عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسْعُودٍ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لاَ تَتَّخِذُوا الضَّيْعَةَ فَتَرْغَبُوا فِي الدُّنْيَا».
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku riƙi gona sai ku yi kwaɗayin duniya".
Tirmizi da Ahmad sun rawaito shiDarajaHasan ne da wani Sanadin
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga riƙon gona; domin hakan yana daga sabubban kwaɗayi a duniya da karkata zuwa gareta abar lahira.
Fa’idoji
- Hani akan yawaita neman duniya da abinda yake kaiwa zuwa juyawa lahira baya.
- A cikin hadisin babu hani daga riƙon binda yake akwai abin samun rayuwa daga gare shi, kaɗai hani ne daga dulmiya a cikin duniya da kuma mantawa da lahira.
- Sindi ya ce: Abin nufi: Kada ku zirfafa a cikin riƙon gona sai ku shagalta da ita daga ambatan Allah.
Madogara
سنن الترمذي (4/ 155) (2328). مسند أحمد (6/ 54) (3579). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (331/7). شرح رياض الصالحين لابن عثيمين (375/3).