Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

ABUBUWAN DA SUKE WARWARE MUSULUNCI

Hadisai 6

Babu sihiri da yake halatta sai mai sihiri

ورُوي عن الحسن أنه قال: "لا يحل السحر إلا ساحر".
An karbo daga Al-Hassan cewa ya ce: "Babu sihiri da yake halatta sai mai sihiri."
Ibnu Abi Hatim ya rawaito shi - Al-Khattabi Ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Sanarwa ita ce maganin sihiri, kuma bayyananniyar ma'anar kalaman Hassan haramun ne kwata-kwata Saboda wanda yake da ilimin sihiri ne kawai yake iya warware sihiri, kuma wannan ya halatta ya narkar da sihiri da sihiri irinsa, kuma aikin Shaidan ne, kuma Ibnul-Qayyim ya yi bayani dalla-dalla kan abin da ya samu: cewa yi wa masu sihir da magunguna halatta da karatun Alkur'ani ya halatta - kuma bi da shi da sihiri kamar shi haramun ne.

Madogara

1-فتح المجيد شرح كتاب التوحيد، مطبعة السنة المحمدية، القاهرة، مصر، الطبعة: السابعة، 1377هـ - 1957م. 2-القول المفيد على كتاب التوحيد، دار ابن الجوزي، المملكة العربية السعودية، الطبعة: الثانية, محرم، 1424هـ. 3-الملخص في شرح كتاب التوحيد، دار العاصمة الرياض، الطبعة: الأولى 1422هـ - 2001م. 4-الجديد في شرح كتاب التوحيد، مكتبة السوادي، جدة، المملكة العربية السعودية، الطبعة: الخامسة، 1424هـ - 2003م. 5-التمهيد لشرح كتاب التوحيد، دار التوحيد، تاريخ النشر: 1424هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ba ya cikimmu wanda ya yi camfi, ko aka yi masa camfi, ko ya yi bokanci ko aka yi masa bokanci, ko ya yi tsafi ko aka yi masa tsafi

عن عمران بن حصين رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «‌لَيْسَ ‌مِنَّا ‌مَنْ ‌تَطَيَّرَ أَوْ تُطُيِّرَ لَهُ، أَوْ تَكَهَّنَ أَوْ تُكُهِّنَ لَهُ، أَوْ سَحَرَ أَوْ سُحِرَ لَهُ، وَمَنْ عَقَدَ عُقْدَةً، وَمَنْ أَتَى كَاهِنًا فَصَدَّقَهُ بِمَا يَقُولُ فَقَدْ كَفَرَ بِمَا أُنْزِلَ عَلَى مُحَمَّدٍ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ».
Daga Imaran Ɗan Husain - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Ba ya cikimmu wanda ya yi camfi, ko aka yi masa camfi, ko ya yi bokanci ko aka yi masa bokanci, ko ya yi tsafi ko aka yi masa tsafi. Duk wanda ya ƙulla wani ƙulli, duk wanda ya je wurin boka ya gasgata shi a kan abin da ya faɗa, to, ya kafircewa abin da aka saukar ga (Annabi) Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Bazzar ne Ya Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi alƙawarin narkon azaba ga wanda ya aikata wasu ayyuka cikin al’ummarsa, da ya ce: Ba ya daga cikimmu. Na farko: Wanda ya yi camfi ko aka yi masa camfi, asalinsa: suna sakin tsuntsu ne lokacin fara wani abu, kamar tafiya ko fatauci ko wanin haka, idan ya yi dama sai ya ce akwai sa’a, sai ya yi abin da ya sa a gaba, idan kuma ya yi hagu sai ya ce babu sa’a sai ya ƙi yi, bai halatta ya yi haka da kansa ba, ko ya sa a yi masa, camfi da kowanne abu na ji ne ko na gani ya shiga ƙarƙashin haka, da tsuntsaye ko dabbobi aka yi, ko masu fama da nakasa, ko wasu lambobi ko ranaku, da sauransu. Na biyu: Wanda ya yi bokanci ko aka yi masa bokanci’. Duk wanda ya ce ya san gaibu ta hanyar taurari, ko wanin haka, ko ya je wurin wanda ya ce ya san gaibu kamar boka da makamantansu, ya kuma gasgata shi a abin da ya faɗa na cewar ya san gaibu, to, haƙiƙa ya kafirta da abin da aka saukarwa Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Na uku: Wanda ya yi asiri ko aka yi masa asiri’. Shi ne wanda yake yin a siri da kansa, ko ya sa a yi masa asiri, domin ya amfanar da wani da shi, ko don ya cutar da wani, ko ya ƙulla ƙulli da zare da asiri da surkulle da aka haramta da tofi a kai.

