Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labarin cewa wanda ya yi rantsuwa da wanin Allah da sunayensa da siffofinsa to hakika ya kafircewa Allah ko ya yi shirka; domin rantsuwa tana hukunta girmama wanda aka rantse da shi, girma kadai ya tabbata ga Allah ne Shi kadai; ba'a rantsuwa sai da Allah da sunayensa da siffofinsa - tsarki ya tabbatar masa, Wannan rantsuwar tana daga karamar shirka; saidai da a ce mai rantsuwa ya girmama abinda ya rantse da shi kamar girmama Allah - Madaukakin sarki - ko sama da haka; to a wannan lokacin zai zama daga babbar shirka.
- Lallai cewa girmamawa da yin rantsuwa hakki ne na Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka - ba'a rantsuwa sai da Allah da sunayenSa da siffofinSa.
- Kwadayin sahabbai akan horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ki, musamman ma idan abin kin ya kasance daga abinda yake rataya ne da shirka ko kafirci.
سنن الترمذي (3/ 194) (1535). سنن أبي داود (5/ 154- 155) (3251). مسند أحمد (9/ 249) (5346)، (9/ 275) (5375)، (10/ 249) (6072). فتح المجيد شرح كتاب التوحيد، لعبد الرحمن التميمي (ص413). القول المفيد على كتاب التوحيد، لابن عثيمين (2/ 214). الملخص في شرح كتاب التوحيد، لصالح الفوزان (ص326). الجديد في شرح كتاب التوحيد، لمحمد القرعاوي (ص365). التمهيد لشرح كتاب التوحيد، لصالح آل الشيخ (ص452). فتاوى اللجنة الدائمة، (1/ 343).