Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda ya rantse da amana to baya daga cikinmu

عَنْ بُرَيْدَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ حَلَفَ بِالْأَمَانَةِ فَلَيْسَ مِنَّا».
Daga Buraidah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: "Wanda ya rantse da amana to baya daga cikinmu".
Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma AhmadDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani kuma ya gargaɗar daga rantsuwa da amana, kuma cewa wanda ya aikata hakan to ba shi daga cikinmu.

Fa’idoji
  1. Haramcin rantsuwa da wanin Allah - Maɗaukakin sarki -, kuma daga cikin hakan: amana, kuma hakan yana daga ƙaramar shirka.
  2. