilimi na shari'a wanda yake koyar da mutane, ko mai neman ilimin shari'a ɗin.

Fa’idoji
  1. La'antar duniya ba ta halatta kai tsaye; dan zuwan hadisan da suke hani daga hakan, saidai la'antar abinda ke nisantarwa daga Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinta kuma yake shagaltarwa daga biyayyrSa to yana halatta.
  2. Dukkan abinda ke cikin duniya to wasa ne kuma shagala ne sai ambatan Allah da abinda yake sababi kuma mai taimako a cikin hakan.
  3. Bayanin falalar ilimi da ma'abotansa da kuma ɗalibansa.
  4. Ibnu Taimiyya ya ce: Kaɗai ana zargin haramun ne bata fuskarsa ba, ko halal ta hanyar neman yawaitawa da alfahari, da abinda ake riƙa dan nufin fariya da gasa, to wannan shi ne wanda yake abin ƙi gurin masu hankali.
Madogara

سنن الترمذي (4/ 151) (2322). سنن ابن ماجه (5/ 231) (4112). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 542). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 424). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (7/ 325). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (3/ 374).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ZARGIN SON DUNIYA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com