عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «اثْنَتَانِ فِي النَّاسِ هُمَا بِهِمْ كُفْرٌ: الطَّعْنُ فِي النَّسَبِ، وَالنِّيَاحَةُ عَلَى الْمَيِّتِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Abu biyu a cikin mutane su kafirci ne a cikinsu: Sukar nasaba, da kukan kera ga mamaci".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da ɗabi'u biyu a cikin mutane suna daga ayyukan kafirai, da kuma ɗabi'un Jahiliyya, su ne:
Na farko: Sukar nasabobin mutane da tauyesu da yi musu girman kai.
Na biyu: Ɗaga murya a lokacin masifa dan yin fushi akan ƙaddara, ko yaga tufafi saboda tsananin baƙin ciki.
Fa’idoji
- Kwaɗaitarwa akan ƙanƙar da kai da rashin yi wa mutane girman kai.
- Wajabcin haƙuri akan masifa da rashin fushi.
- Waɗannan ayyukan suna daga kafirci ƙarami, wanda wani yanki na kafirci yake tare da shi, ba zai zama kafiri kafircin da yake fitarwa daga Musulunci ba har sai kafirci babba ya tabbata gare shi.
- Hanawar Musulunci game da dukkan abinda yake kaiwa zuwa rabuwa tsakanin musulmai na sukar dangantaka da waninsa.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 82) (67).
كتاب التوحيد، للإمام محمد بن عبد الوهاب (ص96).
الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص279).
الجديد في شرح كتاب التوحيد، للقرعاوي (ص315).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي ذَرٍّ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ أَنَّهُ سَمِعَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «لاَ يَرْمِي رَجُلٌ رَجُلًا بِالفُسُوقِ، وَلاَ يَرْمِيهِ بِالكُفْرِ، إِلَّا ارْتَدَّتْ عَلَيْهِ، إِنْ لَمْ يَكُنْ صَاحِبُهُ كَذَلِكَ».
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Wani mutum ba zai jefi wani mutum da fasiƙanci ba, kuma ba zai jefe shi da kafirci ba, sai ta dawo kansa idan m'abocinta bai zama kamar hakan ba".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi cewa wanda ya cewa wani: Kai fasiƙine, ko: Kai kafiri ne, idan ya kasance bai zama kamar yadda ya faɗa ba, ya kasance shi ne wanda ya cancanci siffar da aka anbata kuma maganarsa ta dawo masa, amma idan ya kasance kamar yadda ya faɗa wani abu ba zai dawo masa ba; saboda kasancewarsa ya yi gaskiya a abinda ya faɗa.
Fa’idoji
- Haramcin jifan mutane da kafirci ko fasiƙanci, ba tare da wani abin halattawa na shari'a ba.
- Wajabcin neman tabbaci a fitar da hukunce-hukunce akan mutane.
- Ibnu Daƙiƙul Id ya ce: Wannan narko ne mai girma ga wanda ya kafirta wani daga musulmai alhali bai zama kamar hakan ba, kuma ita matsala ce mai girma.
- Ibnu Hajar al-Asƙalani ya ce: Sai dai ba ya lazimtar kasancewarsa bai zamo fasiƙi ko kafiri ba da hakan, a ce kuma ba zai zama mai saɓo a surar faɗinsa gare shi ba: Kai fasiƙi ne, kai a wannan surar (akwai) rarrabewa: Idan ya yi nufin yi masa nasiha ko nasihar waninsa da bayanin halinsa to ya halatta, idan ya yi nufin aibanta shi da yayata shi da hakan da tsantsar cutarsa to bai halatta ba; domin cewa shi abin umarta ne da rufa masa asiri da sanar da shi da yi masa wa'azi da kyakkyawa, a duk lokacin da hakan ya yi wu gare shi da sauƙi to ba ya halatta gare shi ya aikata shi da tsanani; domin cewa shi zai iya kasancewa sababi na ruɗar da shi da kuma zarcewarsa akan wannan aikin, kamar yadda yake a dabi'ar da yawa daga mutane ita ce tsanani, musamman ma idan mai umarnin ya kasance bai kai wanda ake umartar a daraja ba.
Madogara
صحيح البخاري (8/ 15) (6045).
صحيح مسلم (1/ 79) (61).
نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1073).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (18/ 446).
بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (3/ 82).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 220).
