Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

SHIRKA

Hadisai 11

Allah madaukaki yana cewa: {Don haka kada ku sanya wa Allah kima, duk da cewa kun sani.} Ibn Abbas ya fada a cikin ayar cewa: "Aboki: shirka ne, wanda aka boye daga tururuwa da ke dauke da bakar leda a cikin duhun dare.

قول الله تعالى : {فَلا تَجْعَلُوا لِلَّهِ أَنْدَادًا وَأَنْتُمْ تَعْلَمُونَ}. قال ابن عباس في الآية: "الأنداد: هو الشرك، أخفى من دَبِيبِ النمل على صَفَاةٍ سوداء في ظلمة الليل". وهو أن تقول: والله وحياتك يا فلان، وحياتي، وتقول: لولا كُلَيْبَةُ هذا لأتانا اللصوص، ولولا البط في الدار لأتانا اللصوص، وقول الرجل لصاحبه: ما شاء الله وشئت، وقول الرجل: لولا الله وفلان، لا تجعل فيها فلانا؛ هذا كله به شرك".
Allah madaukaki yana cewa: {Don haka kada ku sanya wa Allah kima, duk da cewa kun sani.} Ibn Abbas ya fada a cikin ayar cewa: "Aboki: shirka ne, wanda aka boye daga tururuwa da ke dauke da bakar leda a cikin duhun dare." Ya kamata a ce: Na rantse da Allah da rayuwarku, Ya-da-haka, da rayuwata, sai ta ce: Ba don wannan bala'in ba, da barayi sun zo mana, kuma ba don agwagi a cikin gida ba barayi sun zo gare mu, kuma maganar mutumin ga abokin nasa: Abin da Allah yake so da abin da yake so, da kuma maganar mutumin: Ba don Allah da haka-da-haka ba, kuma kada a sanya hakan. Wannan duk shirka ne. "Dan Abbas Allah ya kara yarda a gare su ya ce: cikin ayar: Al'Andadu: shine shirka, ita tafi daga tafiyar tururuwa akan fan dutse cikin duhun dare, kuma shine kace: na rantse da Allah da rayuwarka wane da rayuwata! kuma kace: ba dan karen nan ba da Barayi sun zo mana, ko kuma ba dan agwagin cikin gidan ba, da Barayi sun zo mana, da fadin Mutum ga abokin sa: Allah ya so kuma kaima ka so, da fadin Mutum: ba don Allah da wane ba,kada ka sanya kowa acikin ta,wan nan baki dayan sa akwai shirka acikin sa.Dan Abi Hatim ne ya rawaito shi.
Abu Hatim ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Allah - Albarkace da daukaka - ya ce: {Don haka kada ku sanya daidai da Allah, duk da cewa kun sani.Saboda haka ya hana mutane daukar karin magana da sahihancin ra'ayi a gare shi a matsayin wani abu na bautarsa. Sun san cewa Allah shi kaɗai ne Mahalicci kuma Mai azurtawa. Kuma cewa wadannan takwarorin ba su da karfi, matalauta ne, kuma ba su da komai game da lamarin, kuma Ibn Abbas - Allah ya yarda da shi - ya san takwarorinsu tare da abokan tarayya, kuma ya ambaci misalai don daukar su, kuma ya buya daga boyewar tururuwa a kan dutsen sumul mai santsi a cikin duhun dare, sannan ya ambata misalan hakan: wanda ake rantsuwa da shi Da wani abu ba Allah ba, kuma mafi girma shi ne a daidaita Allah da shi sai a ce: Na rantse da Allah da raina, ko kuma in kalli abin ba tare da dalili ba, kuma al'amarin ba zai koma ga Allah ba, sai ta ce: Idan ba don kare ba, wannan da ya tsare mu, da barayi sun zo mana, ko ya ce: Idan ba don agwagwar da ke cikin gidan ba, zai yi mana gargaɗi idan wani ya shigo gidan Barayi, kuma daga shirka: maganar mutum ga mai shi: Abin da Allah yake so da abin da yake so, da kuma fadin mutum: Idan ba don Allah da haka-da-haka ba, kada a sanya haka-da-haka a ciki, to ya nanata cewa duk wannan karamar shirka ce, kuma idan wanda ya ce ya yi imani cewa mutumin ko agwagwar ko kare ne mai tasiri a kansa maimakon Allah to Babban lalata.

