Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wani mutum ba zai jefi wani mutum da fasiƙanci ba, kuma ba zai jefe shi da kafirci ba, sai ta dawo kansa idan m'abocinta bai zama kamar hakan ba

عَنْ أَبِي ذَرٍّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّهُ سَمِعَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «لاَ يَرْمِي رَجُلٌ رَجُلًا بِالفُسُوقِ، وَلاَ يَرْمِيهِ بِالكُفْرِ، إِلَّا ارْتَدَّتْ عَلَيْهِ، إِنْ لَمْ يَكُنْ صَاحِبُهُ كَذَلِكَ».
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Wani mutum ba zai jefi wani mutum da fasiƙanci ba, kuma ba zai jefe shi da kafirci ba, sai ta dawo kansa idan m'abocinta bai zama kamar hakan ba".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi cewa wanda ya cewa wani: Kai fasiƙine, ko: Kai kafiri ne, idan ya kasance bai zama kamar yadda ya faɗa ba, ya kasance shi ne wanda ya cancanci siffar da aka anbata kuma maganarsa ta dawo masa, amma idan ya kasance kamar yadda ya faɗa wani abu ba zai dawo masa ba; saboda kasancewarsa ya yi gaskiya a abinda ya faɗa.

Fa’idoji
  1. Haramcin jifan mutane da kafirci ko fasiƙanci, ba tare da wani abin halattawa na shari'a ba.
  2. Wajabcin neman tabbaci a fitar da hukunce-hukunce akan mutane.
  3. Ibnu Daƙiƙul Id ya ce: Wannan narko ne mai girma ga wanda ya kafirta wani daga musulmai alhali bai zama kamar hakan ba, kuma ita matsala ce mai girma.
  4. Ibnu Hajar al-Asƙalani ya ce: Sai dai ba ya lazimtar kasancewarsa bai zamo fasiƙi ko kafiri ba da hakan, a ce kuma ba zai zama mai saɓo a surar faɗinsa gare shi ba: Kai fasiƙi ne, kai a wannan surar (akwai) rarrabewa: Idan ya yi nufin yi masa nasiha ko nasihar waninsa da bayanin halinsa to ya halatta, idan ya yi nufin aibanta shi da yayata shi da hakan da tsantsar cutarsa to bai halatta ba; domin cewa shi abin umarta ne da rufa masa asiri da sanar da shi da yi masa wa'azi da kyakkyawa, a duk lokacin da hakan ya yi wu gare shi da sauƙi to ba ya halatta gare shi ya aikata shi da tsanani; domin cewa shi zai iya kasancewa sababi na ruɗar da shi da kuma zarcewarsa akan wannan aikin, kamar yadda yake a dabi'ar da yawa daga mutane ita ce tsanani, musamman ma idan mai umarnin ya kasance bai kai wanda ake umartar a daraja ba.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 15) (6045). صحيح مسلم (1/ 79) (61). نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1073). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (18/ 446). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (3/ 82). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 220). التنوير شرح الجامع الصغير، للصنعاني (9/ 275).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
KAFURCI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com