Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai Allah ba ya zalintar mumini wani kyakkyawa, za'a ba shi a duniya kuma za’a yi masa sakayya da ita a lahira

عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ اللهَ لَا يَظْلِمُ مُؤْمِنًا حَسَنَةً، يُعْطَى بِهَا فِي الدُّنْيَا وَيُجْزَى بِهَا فِي الْآخِرَةِ، وَأَمَّا الْكَافِرُ فَيُطْعَمُ بِحَسَنَاتِ مَا عَمِلَ بِهَا لِلَّهِ فِي الدُّنْيَا، حَتَّى إِذَا أَفْضَى إِلَى الْآخِرَةِ، لَمْ تَكُنْ لَهُ حَسَنَةٌ يُجْزَى بِهَا».
Daga Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Allah ba ya zalintar mumini wani kyakkyawa, za'a ba shi a duniya kuma za’a yi masa sakayya da ita a lahira. Amma kafiri sai a ciyar da shi da kyakkyawan abinda ya aikata saboda Allah a duniya, har idan ya tafi lahira, (zai zama) ba shi da wani kyakkyawa da za’a yi masa sakayya da shi".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana girman falalar Allah akan muminai, da kuma adalcinSa ga kafirai. Amma mumini ba za’a tauye ladan kyakkyawan da ya aikata ba; kai za'a ba shi ladan kyakkyawa anan duniya akan biyayyarsa, tare da abinda aka tanadar masa na sakayya a lahira; zai iya rabauta da kykkyawa gaba dayansa a lahira. Amma kafiri sai Allah Ya ba shi sakamakon abinda ya aikata na kyakkyawa da kyakkyawan duniya, har idan ya tafi lahira ba shi da wani ladan da za’a yi masa sakayya da shi a lahira; domin aiki na gari wanda zai yi anfani a duniya da lahira ba makawa mai shi sai ya zama mumini.

Fa’idoji
  1. Lallai cewa wanda ya mutu akan kafirci ba wani aiki da zai yi masa anfana.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2162) (2808)، المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (1/ 460)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (43/ 460)، شرح النووي على مسلم (17/150).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Kaɗaita Allah cikin sunayenSa da siffofinSa

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com