Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE

Hadisai 79

Wanda ya je wurin Ɗan duba (malamin duba) ya tambaye shi wani abu, to, ba za a karɓi Sallarsa ta darare arba’in ba

عن بعض أزواج النبي صلى الله عليه وسلم عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ أَتَى عَرَّافًا فَسَأَلَهُ عَنْ شَيْءٍ لَمْ تُقْبَلْ لَهُ صَلَاةٌ أَرْبَعِينَ لَيْلَةً».
Daga wasu cikin matan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: Wanda ya je wurin Ɗan duba (malamin duba) ya tambaye shi wani abu, to, ba za a karɓi Sallarsa ta darare arba’in ba.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana tsoratarwa a kan zuwa wurin mai duba -suna ne fitacce na boka, da mai taurari, mai zane a kasa da makamantansu, irin wanda yake kafa dalilin sanin gaibu ta hanyar wasu abubuwa na farko-farkon lamari- zallar tambayarsa a kan wani abu na gaibu, zai haramta masa ladan sallah na kwanaki arba’in, wannan uƙuba ce, a kan wannan laifi, kuma zunubi ne mai girma.

Fa’idoji
  1. Haramcin bokanci, da zuwa wurin boka da kuma tambayarsu gaibu.
  2. Tabbas ana hanawa mutum ladan biyayya don ya zama uƙuba a gare shi a kan aikata laifi.
  3. Yana shiga cikin wannan Hadisin abin ake cewa burji da duba shi, da karanta tafin hannu, da ƙwarya, ko da kuwa leƙawa ne kaɗai, domin duka yana cikin bokanci, kuma yana cikin iƙirarin sanin gaibu.
  4. Idan wannan ya zama sakamakon wanda ya je wurin mai duba, to, ya ya halin shi mai duban.??
  5. Sallar kwanaki arba’in idan ya yi ba ta yi ba, kuma ba zai rama ta ba, saidai babu ladanta.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 1751) (2230). مسند أحمد (27/ 197) (16638). الجديد في شرح كتاب التوحيد، للقرعاوي (ص238). الملخص في شرح كتاب التوحيد، للفوزان (ص213).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kana ganin idan na sallaci salloli wadanda aka wajabta, na azimci watan Ramdan, na halatta halal, na haramta haram

عن جابر رضي الله عنه: أَنَّ رَجُلًا سَأَلَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: أَرَأَيْتَ إِذَا صَلَّيْتُ الصَّلَوَاتِ الْمَكْتُوبَاتِ، وَصُمْتُ رَمَضَانَ، وَأَحْلَلْتُ الْحَلَالَ، وَحَرَّمْتُ الْحَرَامَ، وَلَمْ أَزِدْ عَلَى ذَلِكَ شَيْئًا، أَأَدْخُلُ الْجَنَّةَ؟ قَالَ: «نَعَمْ»، قَالَ: وَاللهِ لَا أَزِيدُ عَلَى ذَلِكَ شَيْئًا.
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi -: Lallai wani mutum ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Kana ganin idan na sallaci salloli wadanda aka wajabta, na azimci watan Ramdan, na halatta halal, na haramta haram, ban kara komai akan hakan ba, zan shiga Aljanna? Ya ce : "Eh", ya ce: Na rantse da Allah ba zan kara komai ba akan hakan ba.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya sallaci salloli biyar, wadanda suka wajabta bai kara komai akan su ba na nafilifili, kuma ya azimci watan Ramadan bai yi tadawwa’i ba, ya kudirce halatta halal ya kuma aikata shi, ya kudirce haramta haram ya kuma nisanci ta, to shi zai shiga Aljanna.

Fa’idoji
  1. Kwadayin musulmi akan aikata farillai da barin abubuwan da aka haramta, da kuma manufarsa ta zama shiga Aljanna.
  2. Muhimmancin aikata halal da kudirce halaccinsa, da kuma haramta haram da kudirce haramcin shi.
  3. Aikata wajibai da barin abubuwan da aka haramta, sababi ne na shiga Aljanna.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 44) (15). جامع العلوم والحكم (1/513). شرح الأربعين النووية للعثيمين (ص: 215). فتح القوي المتين في شرح الأربعين للعباد (ص 77).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com