Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Matsayina da duniya, ni a cikinta ba komai bane sai kamar matafiyi ne akan abin hawa da ya sha inuwa a ƙarƙashin wata bishiya sannan ya tafi ya barta

عَنْ عَبْدِ اللهِ بنِ مَسْعُودٍ رَضيَ اللهُ عنهُ قَالَ: نَامَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى حَصِيرٍ، فَقَامَ وَقَدْ أَثَّرَ فِي جَنْبِهِ، فَقُلْنَا: يَا رَسُولَ اللهِ، لَوِ اتَّخَذْنَا لَكَ وِطَاءً، فَقَالَ: «مَا لِي وَلِلدُّنْيَا، مَا أَنَا فِي الدُّنْيَا إِلاَّ كَرَاكِبٍ اسْتَظَلَّ تَحْتَ شَجَرَةٍ ثُمَّ رَاحَ وَتَرَكَهَا».
Daga Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi bacci akan wata tabarma, sai ya tashi haƙiƙa ta yi masa tabo a gefensa, sai muka ce: Ya manzon Allah, inama dai a ce mun yi shimfiɗa saboda kai, sai ya ce: "Matsayina da duniya, ni a cikinta ba komai bane sai kamar matafiyi ne akan abin hawa da ya sha inuwa a ƙarƙashin wata bishiya sannan ya tafi ya barta".
Tirmizi ne ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Abdullahi ɗan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ambaci cewa annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi bacci akan shimfiɗa ƙarama wacce aka saƙata da wasu daga tsirrai, sai ya miƙe alhali tabarmar ta yi tabo a fatar gefensa, sai muka ce: Ya manzon Allah, ina ma dai a ce mu yi maka wata shimfiɗa mai laushi da hakan ya fi kyau daga kwanciyarka akan wannan tabarmar mai kaushi, sai (annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ni bana son sabo da duniya har in yi kwaɗayi a cikinta, kwatankwacina da wanzuwa a cikin duniya bai zama ba sai kamar wani matafiyi ne da ya sha inuwa ƙarƙashin wata bishiya sannan ya tafi ya barta.

Fa’idoji
  1. Bayanin abinda annabi - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - yake akansa na gudun duniya da bijire mata.
  2. A cikin Hadisin babu barin abinda babu makawa gare shi na duniya, kawai shagalta da ita ne akan lahira, domin mutum ya sha inuwar bishiya kuma ya fa'idantu da ita saboda isarsa, bai kuma karkata zuwa gareta ba.
  3. Yin izina da halin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, domin cewa shi ne koyi mai kyau, kuma cewa wanda ya bi sawunsa to ya shiriya, kuma ya rabauta a duniya da lahira.
  4. Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - da kuma soyayyarsu gare shi.
  5. Halaccin buga misalai a cikin Da'awah da kuma koyarwa.
Madogara

سنن الترمذي (4/ 166) (2377). سنن ابن ماجه (5/ 229) (4109). النهاية في غريب الحديث والأثر (979). فيض القدير (5/ 464). تطريز رياض الصالحين (ص: 326). البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (34/ 663).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ZARGIN SON DUNIYA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com