Madogara

الملخص في شرح كتاب التوحيد، صالح بن فوزان بن عبد الله الفوزان، دار العاصمة، الرياض، الطبعة: الأولى، 1422هـ - 2001م. تفسير القرآن العظيم، عبد الرحمن بن محمد بن إدريس ابن أبي حاتم، تحقيق: أسعد محمد الطيب، نشر: مكتبة نزار مصطفى الباز، المملكة العربية السعودية، الطبعة: الثالثة، 1419هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya Allah kada Ka maida kabarina gunki

عن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم: «اللهُمَّ لَا تَجْعَلْ قَبْرِي وَثَنًا، لَعَنَ اللهُ قَوْمًا اتَّخَذُوا قُبُورَ أَنْبِيَائِهِمْ مَسَاجِدَ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya Allah kada Ka maida kabarina gunki, Allah Ya la'anci mutanen da suka maida kaburburan Annabawansu masallatai".
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya roki Ubangijinsa da kada Ya maida kabarinsa tamkar gunkin da mutane suke bauta masa ta hanyar girmama shi, da fuskantarsa a cikin sujjada, sannan tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya sanar da cewa Allah Ya nisantar Ya kore wanda ya maida kaburburan Annabawa masallatai daga rahamarsa' domin maida su masallatai sila ce zuwa bauta musu da kuma kudircewa a cikinsu.

Fa’idoji
  1. Ketare iyaka ta shari'a a cikin kaburburan Annabawa da salihan bayi ya maida su ana bauta musu koma bayan Allah, to kiyayewa daga hanyoyin shirka ya wajaba.
  2. Nufin kaburbura dan girmama su ba ya halatta da kuma yin ibada a gurin su duk yadda kusancin masu su yake ga Allah - Madaukakin sarki -.
  3. Haramcin gina masallatai akan kaburbura.
  4. Haramcin sallah a wurin da kaburbura suke koda bai yi gini ba saidai sallar jana'izar da ba'a yi wa gawar sallah ba kadai.
Madogara

مسند أحمد (12/ 314) (7358). فتح المجيد شرح كتاب التوحيد، لعبد الرحمن التميمي (1/ 434). القول المفيد على كتاب التوحيد، لمحمد بن عثيمين (1/ 434). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص178). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص194). التمهيد لشرح كتاب التوحيد، لصالح آل الشيخ (ص51). مشكاة المصابيح، للتبريزي (1/ 234).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko ya yi shirka

عن ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما أنه سَمِعَ رَجُلًا يَقُولُ: لَا وَالْكَعْبَةِ، فَقَالَ ابْنُ عُمَرَ: لَا يُحْلَفُ بِغَيْرِ اللَّهِ، فَإِنِّي سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «مَنْ حَلَفَ بِغَيْرِ اللهِ فَقَدْ كَفَرَ أَوْ أَشْرَكَ».
Daga Abdullahi Dan Umar - Allah Ya yarda da su - cewa shi ya ji wani mutum yana cewa: A'a na rantse da Ka'abah, sai Dan Umar ya ce: Ba'a rantsuwa da wanin Allah, domin cewa ni na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko ya yi shirka".
Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da AhmadDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labarin cewa wanda ya yi rantsuwa da wanin Allah da sunayensa da siffofinsa to hakika ya kafircewa Allah ko ya yi shirka; domin rantsuwa tana hukunta girmama wanda aka rantse da shi, girma kadai ya tabbata ga Allah ne Shi kadai; ba'a rantsuwa sai da Allah da sunayensa da siffofinsa - tsarki ya tabbatar masa, Wannan rantsuwar tana daga karamar shirka; saidai da a ce mai rantsuwa ya girmama abinda ya rantse da shi kamar girmama Allah - Madaukakin sarki - ko sama da haka; to a wannan lokacin zai zama daga babbar shirka.

