Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

An umurce ni da in yaki mutane har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne, su tsaida sallah, su bayar da zakka

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «أُمِرْتُ أَنْ أُقَاتِلَ النَّاسَ حَتَّى يَشْهَدُوا أَنْ لاَ إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللَّهِ، وَيُقِيمُوا الصَّلاَةَ، وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ، فَإِذَا فَعَلُوا ذَلِكَ عَصَمُوا مِنِّي دِمَاءَهُمْ وَأَمْوَالَهُمْ إِلَّا بِحَقِّ الإِسْلاَمِ، وَحِسَابُهُمْ عَلَى اللَّهِ».
Daga Dan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "An umurce ni da in yaki mutane har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne, su tsaida sallah, su bayar da zakka, idan suka aikata hakan sun tsare jinanensu da dukiyoyinsu daga gareni sai dai da hakkin Musulunci, kuma hisabinsu yana ga Allah".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Ya umarce shi da yakar mushrikai har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai ba Shi da abokin tarayya, kuma su shaida manzanci ga (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da aiki da abinda wannan shaidar ta hukunta na kiyayewa akan salloli biyar a yini da dare, kuma su bada zakka ta wajibi ga wadanda suka cancanta. Idan suka aikata wadannan al'amuran to Musulunci ya tsare jinanensu da dukiyoyinsu, kashe su ba ya halatta sai dai idan sun aikata laifi ko wata barnar da za su cancanci kisa akanta, ta hanyar wajabcin hukunce-hukuncen Musulunci, sannan ranar AlKiyama Allah - Madaukakin sarki - Zai jibinci hisabunsu inda Yake sanin sirrikansu.

Fa’idoji
  1. Hukunce-hukunce kawai suna gudana ne akan zahiri, Allah ne Yake jibintar sirrika.
  2. Muhimmanci kira zuwa Tauhidi kuma cewa shi ne farkon abinda za'a fara da shi a Da'awa.
  3. Wannan Hadisin ba ya nufin tilasta mushrikai kan shiga Musulunci ba, kai su wadanda aka bai wa zabi ne tsakanin shiga Musulunci ko bada jizya, idan suka ki, sai hana kira zuwa ga Musulunci, to babu makwa sai yaki ta hanyar dokokin hukunce-hukuncen Musulunci.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 14) (25). صحيح مسلم (1/ 53) (22). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، لإسماعيل السعدي (ص23). شرح الأربعين النووية، لابن عثيمين (ص125).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
MUSULUNCI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com