التنوير شرح الجامع الصغير، للصنعاني (9/ 275).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها قَالَتْ: قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ، ابْنُ جُدْعَانَ كَانَ فِي الْجَاهِلِيَّةِ يَصِلُ الرَّحِمَ، وَيُطْعِمُ الْمِسْكِينَ، فَهَلْ ذَاكَ نَافِعُهُ؟ قَالَ: «لَا يَنْفَعُهُ، إِنَّهُ لَمْ يَقُلْ يَوْمًا: رَبِّ اغْفِرْ لِي خَطِيئَتِي يَوْمَ الدِّينِ».
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ce: Ya Manzon Allah, Ibn Jud'an ya kasance a lokacin jahiliyya yana sada zumunci, yana ciyar da miskinai, shin hakan zai anfanar da shi? Sai Ya ce: "Ba zai anfanar dashi ba, Lallai shi bai taba fada ba koda yini daya: Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena ranar sakamako".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da Abdullahi Ibnu Jud'an, ya kasance yana daga shugabannin Kuraishawa kafin Musulunci, Yana daga kyawawan ayyukansa cewa shi: Yana sada zumuncin 'yan uawansa, yana ciyar da miskinai, da wasunsu daga cikin mafifitan ayyukan da Musulunci ya kwadaitar akan aikatasu, da cewa wadannan ayyukan ba za su anfanar da shi a lahirarsa ba; saboda kafircewarsa ga Allah, kuma shi bai taba fada ba ko sau daya: Ya Ubangiji ka gafarta mini kuskurena ranar sakamako.
Fa’idoji
- Bayanin falalar imani, kuma shi (imani) sharadine na karbar ayyuka.
- Bayanin shu'umancin kafirci, kuma shi (kafirci) yana daga masu bata ayyuka na gari.
- Kafirai ayyukansu ba za su anfanar da su a lahira ba, saboda rashin imaninsu da Allah da kuma ranar lahira.
- Ayyukan mutum acikin halin kafircinsa za'a rubuta masa su idan ya musulunta, kuma za’a yi masa sakayya akansu.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 196) (214)، شرح النووي على مسلم (3/87)، المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (1/ 459)، إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (4/ 170)، التنوير شرح الجامع الصغير (2/364)، فتح المنعم (2/54)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (3/ 455).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ زَيْدِ بْنِ خَالِدٍ الجُهَنِيِّ رضي الله عنه أَنَّهُ قَالَ: صَلَّى لَنَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ صَلَاةَ الصُّبْحِ بِالْحُدَيْبِيَةِ عَلَى إِثْرِ سَمَاءٍ كَانَتْ مِنَ اللَّيْلَةِ، فَلَمَّا انْصَرَفَ أَقْبَلَ عَلَى النَّاسِ، فَقَالَ: «هَلْ تَدْرُونَ مَاذَا قَالَ رَبُّكُمْ؟» قَالُوا: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: «أَصْبَحَ مِنْ عِبَادِي مُؤْمِنٌ بِي وَكَافِرٌ، فَأَمَّا مَنْ قَالَ: مُطِرْنَا بِفَضْلِ اللهِ وَرَحْمَتِهِ، فَذَلِكَ مُؤْمِنٌ بِي وَكَافِرٌ بِالْكَوْكَبِ، وَأَمَّا مَنْ قَالَ: بِنَوْءِ كَذَا وَكَذَا، فَذَلِكَ كَافِرٌ بِي وَمُؤْمِنٌ بِالْكَوْكَبِ».
