Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci (shi ne) barin sallah

عن جابرٍ رضي الله عنه قال: سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول: «إِنَّ بَيْنَ الرَّجُلِ وَبَيْنَ الشِّرْكِ وَالْكُفْرِ تَرْكَ الصَّلَاةِ».
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci (shi ne) barin sallah".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi gargaɗi game da barin sallar farilla, ya ba da labarin cewa tsakanin mutum da afkawa a shirka da kafirci (shi ne) barin sallah, sallah ita ce rukuni na biyu daga rukunan musulunci, al'amarinta mai girma ne a musulunci, wanda ya barta yana mai musun wajabcinta, to, ya kafirta da ijima'in musulmai, idan ya barta gabaɗaya don wulaƙantarwa da kasala, to, shi kafiri ne, an cirato ijma'in sahabbai a kan hakan, idan ya kasance yana bari wani lokaci wani lokaci kuma yana yin sallah, to, ya kai kansa ga wannan narkon mai tsanani.

Fa’idoji
  1. Muhimmancin sallah da kiyayewa a kanta, ita ce mai banbanta wa tsakanin kafirci da imani.
  2. Gargaɗi mai tsanani a kan barin sallah da tozartata.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 88) (82)، المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (1/ 271)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (2/ 622).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ABUBUWAN DA SUKE WARWARE MUSULUNCI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com