Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

MUSULUNCI

Hadisai 23

Lallai kai zaka je wa wasu mutane mazowa littafi, idan ka je musu to ka kirayesu zuwa su shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa Annabi Muhammad Manzon Allah ne

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِمُعَاذِ بْنِ جَبَلٍ، حِينَ بَعَثَهُ إِلَى الْيَمَنِ: «إِنَّكَ سَتَأْتِي قَوْمًا أَهْلَ كِتَابٍ، فَإِذَا جِئْتَهُمْ فَادْعُهُمْ إِلَى أَنْ يَشْهَدُوا أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ، فَإِنْ هُمْ أَطَاعُوا لَكَ بِذَلِكَ، فَأَخْبِرْهُمْ أَنَّ اللهَ قَدْ فَرَضَ عَلَيْهِمْ خَمْسَ صَلَوَاتٍ فِي كُلِّ يَوْمٍ وَلَيْلَةٍ، فَإِنْ هُمْ أَطَاعُوا لَكَ بِذَلِكَ، فَأَخْبِرْهُمْ أَنَّ اللهَ قَدْ فَرَضَ عَلَيْهِمْ صَدَقَةً تُؤْخَذُ مِنْ أَغْنِيَائِهِمْ فَتُرَدُّ عَلَى فُقَرَائِهِمْ، فَإِنْ هُمْ أَطَاعُوا لَكَ بِذَلِكَ، فَإِيَّاكَ وَكَرَائِمَ أَمْوَالِهِمْ، وَاتَّقِ دَعْوَةَ الْمَظْلُومِ، فَإِنَّهُ لَيْسَ بَيْنَهُ وَبَيْنَ اللهِ حِجَابٌ».
Daga Abdullahi Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce wa Mu'azu Dan Jabal, lokacin da ya aike shi zuwa Yaman: "Lallai kai zaka je wa wasu mutane mazowa littafi, idan ka je musu to ka kirayesu zuwa su shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa Annabi Muhammad Manzon Allah ne, idan su sun bika a kan hakan, to ka sanar da su cewa Allah Ya wajabta musu salloli biyar a kowanne yini da dare, idan su sun bika da hakan, to ka sanar da su cewa Allah Ya wajabta musu sadaka da za'a karba daga mawadatan su sai a dawo da ita ga talakawansu, idan su sun bika da hakan, to na haneka da manyan dukiyoyin su, ka tsoraci addu'ar wanda aka zalinta, lallai cewa ita babu wani shamaki tsakanin ta da Allah".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aiki Mu'azu Dan Jabal zuwa garuruwan Yaman yana mai kira zuwa ga Allah kuma mai ilimantarwa, ya bayyana masa cewa shi zai fuskanci wasu mutane daga Nasara; dan ya zama akan yi musu tanadi, sannan ya fara da mafi muhimmaci sannan mafi muhimmanci a kiran nasu, Sai ya kirasu zuwa gyara akida a farko; da cewa su shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne; Domin cewa da ita ne za su shiga Musulunci, idan sunyi imani da hakan sai ya umarcesu da tsaida sallah' domin cewa ita ce mafi girman wajibai bayan Tauhidi. Idan sun tsaida ita sai ya umarci mawadatan su da bada zakkar dukiyoyin su zuwa talakawansu, sannan ya gargade shi daga karbar mafificiyar dukiya; domin cewa wajibi shi ne tsaka-tsakiya, Sannan yayi masa wasicci da nisantar zalinci' dan kada wanda aka zalinta yayi masa mummunar addu'a domin cewa addu'arsa abar karbace.

Fa’idoji
  1. Ma'anar shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi ne kadaita Allah da bauta, da barin bautar abinda ba shi ba.
  2. Ma'anar shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne shi ne imani da shi da kuma abinda ya zo da shi da gasgata shi, kuma cewa shi ne karshen Manzannin Allah zuwa ga dan Adam..
  3. Lallai cewa magana da mai ilimi da wanda yake tare da wata shubuha ba ta zama kamar magana da jahili ba; saboda haka ya fadakar da Mu'azu da fadinsa: "Lallai cewa kai zaka zo wa wasu mutane ma'abota littafi".
  4. Muhimmancin musulmi ya zama akan basira ga addininsa; dan ya kubuta daga shubuhohin masu sa shubuha, wannan ta hanyar neman ilimi kenan.
  5. Bacin addinin Yahudawa da Nasara bayan aiko Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma cewa su ba su zama daga masu tsira ba a ranar Kiyama har sai sun shiga addinin Allah, kuma sun yi imani da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.
Madogara

صحيح البخاري (2/ 119) (1458)، (2/ 128) (1496)، (9/ 114) (7372). صحيح مسلم (1/ 50) (19). فتح الباري لابن حجر (13/ 349). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح فوزان (ص54). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص64).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

ya rabauta idan gasgata hakan

عَنْ طَلْحَةَ بْنِ عُبَيْدِ اللهِ رضي الله عنه قَالَ: جَاءَ رَجُلٌ إِلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مِنْ أَهْلِ نَجْدٍ ثَائِرُ الرَّأْسِ، نَسْمَعُ دَوِيَّ صَوْتِهِ، وَلَا نَفْقَهُ مَا يَقُولُ حَتَّى دَنَا مِنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَإِذَا هُوَ يَسْأَلُ عَنِ الْإِسْلَامِ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «خَمْسُ صَلَوَاتٍ فِي الْيَوْمِ وَاللَّيْلَةِ» فَقَالَ: هَلْ عَلَيَّ غَيْرُهُنَّ؟ قَالَ: «لَا، إِلَّا أَنْ تَطَّوَّعَ، وَصِيَامُ شَهْرِ رَمَضَانَ»، فَقَالَ: هَلْ عَلَيَّ غَيْرُهُ؟ فَقَالَ: «لَا، إِلَّا أَنْ تَطَّوَّعَ»، وَذَكَرَ لَهُ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الزَّكَاةَ، فَقَالَ: هَلْ عَلَيَّ غَيْرُهَا؟ قَالَ: «لَا، إِلَّا أَنْ تَطَّوَّعَ»، قَالَ: فَأَدْبَرَ الرَّجُلُ، وَهُوَ يَقُولُ: وَاللهِ، لَا أَزِيدُ عَلَى هَذَا، وَلَا أَنْقُصُ مِنْهُ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَفْلَحَ إِنْ صَدَقَ».
Daga Dalha ɗan Ubaidullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum daga mutanen Najad ya zo wurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mai dattin kai, muna jin ƙarfin muryarsa, ba ma fahimtar abinda yake faɗa har ya kusanto ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai gashi yana tambaya game da musulunci, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Salloli biyar a yini da dare" sai ya ce: Shin akwai wasu kuma akaina? ya ce: "A'a, sai dai idan ka yi nafila. Da azumin Ramadan”. Sai ya ce: Shin akwai wani kuma?. sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Saidai idan ka yi na nafila. Sai ya ambata masa zakka, sai ya ce: Shin akaina akwai waninta ? ya ce: "A'a, saidai idan ka yi nafila", ya ce: Sai mutumin ya juya baya, yana cewa: Na rantse da Allah, ba zan kara akan wannan ba, kuma ba zan rage daga gare su ba, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce ya rabauta idan gasgata hakan".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wani mutum daga cikin mutanen Najad ya zo wurin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - gashinsa ya yi datti, kuma muryarsa mai ƙarfi, ba'a fahimtar abinda yake faɗa, har ya kusanto ga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya yi tambaya game da farillan musulunci? Sai annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara da sallah, kuma ya sanar da shi cewa Allah Ya faralanta masa salloli biyar a cikin kowanne yini da dare. Sai ya ce: Shin wani abu daga salloli sun wajaba a kaina banda waɗannan biyar ɗin? Sai ya ce: A'a, sai dai idan ka yi nafila daga sallolin nafila. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Daga abinda Allah Ya wajabta shi akanka azumin watan Ramadan. Sai mutumin ya ce: Shin akwai wani abu na azimi da ya wajaba a kaina banda azimin Ramadan? Sai ya ce: A'a, saidai idan ka yi nafila da wani azimi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ambata masa zakka. Sai mutumin ya ce: Shin wani abu na sadaka bayan farillar zakka ya wajaba a kaina? Ya ce: A'a, saidai idan ka yi nafila. Bayan mutumin ya ji waɗannan bayanai daga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya juya baya ya yi rantsuwa da Allah - Maɗaukakin sarki - cewa shi zai dawwama a kansu ba tare da ƙari ko ragi ba, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce bayan haka: Idan ya gasgata abinda ya faɗa akan abinda ya rantse akansa to shi zai zama daga masu rabauta.

Fa’idoji
  1. Saukin shari’ar musulunci da sauƙinta akan wadanda aka dorawa ita.
  2. Kyakkyawan mu'amalarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga wannan mutumin, haƙiƙa ya ba shi damar zuwa kusa da shi da kuma tambayarsa.
  3. Farawa a cikin Da’awah zuwa ga Allah - Maɗaukkain sarki - da mafi muhimmanci sai mafi muhimmanci.
  4. Musulunci aƙida ne da aiki, ba wani aiki da zai yi amfani ba tare da imani ba, kuma imani ba ya amfani ba tare da aiki ba.
  5. Muhimmancin waɗannan ayyukan kuma cewa su suna daga rukunan musulunci.
  6. Sallar Juma'a tana shiga cikin salloli biyar na wajibai; domin ita Juma’a canji ce daga sallar azahar ɗin ranar Juma'a ga wanda ta wajaba akansa.
  7. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara koyar da shi mafi ƙarfin farillan musulunci su ne rukunansa bayan kalamar shahada; domin shi ya kasance musulmi ne, bai ambaci hajji ba; domin shi kafin a wajabta shi ne, ko kuma shi lokacinsa bai zo ba.
  8. Idan mutum ya taƙaita akan wajibi a cikin shari'a to shi ya rabauta, sai dai wannan ba ya nufin ba'a sunnanta masa ya zo da nafila ba; domin nafila farillai suna cika da ita ne a ranar AlKiyama.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 18) (46). صحيح مسلم (1/ 40) (11). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين. بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (2/ 346). نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (2/ 857). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 242).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

An umurce ni da in yaki mutane har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne, su tsaida sallah, su bayar da zakka

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «أُمِرْتُ أَنْ أُقَاتِلَ النَّاسَ حَتَّى يَشْهَدُوا أَنْ لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَيُقِيمُوا الصَّلاَةَ، وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ، فَإِذَا فَعَلُوا ذَلِكَ عَصَمُوا مِنِّي دِمَاءَهُمْ وَأَمْوَالَهُمْ إِلَّا بِحَقِّ الإِسْلاَمِ، وَحِسَابُهُمْ عَلَى اللَّهِ».
Daga Dan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "An umurce ni da in yaki mutane har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne, su tsaida sallah, su bayar da zakka, idan suka aikata hakan sun tsare jinanensu da dukiyoyinsu daga gareni sai dai da hakkin Musulunci, kuma hisabinsu yana ga Allah".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Ya umarce shi da yakar mushrikai har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Shi da abokin tarayya, kuma su shaida manzanci ga (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da aiki da abinda wannan shaidar ta hukunta na kiyayewa akan salloli biyar a yini da dare, kuma su bada zakka ta wajibi ga wadanda suka cancanta. Idan suka aikata wadannan al'amuran to Musulunci ya tsare jinanensu da dukiyoyinsu, kashe su ba ya halatta sai dai idan sun aikata laifi ko wata barnar da za su cancanci kisa akanta, ta hanyar wajabcin hukunce-hukuncen Musulunci, sannan ranar AlKiyama Allah - Madaukakin sarki - Zai jibinci hisabunsu inda Yake sanin sirrikansu.

Fa’idoji
  1. Hukunce-hukunce kawai suna gudana ne akan zahiri, Allah ne Yake jibintar sirrika.
  2. Muhimmanci kira zuwa Tauhidi kuma cewa shi ne farkon abinda za'a fara da shi a Da'awa.
  3. Wannan Hadisin ba ya nufin tilasta mushrikai kan shiga Musulunci ba, kai su wadanda aka bai wa zabi ne tsakanin shiga Musulunci ko bada jizya, idan suka ki, sai hana kira zuwa ga Musulunci, to babu makwa sai yaki ta hanyar dokokin hukunce-hukuncen Musulunci.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 14) (25). صحيح مسلم (1/ 53) (22). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، لإسماعيل السعدي (ص23). شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص125).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Haƙiƙa ka tambayeni daga wani abu mai girma, kuma shi mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa

عَنْ مُعَاذِ بْنِ جَبَلٍ رضي الله عنه قَالَ: كُنْتُ مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي سَفَرٍ، فَأَصْبَحْتُ يَوْمًا قَرِيبًا مِنْهُ وَنَحْنُ نَسِيرُ، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ أَخْبِرْنِي بِعَمَلٍ يُدْخِلُنِي الجَنَّةَ وَيُبَاعِدُنِي عَنِ النَّارِ، قَالَ: «لَقَدْ سَأَلْتَنِي عَنْ عَظِيمٍ، وَإِنَّهُ لَيَسِيرٌ عَلَى مَنْ يَسَّرَهُ اللَّهُ عَلَيْهِ، تَعْبُدُ اللَّهَ وَلاَ تُشْرِكْ بِهِ شَيْئًا، وَتُقِيمُ الصَّلاَةَ، وَتُؤْتِي الزَّكَاةَ، وَتَصُومُ رَمَضَانَ، وَتَحُجُّ البَيْتَ» ثُمَّ قَالَ: «أَلاَ أَدُلُّكَ عَلَى أَبْوَابِ الخَيْرِ: الصَّوْمُ جُنَّةٌ، وَالصَّدَقَةُ تُطْفِئُ الخَطِيئَةَ كَمَا يُطْفِئُ الْمَاءُ النَّارَ، وَصَلاَةُ الرَّجُلِ مِنْ جَوْفِ اللَّيْلِ» قَالَ: ثُمَّ تَلاَ: «{تَتَجَافَى جُنُوبُهُمْ عَنِ الْمَضَاجِعِ}، حَتَّى بَلَغَ {يَعْمَلُونَ}» ثُمَّ قَالَ: «أَلاَ أُخْبِرُكَ بِرَأْسِ الأَمْرِ كُلِّهِ وَعَمُودِهِ، وَذِرْوَةِ سَنَامِهِ؟» قُلْتُ: بَلَى يَا رَسُولَ اللهِ، قَالَ: «رَأْسُ الأَمْرِ الإِسْلاَمُ، وَعَمُودُهُ الصَّلاَةُ، وَذِرْوَةُ سَنَامِهِ الجِهَادُ» ثُمَّ قَالَ: «أَلاَ أُخْبِرُكَ بِمَلاَكِ ذَلِكَ كُلِّهِ؟» قُلْتُ: بَلَى يَا نَبِيَّ اللهِ، فَأَخَذَ بِلِسَانِهِ قَالَ: «كُفَّ عَلَيْكَ هَذَا» فَقُلْتُ: يَا نَبِيَّ اللهِ، وَإِنَّا لَمُؤَاخَذُونَ بِمَا نَتَكَلَّمُ بِهِ؟ فَقَالَ: «ثَكِلَتْكَ أُمُّكَ يَا مُعَاذُ، وَهَلْ يَكُبُّ النَّاسَ فِي النَّارِ عَلَى وُجُوهِهِمْ أَوْ عَلَى مَنَاخِرِهِمْ إِلاَّ حَصَائِدُ أَلْسِنَتِهِمْ».
Daga Mu'az Bin Jabal -Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wata tafiya, sai na wayi gari wata rana a kusa da shi alhali mu muna tafiya, sai na ce: Ya Manzon Allah ka bani labarin aikin da zai shigar dani aljanna kuma ya nisantar dani daga wuta, sai ya ce: "Haƙiƙa ka tambayeni daga wani abu mai girma, kuma shi mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa, ka bautawa Allah kada ka yi shirka da komai da Shi, ka tsaida sallah, ka bada zakka, ka azimci Ramadan, ka ziyarci Ɗakin Allah”, sannan ya ce: "Shin ba na shiryar dakai ba ga ƙofofin alheri: Azimi garkuwa ne, sadaka tana kashe kuskure kamar yanda ruwa yake kashe wuta, da sallar mutum a tsakiyar dare" ya ce: Sannan ya karanta: "{Sasanninsu suna nisanta daga makwantansu}, har ya kai {Suke aikatawa}". Sannan ya ce: "Shin bana baka labari da asalin al'amari gaba dayansa ba da ginshikinsa, da kololuwar tozansa?" Na ce: Eh, ya Manzon Allah, ya ce: "Asalin al'amari Musulunci, kuma ginshikinsa sallah, kuma kololuwar tozansa Jihadi" sannan ya ce: "Shin bana baka labari da abinda zai tattaro hakan gaba dayansa ba?" na ce: Eh, Ya Manzon Allah, sai ya rike harshensa ya ce: "Ka rike wannan", na ce Shin za’a kama mu da abinda muke magana da shi? ya ce: "Babarka ta yi wabinka ya Mu'az, ai ba wani abu ne yake afka mutane cikin wuta ta fuskokinsu ko ta hancinansu ba sai abinda harasansu suke girba".
Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shiDarajaIngantacce ne a baki dayan hanyoyin sa
Sharhi

Mu'az - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wata tafiya, sai na wayi gari wata rana a kusa da shi alhali mu muna kan tafiya, sai na ce: Ya Manzon Allah ka bani labarin aikin da zai shigar da ni aljanna kuma ya nisantar dani daga wuta, Ya ce: Haƙiƙa ka tambayeni daga wani aiki mai girman aikatawa ga rayuka, kuma mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa; ka yi farillan Musulunci: Na farko: Ka bauta wa Allah Shi kaɗai kada ka taranya wani abu da Shi. Na biyu: Ka tsaida salloli biyar na farilla a yini da dare: Asuba, da Azahar, da La'asar, da Magariba, da Isshai, da sharuɗɗansu da rukunansu da wajibansu. Na uku: Ka fitar da zakkar farilla, ita ce ibada ta dukiya wajiba a kowace dukiyar da takai wani gwargwado abin iyakancewa a shari'a, ana bada ita ga waɗanda suka cancanceta. Na huɗu: Ka azimci Ramadan, shi ne kamewa daga ci da sha da wasunsu daga abubuwan da suke karya azimi da niyyar bauta, daga ɓollowar alfijir zuwa faɗuwar rana. Na biyar: Ka ziyarci Ɗakin Allah, da nufin Makka dan yin ibadun aikin Hajji, dan bauta ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Shin ba na sanar da kai hanya mai kaiwa ga ƙofofn alheri ba? hakan da bin waɗancan farillan da nafilfilin: Na farko: Azimin nafila, shi mai hanawa ne daga afkawa cikin saɓo, hakan da karya sha'awa, da kuma rage ƙarfi. Na biyu: Sadakar nafila tana kashe laifuka bayan an aikata su kuma tana tafiyar da su tana kuma shafe su. Na uku: Sallar dare a kashi ɗaya bisa uku na ƙarshen dare, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya karanta faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Sasanninsu suna nisanta} wato: Suna nisanta {Daga makwantansu} wato: Wuraren kwana { Suna kiran Ubangijinsu} da yin sallah da zikiri da karatu da addu'a, {Dan tsoro da kwaɗayi kuma suna ciyarwa daga abinda muka azirta su, wata rai bata sanin abinda aka ɓoye musu na abinda ido yake farin ciki da shi} wato abinda idanunsu zasu yi farin ciki da shi a ranar Alƙiyama da kuma aljanna ta ni'ima, {Dan sakamako da abinda suka kasance suna aikatawa}. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Shin bana baka labari da asalin Addini ba? da ginshiƙinsa wanda yake dogaro akansa? da ƙololuwar tozansa? Mu'az - Allah Ya yarda ad shi - ya ce: Eh, ya Manzon Allah. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Asalin al'amari: Musulunci shi ne shaidawa biyu, kuma dasu ne tushen Addini zai wayi gari tare da mutum. Ginshiƙinsa: Sallah, babu Musulunci ba tare da sallah ba, kamar yadda babu gida ba tare da ginshiƙi ba, wanda ya yi sallah Addininsa zai ƙarfafa zai ɗaga; kuma ƙololuwar tozansa da ɗaukakarsa yana kasancewa ne da yin yaƙi da yin ƙoƙari a yaƙar maƙiya Addini dan ɗaukaka kalmar Allah. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Shin ba na baka labari da kyautata abinda ya gabata ba? sai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe harshensa, ya ce: Ka hana wannan kada ka yi magana da abinda bai shafeka ba. Mu'az ya ce: Shin Ubangijinmu zai kamamu Ya yi mana hisabi da dukkan abinda muke magana da shi?! Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Mahaifiyarka ta yi wabinka! ba ana nufin mummunar addu'a akansa ba, sai dai yana daga zancen larabawa dan faɗakar da shi zuwa wani al'amarin da ya kasance yana kamata ya farka da shi ya kuma san shi, sannan ya ce: Ai babu abinda yake afka mutane ya jefasu cikin wuta ta fuskokinsu sai abinda harasansu suke girba na kafirci da ƙazafi da zagi da yi da mutum da annamimanci da ƙagen ƙarya da makamancinsu.

Fa’idoji
  1. Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan ilimi, saboda haka ne tambayar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - take yawaita daga garesu.
  2. zirfin ilimin sahabbai - Allah Ya yarda da su - dan saninsu cewa ayyuka sababi ne na shiga aljanna.
  3. Tambayar data fito daga Mu'az - Allah Ya yarda da shi - tambaya ce mai girma; domin cewa shi a haƙiƙa shi ne sirrin rayuwa da samuwa, dukkan samamme a cikin wannan rayuwar ta duniya daga 'ya'yan Adam ko daga aljanu ƙarshensa kodai aljanna ko wuta, saboda haka ne wannan tambayar ta zama mai girma.
  4. Jeranta shigarsa aljanna akan zuwa da rukunan Musulunci guda biyar, su ne: Shaidawa biyu da Sallah da Zakka da Azimi da Hajji.
  5. Asalin Addini kuma mafi tsadar abubuwa muhimmai kuma mafi ɗaukakar wajibai (su ne) kaɗaita Allah, da bauta maSa Shi kaɗai baShi da abokin tarayya.
  6. Rahamar Allah ga bayinSa cewa Ya buɗe musu ƙofofin alheri dan su yi guziri daga sabubban lada da gafarta zunubai.
  7. Falalar neman kusanci (ga Allah) da nafilfili bayan yin farillai.
  8. Sallah a cikin Musulunci kamar ginshiƙin da runfa take tsaye a kansa ne, Musulunci yana tafiya ne da tafiyata, kamar yadda runfa take faɗuwa da faɗuwar ginshiƙinta.
  9. Wajabcin kiyaye harshe daga abinda zai cutar da mutum a cikin Addininsa.
  10. Kame harshe da kiyaye shi da tsare shi shi ne asalin alheri gaba ɗayansa.
Madogara

سنن الترمذي (4/ 362) (2616). سنن ابن ماجه (5/ 116) (3973). مسند أحمد (36/ 344) (22016). التحفة الربانية، لإسماعيل الأنصاري (ص67). شرح الأربعين النووية، للعثيمين (ص291). الأحاديث الأربعين النووية مع ما زاد عليها ابن رجب وعليها الشرح الموجز المفيد، لعبد الله بن صالح المحسن (ص57).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kada ka kashe shi, domin cewa in ka kashe shi to shi yana matsayinka kafin ka kashe shi, kuma kai kana matsyinsa kafin ya fadi kalmarsa wacce ya fadeta

عَنْ المِقْدَادِ بْنَ عَمْرٍو الكِنْدِيَّ رضي الله عنه: أَنَّهُ قَالَ لِرَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَرَأَيْتَ إِنْ لَقِيتُ رَجُلًا مِنَ الكُفَّارِ فَاقْتَتَلْنَا، فَضَرَبَ إِحْدَى يَدَيَّ بِالسَّيْفِ فَقَطَعَهَا، ثُمَّ لاَذَ مِنِّي بِشَجَرَةٍ، فَقَالَ: أَسْلَمْتُ لِلَّهِ، أَأَقْتُلُهُ يَا رَسُولَ اللَّهِ بَعْدَ أَنْ قَالَهَا؟ فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لاَ تَقْتُلْهُ» فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ إِنَّهُ قَطَعَ إِحْدَى يَدَيَّ، ثُمَّ قَالَ ذَلِكَ بَعْدَ مَا قَطَعَهَا؟ فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لاَ تَقْتُلْهُ، فَإِنْ قَتَلْتَهُ فَإِنَّهُ بِمَنْزِلَتِكَ قَبْلَ أَنْ تَقْتُلَهُ، وَإِنَّكَ بِمَنْزِلَتِهِ قَبْلَ أَنْ يَقُولَ كَلِمَتَهُ الَّتِي قَالَ».
Daga Miƙdadu ɗan Amr mutumin Kindi - Allah Ya yarda da shi -: Cewa shi ya cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Shin kana ganin cewa idan na haɗu da wani mutum daga kafirai sai muka yi faɗa, sai ya daki ɗaya daga hannayena da takobi sai ya yanke shi, sannan ya fake dani da wata bishiya, sai ya ce: Na miƙa wuya ga Allah, shin zan kashe shi ya Manzon Allah bayan ya faɗeta? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ka kashe shi" sai ya ce: Ya Manzon Allah lallai cewa shi ya yanke mini ɗaya daga hannayena, sannan ya faɗi hakan bayan ya yanke mini shi? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ka kashe shi, domin cewa in ka kashe shi to shi yana matsayinka kafin ka kashe shi, kuma kai kana matsyinsa kafin ya fadi kalmarsa wacce ya fadeta".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Mikdadu ɗan alAswad - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi idan ya gamu da wani mutum daga kafirai a yaƙi, sai suka yi fito na fito da takubba, har kafirin ya samu ɗaya daga hannayen sa da takobi sai ya yanke shi, sannan kafirin ya gudu daga gare shi ya katangantu da wata bishiya, sai ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shin ya halatta a gareni in kashe shi bayan ya yanke hannuna? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: Kada ka kashe shi. Sai ya ce ya Manzon Allah, lallai cewa shi ya yanke ɗayan hannayena, shin a tare da hakan ba zan kashe shi ba? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Kada ka kashe shi, domin cewa shi ya wayi gari jininsa haramun ne, domin cewa kai in ka kashe shi bayan musuluntarsa; to cewa shi a matsayinka ne wanda jininsa abin tsarewa ne da musuluntarsa, kuma kai kana matsayinsa abin halaratawar jini da ka kashe shi dan yin ƙisasi.

Fa’idoji
  1. Wanda abinda yake nuni akan shiga Musulunci ya bijiro daga gare shi na magana ne ko na aiki to kashe shi ya haramta.
  2. Idan ɗaya daga kafirai ya Musulunta a tsakiyar yaƙi, to haƙiƙa an tsare jininsa, kuma kamewa daga gare shi ya wajaba sai dai idan saɓanin hakan ya bayyana daga gare shi.
  3. Yana wajaba akan musulmi da son ransa ya zama bi ne ga shari'a badan ƙabilanci ko ɗaukar fansa ba.
  4. Ibnu Hajar ya ce: Halaccin tambaya daga (mas'aloli) masu rintshi kafin afkuwarsu dan gini akan rinjayar da cewa ƙissar ba ta afku ba, amma abinda aka ruwaito daga wasu daga magabata daga ƙin hakan to shi abin ɗauka ne akan abinda afkuwarsa yake ƙaranta, amma abinda afkuwarsa yake yi wuwa a al'ada to an shara'anta tambaya game da shi dan a sani.
Madogara

صحيح البخاري (5/ 85) (4019). صحيح مسلم (1/ 95) (95). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 359). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 461). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (6/ 345). المعجم الوسيط، (2/ 815).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya Usama, shin ka kashe shi bayan ya ce: Babu wani abin bauta sai Allah?

عن أسامة بن زيد رضي الله عنهما ، قال: بَعَثَنَا رسولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم إلى الحُرَقَةِ من جُهَيْنَةَ فَصَبَّحْنَا القَوْمَ على مِيَاهِهِم، ولَحِقْتُ أنا ورجلٌ من الأنصارِ رجلًا منهم، فلما غَشِينَاهُ، قال: لا إله إلا الله، فَكَفَّ عنه الأَنْصَارِيُّ، وطَعَنْتُهُ بِرُمْحِي حَتَّى قَتَلْتُهُ، فَلَمَّا قَدِمْنَا المدينةَ، بَلَغَ ذَلِكَ النبيَّ صلى الله عليه وسلم فقال لي: «يا أسامةُ، أَقَتَلْتَهُ بَعْدَ مَا قَالَ: لا إلهَ إلَّا اللهُ؟!» قُلْتُ: يا رسولَ اللهِ، إنما كان مُتَعَوِّذًا، فقال: «أَقَتَلْتَهُ بعد ما قال: لا إلهَ إلَّا اللهُ؟!» فَمَا زَالَ يُكَرِّرُهَا عَلَيَّ حتى تَمَنَّيْتُ أَنِّي لم أَكُنْ أَسْلَمْتُ قَبْلَ ذَلِكَ اليَوْمِ. وفي رواية: فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «أَقَالَ: لا إلهَ إلا اللهُ وَقَتَلْتَهُ؟!» قُلْتُ: يا رسولَ اللهِ، إنما قَالَهَا خَوْفًا من السِّلَاحِ، قال: «أَفَلَا شَقَقْتَ عَنْ قَلْبِهِ حَتَّى تَعْلَمَ أَقَالَهَا أَمْ لَا؟!» فَمَا زَالَ يُكَرِّرُهَا حَتَّى تَمَنَّيْتُ أَنِّي أَسْلَمْتُ يَوْمَئِذٍ. وعن جندب بن عبد الله رضي الله عنه : أن رسول الله صلى الله عليه وسلم بَعَثَ بَعْثًا مِن المسلمينَ إلى قومٍ من المشركينَ، وأنهم الْتَقَوا، فَكَانَ رجلٌ مِن المشركينَ إذا شَاءَ أَنْ يَقْصِدَ إلى رجلٍ مِن المسلمينَ قَصَدَ له فَقَتَلَهُ، وأَنَّ رجلًا مِن المسلمينَ قَصَدَ غَفْلَتَهُ. وكُنَّا نَتَحَدَّثُ أَنَّهُ أسامةُ بْنُ زيدٍ، فَلَمَّا رَفَعَ عَلَيْهِ السَّيْفَ، قال: لا إلهَ إلا اللهُ، فَقَتَلَهُ، فجاءَ البَشِيرُ إلى رسولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم فَسَأَلَهُ وأَخْبَرَهُ، حتى أَخْبَرَهُ خَبَرَ الرجلِ كَيْفَ صَنَعَ، فَدَعَاهُ فَسَأَلَهُ، فقال: «لِمَ قَتَلْتَهُ؟» فقال: يا رسولَ اللهِ، أَوْجَعَ في المسلمينَ، وقَتَلَ فُلانًا وفُلانًا، وسَمَّى له نَفَرًا، وإِنِّي حَمَلْتُ عليهِ، فَلَمَّا رَأَى السَّيْفَ، قال: لا إلهَ إلا اللهُ. قال رسولُ اللهِ صلى الله عليه وسلم : «أَقَتَلْتَهُ؟» قال: نعم. قال: «فَكَيْفَ تَصْنَعُ بلا إلهَ إلا اللهُ، إذا جَاءَتْ يَومَ القِيَامَةِ؟» قال: يا رسولَ اللهِ، اسْتَغْفِرْ لِي. قال: «وكَيْفَ تَصْنَعُ بلا إلهَ إلا اللهُ إذا جَاءَتْ يَوْمَ القِيَامَةِ؟» فجعل لا يَزِيدُ على أَنْ يقولَ: «كَيْفَ تَصْنَعُ بلا إلهَ إلا اللهُ إذا جَاءَتْ يَوْمَ القيامةِ».
A kan Usama bin Zayd - yardar Allah ta tabbata a gare su - wanda ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya aike mu zuwa Harka ta bangarori biyu, kuma mun zama mutane a kan ruwan su, sai dayan su ya hada ku. Al-Ansari, na soke shi da mashina har sai da na kashe shi, lokacin da muka zo Madina, wannan ya isa ga Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- don haka ya ce da ni: "Ya Allah, shin ka kashe shi?!" Oh Allah, ka kashe shi?! Na ce: Ya Manzon Allah, kawai ya kasance mai ba da shawara ne, sai ya ce: Shin ka kashe shi ne a bayan abin da ya ce: Babu wani abin bauta sai Allah? Har yanzu yana maimaita min har sai da nayi fatan ban musulunta ba kafin wannan ranar. Kuma a cikin wata ruwaya: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ya ce:" Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma kun kashe shi?! " Na ce: Ya Manzon Allah, kawai ya fada ne saboda tsoron makami. Ya yi ta maimaitawa har sai da na yi fata da na musulunta a wannan ranar. Daga Jundub bin Abdullah - yardar Allah ta tabbata a gare shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya aiko da sako daga musulmai zuwa ga mutanen mushrikai, sai suka ji tsoro, don haka idan yana son zuwa wurin wani mutum Musulmi, sai ya tafi zuwa gare shi. Na musulmin da aka yi niyya su kau da kai. Muna magana ne cewa Usama bin Zaid, lokacin da ya daga takobin, sai ya ce: Babu wani abin bauta sai Allah, yana kashe shi, sai Bashir ya zo wurin Manzon Allah, amincin Allah ya tabbata a gare shi, ya tambaye shi ya gaya masa, har ma ya gaya masa labarin mutumin yadda ake kerawa, ya kira shi ya tambaye shi, ya ce: «bai kashe shi ba ? » Ya ce: Ya Manzon Allah, ya kasance yana jin zafi a tsakanin Musulmi, sai ya kashe haka da mai haka da haka, kuma ya kira shi kungiya, ni kuma na dauke shi a kansa, don haka da ya ga takobi, sai ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Shin ka kashe shi? Ya ce: Na'am. Ya ce: Yaya za ku yi in ba tare da Allah ba face Allah, idan ta kasance a ranar tashin kiyama? Ya ce: Ya Manzon Allah, ka nema mini gafara. Ya ce: "Yaya za ku yi ba tare da Allah ba idan ba Allah ba idan ta zo ranar tashin kiyama?" Bai yi komai ba sai cewa ya yi: "Ta yaya za ku yi ba tare da Allah ba sai Allah idan ta kasance a ranar tashin kiyama"
Muslim ne ya rawaito shi duka Riwar ta sa biyun - Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

