Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Allah Zai damke kasa, Zai ninke sammai da hannunSa na dama, sannan Ya ce: Ni ne sarki, ina sarakunan kasa

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «يَقْبِضُ اللَّهُ الأَرْضَ، وَيَطْوِي السَّمَوَاتِ بِيَمِينِهِ، ثُمَّ يَقُولُ: أَنَا المَلِكُ، أَيْنَ مُلُوكُ الأَرْضِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Allah Zai damke kasa, Zai ninke sammai da hannunSa na dama, sannan Ya ce: Ni ne sarki, ina sarakunan kasa".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Madaukakin sarki - a ranar Alkiyama Zai damke kasa Ya tattarota, Ya ninke sama da hannunSa na dama Ya ninke sashinta a saman sashi Ya tafiyar da ita Ya karar da ita, sannan Ya ce: Ni ne sarki, ina sarakunan kasa?!

Fa’idoji
  1. Tinatarwa da cewa mulkin Allah Shi ne wanzajje kuma mulkin waninSa mai gushewa ne.
  2. Girman Allah da girman ikonSa da sarautarSa da cikar mulkinSa.
Madogara

صحيح البخاري (6/ 126) (4812)، صحيح مسلم (4/ 2148) (2787)، فتح الباري (13/367)، عمدة القاري شرح صحيح البخاري (23/ 101)، البحر المحيط الثجاج (43/324).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com