Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Abu biyu a cikin mutane su kafirci ne a cikinsu: Sukar nasaba, da kukan kera ga mamaci

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «اثْنَتَانِ فِي النَّاسِ هُمَا بِهِمْ كُفْرٌ: الطَّعْنُ فِي النَّسَبِ، وَالنِّيَاحَةُ عَلَى الْمَيِّتِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Abu biyu a cikin mutane su kafirci ne a cikinsu: Sukar nasaba, da kukan kera ga mamaci".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da ɗabi'u biyu a cikin mutane suna daga ayyukan kafirai, da kuma ɗabi'un Jahiliyya, su ne: Na farko: Sukar nasabobin mutane da tauyesu da yi musu girman kai. Na biyu: Ɗaga murya a lokacin masifa dan yin fushi akan ƙaddara, ko yaga tufafi saboda tsananin baƙin ciki.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa akan ƙanƙar da kai da rashin yi wa mutane girman kai.
  2. Wajabcin haƙuri akan masifa da rashin fushi.
  3. Waɗannan ayyukan suna daga kafirci ƙarami, wanda wani yanki na kafirci yake tare da shi, ba zai zama kafiri kafircin da yake fitarwa daga Musulunci ba har sai kafirci babba ya tabbata gare shi.
  4. Hanawar Musulunci game da dukkan abinda yake kaiwa zuwa rabuwa tsakanin musulmai na sukar dangantaka da waninsa.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 82) (67). كتاب التوحيد، للإمام محمد بن عبد الوهاب (ص96). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص279). الجديد في شرح كتاب التوحيد، للقرعاوي (ص315).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
KAFURCI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com