Fa’idoji
  1. Wajibcin dogaro ga Allah, da imani da abin da Allah Ya hukunta Ya kuma ƙaddara. Da kuma haramcin camfi da asiri da bokanci, ko tambayar masu yin haka.
  2. Iƙirarin sanin gaibu ɓangare ne na shirka, wanda yake kore Tauhidi.
  3. Haramcin gasgata bokaye da zuwa wurinsu, kuma yana shiga nan duba a tafin hannu, da kwarya da buruji da nazari a kansu, ko da kuwa don leƙawa ne.
Madogara

مسند البزار = البحر الزخار (9/ 52) (3578). شرح السنة للبغوي (12/ 182). مجموع الفتاوى (35/ 173). القول المفيد على كتاب التوحيد، لابن عثيمين (1/ 543). التمهيد لشرح كتاب التوحيد، لصالح آل الشيخ (ص315). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص242). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص217).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Dukkan wanda ya ɗosani wani yanki na ilimin taurari, to, haƙiƙa ya ɗosani wani yanki na tsafi, ya ƙara abin da ya ƙara

عن ابن عباس رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «من اقتبَسَ علْمًا مِنَ النُّجُومِ اقْتبَسَ شُعبَة مِن السِّحرِ، زادَ ما زادَ».
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkan wanda ya ɗosani wani yanki na ilimin taurari, to, haƙiƙa ya ɗosani wani yanki na tsafi, ya ƙara abin da ya ƙara".
Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da AhmadDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana duk wanda ya koyi, ya samu wani tsagi na ilimin taurari da buruji da kuma kafa dalili da motsinsu da shigarsu da fitarsu a kan abin da zai faru a bayan ƙasa na mutuwar wane, ko rayuwarsa, ko rashin lafiyarsa, da makamancin haka cikin abinda zai faru nan gaba, to, haƙiƙa ya koyi wani tsagi na sihiri, kuma duk lokacin da mutum ya ƙara wannan ilimin, to, ya ƙara asiri [tsafi] ne.

Fa’idoji
  1. Haramcin ilimin taurari wanda yake na ba da labarin abin da zai faru nan gaba, dogaro da yanayin taurari, domin yana cikin iƙirarin sanin gaibu.
  2. Ilimin taurari haramun ne, yana cikin nau’ukan asiri [tsafi] wanda yake kore Tauhidi, saɓanin nazarin taurari domin sanin inda mutum ya nufa, ko sanin alƙibla, ko sanin shigar lokacin wasu bukukuwa, ko watanni, to, wannan ya halatta.
  3. Duk lokacin da ya ƙara a koyar ilimin taurari, to, yana ƙara koyar wani kaso ne na asiri [tsafi].
  4. Taurari suna da fa'idoji uku, Allah ya ambace su a LittafinSa: Ƙawa ga sama, alamomi da za’a dinga ganewa da su, jifa ga shaiɗanu.
Madogara

سنن أبي داود (6/ 50) (3905). سنن ابن ماجه (4/ 670) (3726). مسند أحمد (3/ 454) (2000). الجديد في شرح كتاب التوحيد، للقرعاوي (ص230). الملخص في شرح كتاب التوحيد، للفوزان (ص206).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Shin kun san mai Ubangijinku Ya ce?" Suka ce: Allah da Manzonsane mafi sani, ya ce: "Mumini da kafiri sun wayi gari daga bayina

عَنْ زَيْدِ بْنِ خَالِدٍ الجُهَنِيِّ رضي الله عنه أَنَّهُ قَالَ: صَلَّى لَنَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ صَلَاةَ الصُّبْحِ بِالْحُدَيْبِيَةِ عَلَى إِثْرِ سَمَاءٍ كَانَتْ مِنَ اللَّيْلَةِ، فَلَمَّا انْصَرَفَ أَقْبَلَ عَلَى النَّاسِ، فَقَالَ: «هَلْ تَدْرُونَ مَاذَا قَالَ رَبُّكُمْ؟» قَالُوا: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: «أَصْبَحَ مِنْ عِبَادِي مُؤْمِنٌ بِي وَكَافِرٌ، فَأَمَّا مَنْ قَالَ: مُطِرْنَا بِفَضْلِ اللهِ وَرَحْمَتِهِ، فَذَلِكَ مُؤْمِنٌ بِي وَكَافِرٌ بِالْكَوْكَبِ، وَأَمَّا مَنْ قَالَ: بِنَوْءِ كَذَا وَكَذَا، فَذَلِكَ كَافِرٌ بِي وَمُؤْمِنٌ بِالْكَوْكَبِ».
Daga Zaidu Dan Khalid AlJuhani - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallar Asuba a Hudaibiyya a bayan (ruwan daya sauka) a wannan daren da ya wuce, lokacin da ya sallame sai ya juya ya fuskanto mutane, ya ce: "Shin kun san mai Ubangijinku Ya ce?" Suka ce: Allah da Manzonsane mafi sani, ya ce: "Mumini da kafiri sun wayi gari daga bayina" Amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da falalar Ubangiji da rahamarSa, to wannan ya yi imani da Ni, kuma ya kafircewa taurari. Amma wanda ya ce: Da tauraro kaza da kaza, to wannan ya kafirce mi Ni kuma ya yi imani da taurari".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi sallar Asuba a Hudaibiyya - ita wata alkaryace kusa da Makka bayan wani ruwa da ya sauka a wannan daren, Lokacin da ya yi sallama ya idar da sallarasa sai ya fuskanto mutane da fuskarsa, sai ya tambayesu: Shin kun san me Ubangijinku - Mai girma da daukaka - Ya ce ? Sai suka amsa masa: Allah da ManzonSane mafi sani. Sai ya ce: Lallai Allah - Madaukakin sarki - Ya bayyana cewa mutane a lokacin saukar ruwa sun kasu gida biyu: Bangare daya sun yi imani da Allah - Madaukakin sarki -, daya bangaren kuma suka kafircewa Allah - Madaukakin sarki -; Amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da falalar Allah da rahamarSa, ya danganta saukar ruwa ga Allah - Madaukakin sarki -; to wannan ya yi imani da Allah Mahalicci Mai jujjuya al'amura a cikin halittarsa , kuma ya kafircewa taurari. To amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da tauraro iri kaza da kaza; to wannan ya kafircewa Allah kuma ya yi imani da taurari, shi karamin kafarcine ta inda ya danganta saukar ruwa ga taurari; kuma Allah bai sanya shi wani sababi na shari'a ba ko na kaddara, Amma wanda ya danganta saukar ruwa da waninsa daga fararrun abubuwa na kasa ga motsin taurari a bullowarsu da faduwarsu yana mai kudire cewa su ne masu aikin na hakika to shi kafirine kafirci babba.

