Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai shi bai taba fada ba koda yini daya: Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena ranar sakamako

عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها قَالَتْ: قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ، ابْنُ جُدْعَانَ كَانَ فِي الْجَاهِلِيَّةِ يَصِلُ الرَّحِمَ، وَيُطْعِمُ الْمِسْكِينَ، فَهَلْ ذَاكَ نَافِعُهُ؟ قَالَ: «لَا يَنْفَعُهُ، إِنَّهُ لَمْ يَقُلْ يَوْمًا: رَبِّ اغْفِرْ لِي خَطِيئَتِي يَوْمَ الدِّينِ».
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ce: Ya Manzon Allah, Ibn Jud'an ya kasance a lokacin jahiliyya yana sada zumunci, yana ciyar da miskinai, shin hakan zai anfanar da shi? Sai Ya ce: "Ba zai anfanar dashi ba, Lallai shi bai taba fada ba koda yini daya: Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena ranar sakamako".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da Abdullahi Ibnu Jud'an, ya kasance yana daga shugabannin Kuraishawa kafin Musulunci, Yana daga kyawawan ayyukansa cewa shi: Yana sada zumuncin 'yan uawansa, yana ciyar da miskinai, da wasunsu daga cikin mafifitan ayyukan da Musulunci ya kwadaitar akan aikatasu, da cewa wadannan ayyukan ba za su anfanar da shi a lahirarsa ba; saboda kafircewarsa ga Allah, kuma shi bai taba fada ba ko sau daya: Ya Ubangiji ka gafarta mini kuskurena ranar sakamako.

Fa’idoji
  1. Bayanin falalar imani, kuma shi (imani) sharadine na karbar ayyuka.
  2. Bayanin shu'umancin kafirci, kuma shi (kafirci) yana daga masu bata ayyuka na gari.
  3. Kafirai ayyukansu ba za su anfanar da su a lahira ba, saboda rashin imaninsu da Allah da kuma ranar lahira.
  4. Ayyukan mutum acikin halin kafircinsa za'a rubuta masa su idan ya musulunta, kuma za’a yi masa sakayya akansu.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 196) (214)، شرح النووي على مسلم (3/87)، المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (1/ 459)، إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (4/ 170)، التنوير شرح الجامع الصغير (2/364)، فتح المنعم (2/54)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (3/ 455).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
MUSULUNCI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com

Lallai shi bai taba fada ba koda yini daya: Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena ranar sakamako · Hadisai tare da sharhi · Sabīl