Fa’idoji
  1. Lallai cewa girmamawa da yin rantsuwa hakki ne na Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka - ba'a rantsuwa sai da Allah da sunayenSa da siffofinSa.
  2. Kwadayin sahabbai akan horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ki, musamman ma idan abin kin ya kasance daga abinda yake rataya ne da shirka ko kafirci.
Madogara

سنن الترمذي (3/ 194) (1535). سنن أبي داود (5/ 154- 155) (3251). مسند أحمد (9/ 249) (5346)، (9/ 275) (5375)، (10/ 249) (6072). فتح المجيد شرح كتاب التوحيد، لعبد الرحمن التميمي (ص413). القول المفيد على كتاب التوحيد، لابن عثيمين (2/ 214). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص326). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص365). التمهيد لشرح كتاب التوحيد، لصالح آل الشيخ (ص452). فتاوى اللجنة الدائمة، (1/ 343).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai cewa mafi tsoron abinda nake jiye muku tsoro karamar shirka" suka ce : Mece ce karamar shirka ya Manzon Allah? ya ce: "Riya

عَنْ مَحْمُودِ بْنِ لَبِيدٍ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «إِنَّ أَخْوَفَ مَا أَخَافُ عَلَيْكُمُ الشِّرْكُ الْأَصْغَرُ» قَالُوا: وَمَا الشِّرْكُ الْأَصْغَرُ يَا رَسُولَ اللهِ؟ قَالَ: «الرِّيَاءُ، يَقُولُ اللهُ عز وجل لَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ إِذَا جُزِيَ النَّاسُ بِأَعْمَالِهِمْ: اذْهَبُوا إِلَى الَّذِينَ كُنْتُمْ تُرَاؤُونَ فِي الدُّنْيَا، فَانْظُرُوا هَلْ تَجِدُونَ عِنْدَهُمْ جَزَاءً؟».
Daga Mahmud Dan Labid - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa mafi tsoron abinda nake jiye muku tsoro karamar shirka" suka ce : Mece ce karamar shirka ya Manzon Allah? ya ce: "Riya, Allah - Mai girma da daukaka - Zai ce da su a ranar Alkiyama idan za’a yi wa mutane sakayyar ayyukansu: Ku tafi zuwa ga wadanda kuka kasance kuna nuna musu ayyukanku a duniya, sai ku duba shin zaku samu wani sakamako a wurin su?".
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa mafi yawan abinda yake jin tsoronsa ga al'ummarsa: Karamar shirka ita ce: Riya; Ita ce ya yi aiki saboda mutane. Sannan ya bada labari game da ukubar masu riya a ranar Alkiyama za’a ce da su: Ku tafi zuwa ga wadanda kuka kasance kuna aiki saboda su, ku duba shin suna mallakar saka muku da baku lada akan wannan aikin?!

Fa’idoji
  1. Wajabcin tsarkake aiki saboda Allah - Mai girma da daukaka - da gargadarwa daga riya.
  2. Tsananin tausayinsa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa, da kwadayinsa akan shiriyarsu da kuma nasiharsa garesu.
  3. Idan wannan ya zama shi ne tsoronsa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi alhali shi yana yiwa sahabbansa magana kuma su ne shugabannin salihai to tsoro akan wanda ke bayansu ya fi tsanani.
Madogara

مسند أحمد (39/ 39) (23630). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص57). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص45).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Canfi shirka ne, canfi shirka ne, canfi shirka ne, - sau uku -", babu wani a cikinmu saidai, saidai cewa Allah - Mai girma da daukaka - Yana tafiyar da shi da dogara (ga Allah)

عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسعودٍ رضي الله عنه عن رَسولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم قال: «الطِّيَرَةُ شِرْكٌ، الطِّيَرَةُ شِرْكٌ، الطِّيَرَةُ شِرْكٌ، -ثلاثًا-»، وَمَا مِنَّا إِلَّا، وَلَكِنَّ اللهَ عَزَّ وَجَلَّ يُذْهِبُهُ بِالتَّوَكُّلِ.
Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya ce: "Canfi shirka ne, canfi shirka ne, canfi shirka ne, - sau uku -", babu wani a cikinmu saidai, saidai cewa Allah - Mai girma da daukaka - Yana tafiyar da shi da dogara (ga Allah).
Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargadi daga canfi shi ne canfi daga kowanne abu, abin ji ne ko abin gani, daga tsuntsayene ko dabbobi ko masu larurori ko lambobi ko kwanuka ko makamancin hakan, kadai ya ambaci canfi ne domin cewa shi ne ya fi shahara a lokacin Jahiliyya, asalinsa shi ne sakin tsuntsu a lokacin fara wani aiki na tafiya ne ko kasuwanci ko makamancin hakan, idan ya tashi a bangaren dama sai ya yi yunkuri ya ci gaba da abinda yake nufi, idan ya tashi bangaren hagu sai ya canfa ya kame daga abinda yake nufi. Ya bada labarin cewa hakan shirka ce, kadai canfi ya zama shirka; domin ba mai zuwa da alheri sai Allah, kuma ba mai tunkude sharri sai Allah Shi kadai ba shi da abokin tarayya. Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ambaci cewa wani abu na canfi zai iya darsuwa a zuciyar musulmi, saidai ya wajaba akansa ya tunkude shi da dogaro ga Allah, tare da aikata sabubba.

Fa’idoji
  1. Canfi shirka ne; domin acikinsa akwai rataya zuciya da wanin Allah.
  2. Muhimmancin maimaita mas'aloli muhimmai, dan a kiyaye su kuma su tabbata a cikin zukata.
  3. Dogaro ga Allah - Madaukain sarki - yana tafiyar da canfi.
  4. Umarni da dogaro ga Allah Shi kadai, da rataya zuciya da Shi - tsarki ya tabbatar maSa -.
Madogara

سنن أبي داود (6/ 54) (3915). سنن ابن ماجه (4/ 560) (3538). سنن الترمذي (3/ 258) (1614). مسند أحمد (6/ 213) (3687). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص259). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص233).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Shin ba haramta abin da Allah ya halatta suke ba sai kuma ku haramta shi? kuma su halarta abin da Allah ya haramta kuma ku halarta shi ba? sai na ce:e. sai ya ce wannan shi ne ibadarsu.

عن عدي بن حاتم رضي الله عنه : "أنه سمع النبي صلى الله عليه وسلم يقرأ هذه الآية: "اتَّخَذُوا أَحْبَارَهُمْ وَرُهْبَانَهُمْ أَرْبَابًا مِنْ دُونِ اللَّهِ وَالْمَسِيحَ ابْنَ مَرْيَمَ وَمَا أُمِرُوا إِلاَّ لِيَعْبُدُوا إِلَهًا وَاحِدًا لا إِلَهَ إِلاَّ هُوَ سُبْحَانَهُ عَمَّا يُشْرِكُونَ" فقلت له: إنا لسنا نعبدهم، قال: أليس يُحَرِّمُونَ ما أحل الله فتُحَرِّمُونَهُ؟ ويُحِلُّونَ ما حَرَّمَ الله فتُحِلُّونَهُ؟ فقلت: بلى، قال: فتلك عبادتهم".
An samo daga Adi Dan Hatim -Allah ya yarda dashi- "cewa ya ji Annabi -tsira da amincin Allah yana karanta wannan ayar: Sun riki malamansu "yahudawa" da malamansu "nasarawa" abin yiwa bauta ba Allah ba haka nan Isa Dan Maryam. kuma ba'a umarce su ba sai da cewa su bautawa abin bauta shi kadai wanda ba abin bautawa da cancanta sai shi tsarki ya tabbatar masa game da abin da suke yi masa tarayya? sai na ce da shi: lallai mu ba bauta musu muke yi ba. sai ya ce: shin ba haramta abin da Allah ya halatta suke ba sai ku ma ku haramta shi? kuma su halarta abin da Allah ya haramta ku ma ku halarta shi ba? sai nace: ey.Sai yace wannan ita ce bauta musu din."
Al-Tirmithi Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

yayin da wannan Sahabin mai girma yaji karatun Manzon Allah-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-na wannan ayar wacce ta kunshi labarin yahudu da nasara:cewa sun mayar da malamansu da masu ibadar cikinsu abin bauta,suna shar'anta musu abinda yasabawa shari'ar Allah kuma suyi musu biyayya a kan haka,to sai ma'anar ayar ta rikitar,domin shi sahabin ya zaci cewa bauta ta takaita akan yin sujjada da makamantanta,sai Manzo -tsira da amincin Allah-ya bayyana masa cewa yana daga bautawa malamai yi musu biyayya a wajan haramta halal da kuma halarta haram,sabanin hukunci Allah madaukaki da Manzonsa tsira da aminci su tabbata a gare shi