رياض الصالحين، للنووي، نشر: دار ابن كثير للطباعة والنشر والتوزيع، دمشق – بيروت، تحقيق: ماهر ياسين الفحل، الطبعة: الأولى، 1428هـ - 2007م. دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لابن علان، نشر دار الكتاب العربي. نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الرابعة عشر، 1407ه 1987م. شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين، نشر: دار الوطن للنشر، الرياض، الطبعة: 1426ه. كنوز رياض الصالحين، نشر: دار كنوز إشبيليا، الطبعة: الأولى، 1430ه 2009م. بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين لسليم الهلالي، ط1، دار ابن الجوزي، الدمام، 1415ه. صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422ه. صحيح مسلم، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kwatankwacin muminai a soyayyarsu da jinkansu da tausayinsu tamkar jiki ne, idan wata gaba daga gare shi ta yi ciwo sai ragowar jikin ya dauka da rashin bacci da zazzabi

عَنِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَثَلُ الْمُؤْمِنِينَ فِي تَوَادِّهِمْ وَتَرَاحُمِهِمْ وَتَعَاطُفِهِمْ مَثَلُ الْجَسَدِ، إِذَا اشْتَكَى مِنْهُ عُضْوٌ تَدَاعَى لَهُ سَائِرُ الْجَسَدِ بِالسَّهَرِ وَالْحُمَّى».
Daga Nu'uman Dan Bashir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kwatankwacin muminai a soyayyarsu da jinkansu da tausayinsu tamkar jiki ne, idan wata gaba daga gare shi ta yi ciwo sai ragowar jikin ya dauka da rashin bacci da zazzabi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa yana wajaba halin musulmai sashinsu tare da sashi ya zama da son alheri da tausayi da taimakekeniya da taimako, da jin zafin abinda ya faru gare su na cuta kamar jiki daya ne, idan wata gaba ta yi rashin lafiya daga gare shi , sai jikin ya dauka gaba dayansa da rashin bacci da zazzabi.

Fa’idoji
  1. Yana kamata girmama hakkokin musulmai da kwadaitarwa akan taimakekeniyarsu da tausayin junansu.
  2. Yana kamata soyayya da taimako su kasance tsakanin ma'abota imani.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 10) (6011). صحيح مسلم (4/ 1999) (2586). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (1/ 246). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 317). كنوز رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (4/ 405). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص173). المعجم الوسيط (1/ 492).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