Fa’idoji
  1. Anso fadin: An yi mana ruwa da falalar Allah da rahamarSa bayan saukar ruwa.
  2. Wanda ya danganta ni'imar saukar ruwa da wasunsu ga taurari a halitta da samarwa to shi kafirine kafirci babba, idan ya danganta shi akan cewa shi wani sababi ne to shi kafirine kafirci karami domin cewa shi ba sababi ne na shari'a ko na gani ba.
  3. Lallai ni'ima tana kasancewa sababi na kafirci idan an butulce, kuma tana zama sababi na imani idan an gode.
  4. Hani akan fadin: "An yi mana ruwa da tauraro kaza da kaza", koda an nufi lokaci; dan toshe kafar shirka.
  5. Wajabcin damfarar zuciya ga Allah - Madaukakin sarki - a jawo ni'imomi da tunkude bala’o’i.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 169) (846)، صحيح مسلم (1/ 83) (71)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (2/ 484)، المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (1/ 260).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci (shi ne) barin sallah

عن جابرٍ رضي الله عنه قال: سمعت النبي صلى الله عليه وسلم يقول: «إِنَّ بَيْنَ الرَّجُلِ وَبَيْنَ الشِّرْكِ وَالْكُفْرِ تَرْكَ الصَّلَاةِ».
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci (shi ne) barin sallah".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi gargaɗi game da barin sallar farilla, ya ba da labarin cewa tsakanin mutum da afkawa a shirka da kafirci (shi ne) barin sallah, sallah ita ce rukuni na biyu daga rukunan musulunci, al'amarinta mai girma ne a musulunci, wanda ya barta yana mai musun wajabcinta, to, ya kafirta da ijima'in musulmai, idan ya barta gabaɗaya don wulaƙantarwa da kasala, to, shi kafiri ne, an cirato ijma'in sahabbai a kan hakan, idan ya kasance yana bari wani lokaci wani lokaci kuma yana yin sallah, to, ya kai kansa ga wannan narkon mai tsanani.

Fa’idoji
  1. Muhimmancin sallah da kiyayewa a kanta, ita ce mai banbanta wa tsakanin kafirci da imani.
  2. Gargaɗi mai tsanani a kan barin sallah da tozartata.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 88) (82)، المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (1/ 271)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (2/ 622).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai alƙawarin da ke tsakanin mu da su (shi ne) sallah, wanda ya barta, to, haƙiƙa ya kafirta

عن بريدة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «إِنَّ الْعَهْدَ الَّذِي بَيْنَنَا وَبَيْنَهُمُ الصَّلَاةُ، فَمَنْ تَرَكَهَا فَقَدْ كَفَرَ».
Daga Buraidah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: "Lallai alƙawarin da ke tsakanin mu da su (shi ne) sallah, wanda ya barta, to, haƙiƙa ya kafirta".
Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa alƙawari tsakanin musulmai da wasunsu daga kafirai da munafikai (shi ne) sallah, wanda ya barta to haƙiƙa ya kafirta.

Fa’idoji
  1. Girman al'amarin sallah, kuma cewa ita ce mai banbantawa tsakanin mumini da kafiri.
  2. Tabbatar da hukunce-hukuncen musulunci da zahiri daga halin mutum ba baɗininsa ba.
Madogara

سنن النسائي (1/ 231) (463)، سنن الترمذي (4/ 365) (2621)، سنن ابن ماجه (2/ 181) (1079)، مسند أحمد (38/ 20) (22937)، فيض القدير (4/ 395)، ذخيرة العقبى في شرح المجتبى (6/ 192) (6/ 193).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com