Madogara

كتاب التوحيد، للإمام محمد بن عبد الوهاب، ت: د. دغش العجمي. مكتبة أهل الأثر, الطبعة الخامسة, 1435ه. الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد بن عبد العزيز السليمان القرعاوي, ت: محمد بن أحمد سيد, مكتبة السوادي، الطبعة: الخامسة، 1424ه. الملخص في شرح كتاب التوحيد، للشيخ صالح الفوزان, دار العاصمة, الطبعة الأولى، 1422ه. سلسلة الأحاديث الصحيحة، للألباني, مكتبة المعارف, الطبعة الأولى, 1415ه. جامع الترمذي, ت: أحمد شاكر, مكتبة ومطبعة مصطفى البابي, الطبعة: الثانية، 1395ه.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

cewa an tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - game da ambulaf? Ya ce: Aikin Iblis ne.

عن جابر رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم سئل عن النُّشْرَةِ؟ فقال: هي من عمل الشيطان.
Daga Jaber, yardar Allah ta tabbata a gare shi, cewa an tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - game da ambulaf? Ya ce: Aikin Iblis ne.
Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Cewa an tambayi Annabi –SAW- ya yi salati da amincin Allah su tabbata a gare shi- game da mu'amala da matsafa bisa tsarin da zamanin jahiliyya ya yi amfani da shi, kamar su: maganin sihiri ta hanyar maita, menene hukuncin hakan. Saboda tana da nau'ikan sihiri da kuma amfani da aljan, shirka ne kuma haramun ne. Amma littafin da ya halatta: shi ne yin sihiri ta hanyar ruqiya ko ta hanyar neman sa, da kuma bayyana shi da hannu yayin karatun Alkur'ani ko kuma tare da halattattun magunguna.

Madogara

1- الملخص في شرح كتاب التوحيد، صالح بن فوزان بن عبد الله الفوزان، دار العاصمة، الرياض، الطبعة: الأولى، 1422هـ - 2001م. 2- الجديد في شرح كتاب التوحيد، محمد بن عبد العزيز السليمان القرعاوي، تحقيق: محمد بن أحمد سيد، مكتبة السوادي، الطبعة: الخامسة، 1424هـ - 2003م. 3- سنن أبي داود، سليمان بن الأشعث أبوداود، تحقيق: محمد محيي الدين عبد الحميد، المكتبة العصرية، صيدا، بيروت. 4- مسند الإمام أحمد بن حنبل، أحمد بن حنبل أبو عبدالله الشيباني، تحقيق: شعيب الأرنؤوط و عادل مرشد، وآخرون، تحت إشراف: عبد الله بن عبد المحسن التركي، مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى، 1421هـ - 2001م. 5- سلسلة الأحاديث الصحيحة وشيء من فقهها وفوائدها، محمد ناصر الدين الألباني، مكتبة المعارف للنشر والتوزيع، الرياض.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Wanda camfi ya mayar da shi ga barin bukatarsa; to hakika ya yi shirka suka ce menene kaffarar hakan? ya ce: Ka ce ya Allah! babu wani alheri sai alhairinka, kuma babu camfi sai dai abin da ka nufa, kuma babu abin bauta da cancanta in ba kai ba

عن عبد الله بن عمرو بن العاص - رضي الله عنه- مرفوعاً: "مَن ردته الطِّيَرَة عن حاجته فقد أشرك، قالوا: فما كفارة ذلك؟ قال: أن تقول: اللهم لا خير إلا خيرك، ولا طَيْرَ إِلَّا طَيْرُكَ ولا إله غيرك".
Wanda camfi ya mayar da shi ga barin bukatarsa; to hakika ya yi shirka suka ce menene kaffarar hakan? ya ce: Ka ce ya Allah! babu wani alheri sai alhairinka, kuma babu camfi sai dai abin da ka nufa, kuma babu abin bauta da cancanta in ba kai ba
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya gaya mana a cikin wannan hadisin cewa duk wanda mummunan fata ya hana shi ci gaba da abin da ya yi niyya, to, ya zo da irin shirka, kuma lokacin da Sahabbai suka tambaye shi game da kaffarar wannan babban zunubi, sai ya shiryar da su zuwa ga wadannan maganganun masu karimci a cikin hadisin da suka hada da wakiltar lamarin zuwa ga Allah Madaukakin Sarki. Ya hana ikon kowa.