Daga Zaidu Dan Khalid AlJuhani - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallar Asuba a Hudaibiyya a bayan (ruwan daya sauka) a wannan daren da ya wuce, lokacin da ya sallame sai ya juya ya fuskanto mutane, ya ce: "Shin kun san mai Ubangijinku Ya ce?" Suka ce: Allah da Manzonsane mafi sani, ya ce: "Mumini da kafiri sun wayi gari daga bayina"
Amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da falalar Ubangiji da rahamarSa, to wannan ya yi imani da Ni, kuma ya kafircewa taurari. Amma wanda ya ce: Da tauraro kaza da kaza, to wannan ya kafirce mi Ni kuma ya yi imani da taurari".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi sallar Asuba a Hudaibiyya - ita wata alkaryace kusa da Makka bayan wani ruwa da ya sauka a wannan daren, Lokacin da ya yi sallama ya idar da sallarasa sai ya fuskanto mutane da fuskarsa, sai ya tambayesu: Shin kun san me Ubangijinku - Mai girma da daukaka - Ya ce ? Sai suka amsa masa: Allah da ManzonSane mafi sani. Sai ya ce: Lallai Allah - Madaukakin sarki - Ya bayyana cewa mutane a lokacin saukar ruwa sun kasu gida biyu: Bangare daya sun yi imani da Allah - Madaukakin sarki -, daya bangaren kuma suka kafircewa Allah - Madaukakin sarki -; Amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da falalar Allah da rahamarSa, ya danganta saukar ruwa ga Allah - Madaukakin sarki -; to wannan ya yi imani da Allah Mahalicci Mai jujjuya al'amura a cikin halittarsa , kuma ya kafircewa taurari. To amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da tauraro iri kaza da kaza; to wannan ya kafircewa Allah kuma ya yi imani da taurari, shi karamin kafarcine ta inda ya danganta saukar ruwa ga taurari; kuma Allah bai sanya shi wani sababi na shari'a ba ko na kaddara, Amma wanda ya danganta saukar ruwa da waninsa daga fararrun abubuwa na kasa ga motsin taurari a bullowarsu da faduwarsu yana mai kudire cewa su ne masu aikin na hakika to shi kafirine kafirci babba.
Fa’idoji
- Anso fadin: An yi mana ruwa da falalar Allah da rahamarSa bayan saukar ruwa.
- Wanda ya danganta ni'imar saukar ruwa da wasunsu ga taurari a halitta da samarwa to shi kafirine kafirci babba, idan ya danganta shi akan cewa shi wani sababi ne to shi kafirine kafirci karami domin cewa shi ba sababi ne na shari'a ko na gani ba.
- Lallai ni'ima tana kasancewa sababi na kafirci idan an butulce, kuma tana zama sababi na imani idan an gode.
- Hani akan fadin: "An yi mana ruwa da tauraro kaza da kaza", koda an nufi lokaci; dan toshe kafar shirka.
- Wajabcin damfarar zuciya ga Allah - Madaukakin sarki - a jawo ni'imomi da tunkude bala’o’i.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 169) (846)، صحيح مسلم (1/ 83) (71)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (2/ 484)، المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (1/ 260).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن جابرٍ رضي الله عنه قال: سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول: «إِنَّ بَيْنَ الرَّجُلِ وَبَيْنَ الشِّرْكِ وَالْكُفْرِ تَرْكَ الصَّلَاةِ».
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci (shi ne) barin sallah".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi gargaɗi game da barin sallar farilla, ya ba da labarin cewa tsakanin mutum da afkawa a shirka da kafirci (shi ne) barin sallah, sallah ita ce rukuni na biyu daga rukunan musulunci, al'amarinta mai girma ne a musulunci, wanda ya barta yana mai musun wajabcinta, to, ya kafirta da ijima'in musulmai, idan ya barta gabaɗaya don wulaƙantarwa da kasala, to, shi kafiri ne, an cirato ijma'in sahabbai a kan hakan, idan ya kasance yana bari wani lokaci wani lokaci kuma yana yin sallah, to, ya kai kansa ga wannan narkon mai tsanani.
Fa’idoji
- Muhimmancin sallah da kiyayewa a kanta, ita ce mai banbanta wa tsakanin kafirci da imani.
- Gargaɗi mai tsanani a kan barin sallah da tozartata.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 88) (82)، المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (1/ 271)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (2/ 622).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن بريدة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «إِنَّ الْعَهْدَ الَّذِي بَيْنَنَا وَبَيْنَهُمُ الصَّلَاةُ، فَمَنْ تَرَكَهَا فَقَدْ كَفَرَ».
Daga Buraidah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: "Lallai alƙawarin da ke tsakanin mu da su (shi ne) sallah, wanda ya barta, to, haƙiƙa ya kafirta".
Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa alƙawari tsakanin musulmai da wasunsu daga kafirai da munafikai (shi ne) sallah, wanda ya barta to haƙiƙa ya kafirta.
Fa’idoji
- Girman al'amarin sallah, kuma cewa ita ce mai banbantawa tsakanin mumini da kafiri.
- Tabbatar da hukunce-hukuncen musulunci da zahiri daga halin mutum ba baɗininsa ba.
Madogara
سنن النسائي (1/ 231) (463)، سنن الترمذي (4/ 365) (2621)، سنن ابن ماجه (2/ 181) (1079)، مسند أحمد (38/ 20) (22937)، فيض القدير (4/ 395)، ذخيرة العقبى في شرح المجتبى (6/ 192) (6/ 193).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com