Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Dukkan wanda ya ɗosani wani yanki na ilimin taurari, to, haƙiƙa ya ɗosani wani yanki na tsafi, ya ƙara abin da ya ƙara

عن ابن عباس رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «من اقتبَسَ علْمًا مِنَ النُّجُومِ اقْتبَسَ شُعبَة مِن السِّحرِ، زادَ ما زادَ».
Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Dukkan wanda ya ɗosani wani yanki na ilimin taurari, to, haƙiƙa ya ɗosani wani yanki na tsafi, ya ƙara abin da ya ƙara".
Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da AhmadDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana duk wanda ya koyi, ya samu wani tsagi na ilimin taurari da buruji da kuma kafa dalili da motsinsu da shigarsu da fitarsu a kan abin da zai faru a bayan ƙasa na mutuwar wane, ko rayuwarsa, ko rashin lafiyarsa, da makamancin haka cikin abinda zai faru nan gaba, to, haƙiƙa ya koyi wani tsagi na sihiri, kuma duk lokacin da mutum ya ƙara wannan ilimin, to, ya ƙara asiri [tsafi] ne.

Fa’idoji
  1. Haramcin ilimin taurari wanda yake na ba da labarin abin da zai faru nan gaba, dogaro da yanayin taurari, domin yana cikin iƙirarin sanin gaibu.
  2. Ilimin taurari haramun ne, yana cikin nau’ukan asiri [tsafi] wanda yake kore Tauhidi, saɓanin nazarin taurari domin sanin inda mutum ya nufa, ko sanin alƙibla, ko sanin shigar lokacin wasu bukukuwa, ko watanni, to, wannan ya halatta.
  3. Duk lokacin da ya ƙara a koyar ilimin taurari, to, yana ƙara koyar wani kaso ne na asiri [tsafi].
  4. Taurari suna da fa'idoji uku, Allah ya ambace su a LittafinSa: Ƙawa ga sama, alamomi da za’a dinga ganewa da su, jifa ga shaiɗanu.
Madogara

سنن أبي داود (6/ 50) (3905). سنن ابن ماجه (4/ 670) (3726). مسند أحمد (3/ 454) (2000). الجديد في شرح كتاب التوحيد، للقرعاوي (ص230). الملخص في شرح كتاب التوحيد، للفوزان (ص206).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ABUBUWAN DA SUKE WARWARE MUSULUNCI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com