Madogara

1- فتح المجيد شرح كتاب التوحيد، مطبعة السنة المحمدية، القاهرة، مصر، الطبعة: السابعة، 1377هـ - 1957م. 2- القول المفيد على كتاب التوحيد، دار ابن الجوزي، المملكة العربية السعودية، الطبعة: الثانية, محرم، 1424ه. 3- الملخص في شرح كتاب التوحيد، دار العاصمة الرياض، الطبعة: الأولى 1422هـ - 2001م. 4- الجديد في شرح كتاب التوحيد، مكتبة السوادي، جدة، المملكة العربية السعودية، الطبعة: الخامسة، 1424هـ - 2003م. 5- التمهيد لشرح كتاب التوحيد، دار التوحيد، تاريخ النشر: 1424هـ. 6- مسند الإمام أحمد بن حنبل، المحقق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون، إشراف: د عبد الله بن عبد المحسن التركي، الناشر: مؤسسة الرسالة-الطبعة: الأولى، 1421هـ - 2001م. 7- السلسلة الصحيحة، مكتبة المعارف للنشر والتوزيع، الرياض، الطبعة: الأولى.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 11
Hadisai 11
  1. Allah madaukaki yana cewa: {Don haka kada ku sanya wa Allah kima, duk da cewa kun sani.} Ibn Abbas ya fada a cikin ayar cewa: "Aboki: shirka ne, wanda aka boye daga tururuwa da ke dauke da bakar leda a cikin duhun dare.
  2. Ya Allah kada Ka maida kabarina gunki
  3. Wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko ya yi shirka
  4. Lallai cewa mafi tsoron abinda nake jiye muku tsoro karamar shirka" suka ce : Mece ce karamar shirka ya Manzon Allah? ya ce: "Riya
  5. Canfi shirka ne, canfi shirka ne, canfi shirka ne, - sau uku -", babu wani a cikinmu saidai, saidai cewa Allah - Mai girma da daukaka - Yana tafiyar da shi da dogara (ga Allah)
  6. Shin ba haramta abin da Allah ya halatta suke ba sai kuma ku haramta shi? kuma su halarta abin da Allah ya haramta kuma ku halarta shi ba? sai na ce:e. sai ya ce wannan shi ne ibadarsu.
  7. cewa an tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - game da ambulaf? Ya ce: Aikin Iblis ne.
  8. Wanda camfi ya mayar da shi ga barin bukatarsa; to hakika ya yi shirka suka ce menene kaffarar hakan? ya ce: Ka ce ya Allah! babu wani alheri sai alhairinka, kuma babu camfi sai dai abin da ka nufa, kuma babu abin bauta da cancanta in ba kai ba
  9. Wanda ya gamu da Allah ba ya tarayya da shi da wani to zai shiga Aljanna, wanda kuma ya gamu da shi yana shirka da shi to zai shiga wuta
  10. Daga Dan Abbass cikin fadin Allah inda yake cewa: kuma suka ce kada ku kuskura ku bar Allolinku kuma kada ku bar Waddan da Suwa'an da kuma Yagusa da ya'uka da kuma Nasra, sai ya ce wadan nan sunayen na wasu Mutanen kikrki ne daga cikin Mutanen Annabi Nuh, yayai da suka Mutu sai shaidan yayi musu wahayi ga Mutanensu kan su kafa a wurarensu da suke zama gumaka, kuma su sa musu sunansu sai kuwa suka yi, kuma ba'a bauta musu ba sai bayan wadan nan sun Mutu kuma an manta da Ilimin sai aka rika bauta musu"
  11. Wanda ya rantse da amana to baya daga cikinmu

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com