Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda camfi ya mayar da shi ga barin bukatarsa; to hakika ya yi shirka suka ce menene kaffarar hakan? ya ce: Ka ce ya Allah! babu wani alheri sai alhairinka, kuma babu camfi sai dai abin da ka nufa, kuma babu abin bauta da cancanta in ba kai ba

عن عبد الله بن عمرو بن العاص - رضي الله عنه- مرفوعاً: "مَن ردته الطِّيَرَة عن حاجته فقد أشرك، قالوا: فما كفارة ذلك؟ قال: أن تقول: اللهم لا خير إلا خيرك، ولا طَيْرَ إِلَّا طَيْرُكَ ولا إله غيرك".
Wanda camfi ya mayar da shi ga barin bukatarsa; to hakika ya yi shirka suka ce menene kaffarar hakan? ya ce: Ka ce ya Allah! babu wani alheri sai alhairinka, kuma babu camfi sai dai abin da ka nufa, kuma babu abin bauta da cancanta in ba kai ba
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya gaya mana a cikin wannan hadisin cewa duk wanda mummunan fata ya hana shi ci gaba da abin da ya yi niyya, to, ya zo da irin shirka, kuma lokacin da Sahabbai suka tambaye shi game da kaffarar wannan babban zunubi, sai ya shiryar da su zuwa ga wadannan maganganun masu karimci a cikin hadisin da suka hada da wakiltar lamarin zuwa ga Allah Madaukakin Sarki. Ya hana ikon kowa.

Madogara

1- فتح المجيد شرح كتاب التوحيد، مطبعة السنة المحمدية، القاهرة، مصر، الطبعة: السابعة، 1377هـ - 1957م. 2- القول المفيد على كتاب التوحيد، دار ابن الجوزي، المملكة العربية السعودية، الطبعة: الثانية, محرم، 1424ه. 3- الملخص في شرح كتاب التوحيد، دار العاصمة الرياض، الطبعة: الأولى 1422هـ - 2001م. 4- الجديد في شرح كتاب التوحيد، مكتبة السوادي، جدة، المملكة العربية السعودية، الطبعة: الخامسة، 1424هـ - 2003م. 5- التمهيد لشرح كتاب التوحيد، دار التوحيد، تاريخ النشر: 1424هـ. 6- مسند الإمام أحمد بن حنبل، المحقق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون، إشراف: د عبد الله بن عبد المحسن التركي، الناشر: مؤسسة الرسالة-الطبعة: الأولى، 1421هـ - 2001م. 7- السلسلة الصحيحة، مكتبة المعارف للنشر والتوزيع، الرياض، الطبعة: الأولى.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SHIRKA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com