An gina Musulunci abisa abubuwa biyar

عَنْ عَبْدِ اللهِ بنِ عُمَر رضي الله عنهما قال: قال رسولُ الله صلى الله عليه وسلم: «بُنِيَ الْإِسْلَامُ عَلَى خَمْسٍ: شَهَادَةِ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، وَإِقَامِ الصَّلَاةِ، وَإِيتَاءِ الزَّكَاةِ، وَحَجِّ الْبَيْتِ، وَصَوْمِ رَمَضَانَ».
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "An gina Musulunci abisa abubuwa biyar, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ziyarar daki, da azimin Ramadan".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta musulunci da ingantaccen gini da rukunansa biyar masu dauke da wancan ginin, ragowar dabi'un musulunci kamar cika ginin ne, Farkon wadanan rukunan: Shaidawa biyu; shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, (shaidawa) Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, su rukuni daya ne; dayansu ba ya rabuwa da dayan, bawa zai furtasu yana mai tabbatar da kadaituwar Allah da kuma cancantarSa ga bauta Shi kadai banda waninSa, kuma yana mai aiki da abinda suka hukunta, kuma yana mai imani da Manzancin Annabi Mukammadu - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana mai binsa. Rukuni na biyu: Tsaida sallah, su ne sallolin farillai biyar a yini da dare: Asuba, da Azahar, da La'asar, da magariba, da Lisha, da sharuddansu da rukunansu da wajibansu. Rukuni na uku: Fitar da zakkar farilla, ita ibada ce ta dukiya wajiba a kowacce dukiyar da takai wani gwargwado abin iyakancewa a shari'a, ana bada ita ga wadanda suka cancanceta. Rukuni na hudu: Hajji, shi ne nufin Makka dan tsaida ibadu, dan yin bauta ga Allah - Mai girma da daukaka -. Rukuni na biyar: Azumin Ramadan, shi ne kamewa daga ci da sha da wasunsu daga masu bata azimi da niyyar bauta ga Allah, daga bullowar alfijir zuwa faduwar rana.

Fa’idoji
  1. Lazimtuwar shaidawa biyu, dayansu ba ya inganta sai da dayan; saboda haka ya sanya su rukuni daya ne.
  2. Shaidawa biyu su ne tushen Addini, ba'a karbar wata magana ko wani aiki sai da su.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 11) (8)، صحيح مسلم (1/ 45) (16)، و(1/ 88) (82)، فتح الباري لابن رجب (1/ 22)، جامع العلوم والحكم (1/147)، شرح الأربعين لابن العطّار (ص 62)، شرح الأربعين النووية لعبد الكريم الخضير (ص 87)، فتح القوي المتين في شرح الأربعين للعباد (ص 29)، شرح الأربعين النووية لصالح آل الشيخ (ص 91 - 95)، التحفة الربانية لإسماعيل الأنصاري (ص 12).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 23
Hadisai 23
  1. Lallai kai zaka je wa wasu mutane mazowa littafi, idan ka je musu to ka kirayesu zuwa su shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa Annabi Muhammad Manzon Allah ne
  2. ya rabauta idan gasgata hakan
  3. An umurce ni da in yaki mutane har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne, su tsaida sallah, su bayar da zakka
  4. Haƙiƙa ka tambayeni daga wani abu mai girma, kuma shi mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa
  5. Kada ka kashe shi, domin cewa in ka kashe shi to shi yana matsayinka kafin ka kashe shi, kuma kai kana matsyinsa kafin ya fadi kalmarsa wacce ya fadeta
  6. Ya Usama, shin ka kashe shi bayan ya ce: Babu wani abin bauta sai Allah?
  7. Kwatankwacin muminai a soyayyarsu da jinkansu da tausayinsu tamkar jiki ne, idan wata gaba daga gare shi ta yi ciwo sai ragowar jikin ya dauka da rashin bacci da zazzabi
  8. An gina Musulunci abisa abubuwa biyar
  9. Wanda ya kyautata a Musulunci ba za'a kama shi da abinda ya aikata ba a lokacin Jahiliyya, wanda kuma ya munana a cikin Musulunci za'a kama shi da na farko da na karshe
  10. Lallai shi bai taba fada ba koda yini daya: Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena ranar sakamako
  11. Shaidan yana zo wa dayanku sai ya ce: Waye ya halicci kaza? waye ya halicci abu kaza? har ya ce: Waye ya halicci Ubanugijinka? idan ya ga haka to (sai) ya nemi tsarin Allah ya kuma hanu
  12. Lallai Allah ba ya zalintar mumini wani kyakkyawa, za'a ba shi a duniya kuma za’a yi masa sakayya da ita a lahira
  13. Ka musulunta akan abinda ka gabatar na alheri
  14. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zantar damu alhali shi mai gaskiya ne abin gasgatawa: "Lallai cewa halittar dayanku ana tarota a cikin mahaifiyarsa yini arba'in da dare arba'in
  15. Ni ne Dimam dan Sa'alabata dan uwan Banu Sa'ad dan Bakar
  16. Yahudawa an yi fushi da su, Kiristoci kuwa batattu ne
  17. Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, zan yi maka shaida da ita ranar Alkiyama
  18. Lallai abin da kake faɗa kuma kake kira zuwa gareshi mai kyau ne, ina ma dai ka sanar da mu cewa akwai kaffara ga abin da muka aikata
  19. Wanda ya sallaci irin sallarmu kuma ya fuskanci alƙiblarmu, kuma ya ci yankanmu to wannan shine muslmin da yake da alƙawarin Allah da alƙawarin ManzonSa, dan haka kada ku warware alƙawarin Allah
  20. Duk mutumin da ya cewa ɗan'uwansa: Ya kai kafiri, to haƙiƙa ɗayansu ya dawo da ita (ya lazimceta), idan ya zama kamar yadda ya ce ne, inba haka bafa to zata dawo kansa
  21. An gina Musulunci abisa abubuwa biyar
  22. Kana ganin idan na sallaci salloli waɗanda aka wajabta, na azimci watan Ramdan, na halatta halal, na haramta haram
  23. Haƙiƙa ka yi tambaya game da wani abu mai girma, kuma cewa shi mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com