Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda ya gamu da Allah ba ya tarayya da shi da wani to zai shiga Aljanna, wanda kuma ya gamu da shi yana shirka da shi to zai shiga wuta

عن جابر بن عبد الله رضي الله عنهما قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «مَنْ لَقِيَ اللهَ لَا يُشْرِكُ بِهِ شَيْئًا دَخَلَ الْجَنَّةَ، وَمَنْ لَقِيَهُ يُشْرِكُ بِهِ دَخَلَ النَّارَ».
Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya gamu da Allah ba ya tarayya da shi da wani to zai shiga Aljanna, wanda kuma ya gamu da shi yana shirka da shi to zai shiga wuta".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsiara da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana sanar da cewa wanda ya mutu ba ya hada Allah da kowa to makaomarsa ita ce Aljanna , koda an azabtar da shi akan sashin zunubansa, kuma cewa wanda ya mutu alhali shi yana tarayya da Allah to zai dawwama a wuta.

Fa’idoji
  1. Falalar Tauhidi, kuma cewa shi sababi ne na tsira daga dawwama a wuta.
  2. Kusancin Aljanna da wuta ga bawa, kuma cewa shi babu wani abu a tsakaninsa da su sai mutuwa.
  3. Gargadi daga shirka, kadan dinta da mai yawanta; domin cewa tsira daga wuta ta hanyar nisantar ta ne.
  4. Izina a ayyuka da karshen su ne.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 94) (93). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص49). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص60).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SHIRKA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com