Wanda ya kyautata a Musulunci ba za'a kama shi da abinda ya aikata ba a lokacin Jahiliyya, wanda kuma ya munana a cikin Musulunci za'a kama shi da na farko da na karshe
Daga Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce: Wani mutum ya ce: ya Manzon Allah, shin za'a kamamu da abinda muka aikata a lokacin Jahiliyya? ya ce: "Wanda ya kyautata a Musulunci ba za'a kama shi da abinda ya aikata ba a lokacin Jahiliyya, wanda kuma ya munana a cikin Musulunci za'a kama shi da na farko da na karshe".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana falalar shiga Musulunci. Kuma cewa wanda ya musulunta kuma ya kyautata Musuluncinsa ya zama mai tsarkakewa mai gaskiya, to ba za’a yi masa hisabi da abinda ya aikata na sabo ba a lokacin Jahiliyya, Wanda ya munana a cikin Musulunci, da ya zama munafiki ko ya yi ridda ga Addininsa, za'a yi masa hisabi da abinda ya aikata a cikin kafirci, da kuma abinda ya aikata a cikin Musulunci.
Fa’idoji
Himmatuwar sahabbai - Allah Ya yarda da su - da kuma tsoronsu daga abinda ke tare da su na ayyukan Jahiliyya (da suka yi a baya).
Kwadaitarwa akan tabbata akan Musulunci.
Falalar shiga addinin Musulunci, kuma cewa shi yana kankare ayyukan da suka gabata.
Wanda ya yi ridda da munafiki za’a yi masa hisabi da dukkanin wani aikin da ya gabatar a lokacin Jahiliyya, haka ma kuma da dukkanin wani zinibin da ya aikata shi a cikin Musulunci.
Madogara
صحيح البخاري (9/ 14) (6921).
صحيح مسلم (1/ 111) (120).
مشارق الأنوار على صحاح الآثار (2/229).
الكواكب الدراري (24/43).
عمدة القاري شرح صحيح البخاري (24/ 76).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com