عن أبي موسى الأشعري رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ حَمَلَ عَلَيْنَا السِّلَاحَ فَلَيْسَ مِنَّا».
Daga Abu Musa Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya ɗaga makami a kammu, to, ba ya tare da mu"
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana gargaɗarwa daga ɗaukar makami a kan musulmai, don tsorata su ko yi musu ƙwace, wanda ya aikata hakan ba tare da wani haƙƙi ba, to, haƙiƙa ya aikata babban laifi daga manyan laifuka, kuma ya cancanci wannan narkon mai tsanani.
Fa’idoji
Gargaɗi mai tsanani game da yaƙar musulmi ga 'yan uwansa musulmai.
Daga mafi girman laifuka da ɓarna mai girma a ban ƙasa ɗaga makami a kan musulmai, da kuma ɓarna ta hanyar kisa.
Narkon da aka ambata ba ya shafar yaƙin (da aka yi) da haƙƙi, kamar yaƙar 'yan tawaye da maɓarnata da wasunsu.
Haramcin tsoratar da musulmai da makami ko waninsa - ko da ta fuskar wasa ne ne -.
Madogara
صحيح البخاري (9/ 49) (7071).
صحيح مسلم (1/ 98) (100).
خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص406).
الإفهام في شرح عمدة الأحكام، لابن باز (ص815).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (2/ 195).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص752).
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Wani mutum ba zai jefi wani mutum da fasiƙanci ba, kuma ba zai jefe shi da kafirci ba, sai ta dawo kansa idan m'abocinta bai zama kamar hakan ba".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi cewa wanda ya cewa wani: Kai fasiƙine, ko: Kai kafiri ne, idan ya kasance bai zama kamar yadda ya faɗa ba, ya kasance shi ne wanda ya cancanci siffar da aka anbata kuma maganarsa ta dawo masa, amma idan ya kasance kamar yadda ya faɗa wani abu ba zai dawo masa ba; saboda kasancewarsa ya yi gaskiya a abinda ya faɗa.
Fa’idoji
Haramcin jifan mutane da kafirci ko fasiƙanci, ba tare da wani abin halattawa na shari'a ba.
Wajabcin neman tabbaci a fitar da hukunce-hukunce akan mutane.
Ibnu Daƙiƙul Id ya ce: Wannan narko ne mai girma ga wanda ya kafirta wani daga musulmai alhali bai zama kamar hakan ba, kuma ita matsala ce mai girma.
Ibnu Hajar al-Asƙalani ya ce: Sai dai ba ya lazimtar kasancewarsa bai zamo fasiƙi ko kafiri ba da hakan, a ce kuma ba zai zama mai saɓo a surar faɗinsa gare shi ba: Kai fasiƙi ne, kai a wannan surar (akwai) rarrabewa: Idan ya yi nufin yi masa nasiha ko nasihar waninsa da bayanin halinsa to ya halatta, idan ya yi nufin aibanta shi da yayata shi da hakan da tsantsar cutarsa to bai halatta ba; domin cewa shi abin umarta ne da rufa masa asiri da sanar da shi da yi masa wa'azi da kyakkyawa, a duk lokacin da hakan ya yi wu gare shi da sauƙi to ba ya halatta gare shi ya aikata shi da tsanani; domin cewa shi zai iya kasancewa sababi na ruɗar da shi da kuma zarcewarsa akan wannan aikin, kamar yadda yake a dabi'ar da yawa daga mutane ita ce tsanani, musamman ma idan mai umarnin ya kasance bai kai wanda ake umartar a daraja ba.
Madogara
صحيح البخاري (8/ 15) (6045).
صحيح مسلم (1/ 79) (61).
نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1073).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (18/ 446).
بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (3/ 82).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 220).
التنوير شرح الجامع الصغير، للصنعاني (9/ 275).
عن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: «من خَبَّبَ زوجة امْرِئٍ أو مَمْلُوكَهُ فليس مِنَّا».
Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Manzon Allah "Duk wanda ya lalata Matar Wani ko baiwarsa to baya tare da mu"
Abu Daud Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Duk wanda ya yi qoqarin vata Matar wani Mutum, kuma duk xaya ne mai vatawar Namiji ne ko mace, kamar ya riqa faxar laifukan Mijinta ko Munanan halayansa har taji ta tsani Mijinta, tayi masa tawaye, kuma ta nemi ta rabu da shi da saki ko Khul'u, ko ya lalata Bawan Mutum ya sanya shi yayi wani aiki da zai tawaye ga mai gidansa, ko yayi masa Mummunar Mu'amala, to wanda yayi haka baya tare da shiriyarmu, ko kan turbarmu, aa wannan ma yana cikin aikin Shaixan
Madogara
نزهة المتقين، تأليف: جمعٌ من المشايخ، الناشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة الأولى: 1397 هـ الطبعة الرابعة عشر 1407 هـ.
كنوز رياض الصالحين، تأليف: حمد بن ناصر بن العمار ، الناشر: دار كنوز أشبيليا، الطبعة الأولى: 1430 هـ.
شرح سنن أبي داود، تأليف: عبد المحسن بن حمد بن عبد المحسن العباد، نسخة الإلكترونية.
صحيح الجامع الصغير وزيادته، تأليف: محمد ناصر الدين الألباني، الناشر: المكتب الإسلامي.
رياض الصالحين، تأليف : محيي الدين يحيى بن شرف النووي ، تحقيق: د. ماهر بن ياسين الفحل ، الطبعة: الأولى، 1428 هـ.
سنن أبي داود، تأليف: سليمان بن الأشعث السَِّجِسْتاني، تحقيق: محمد محيي الدين عبد الحميد، الناشر: المكتبة العصرية، صيدا.
دليل الفالحين، تأليف: محمد بن علان، الناشر: دار الكتاب.
شرح رياض الصالحين، تأليف: محمد بن صالح العثيمين، الناشر: دار الوطن للنشر، الطبعة: 1426 هـ.
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com