Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Shaidan yana zo wa dayanku sai ya ce: Waye ya halicci kaza? waye ya halicci abu kaza? har ya ce: Waye ya halicci Ubanugijinka? idan ya ga haka to (sai) ya nemi tsarin Allah ya kuma hanu

عَن أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يَأْتِي الشَّيْطَانُ أَحَدَكُمْ فَيَقُولُ: مَنْ خَلَقَ كَذَا؟ مَنْ خَلَقَ كَذَا؟ حَتَّى يَقُولَ: مَنْ خَلَقَ رَبَّكَ؟ فَإِذَا بَلَغَهُ فَلْيَسْتَعِذْ بِاللهِ وَلْيَنْتَهِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shaidan yana zo wa dayanku sai ya ce: Waye ya halicci kaza? waye ya halicci abu kaza? har ya ce: Waye ya halicci Ubanugijinka? idan ya ga haka to (sai) ya nemi tsarin Allah ya kuma hanu".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da maganin abinda ke taso da tambayoyin da Shaidan yake sa wasiwasi akan su ga mumini. Sai Shaidan ya ce: Waye ya halicci abu kaza? waye ya halicci kaza? waye ya halicci sama? kuma waye ya halicci kasa? Sai mumini ya ba shi amsa a Addinance da dabi'ance da hankalce da fadinsa: Allah ne. Saidai Shaidan ba ya tsayawa a wannan iyakar na wasiwasi, kai yana cirata har sai ya ce: Waye ya halicci Ubangijinka? A wannan yayin ne mumini zai ture wadannan wasiwasin da al'amaura uku: Da yin imani da Allah. Da neman tsarin Allah daga Shaidan. Da kuma tsayawa kada ya zarce akan wasuwasin.

Fa’idoji
  1. Bijirewa daga wasiwasin Shaidan da darshe-darshen sa da rashin tunani a kan su, da fakewa zuwa ga Allah - Madaukakin sarki a cikin tafiyar da su.
  2. Dukkanin abinda yake afkuwa a cikin zuciyar mutum na wasuwasin da ya sabawa shari'a to daga Shaidan ne.
  3. Hani daga tinani a cikin zatin Allah, da kwadaitarwa akan tunani a abubuwan halittarSa da kuma ayoyinSa.
Madogara

صحيح البخاري (4/ 123) (3276)، صحيح مسلم (1/ 120) (134)، إكمال المعلم (1/432)، المفهم (1/345)، فتح الباري (6/ 340)، طرح التثريب (8/163)، بهجة قلوب الأبرار (ص 27).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
IMANI DA ALLAH MAI GIRMA DA ƊAUKAKA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com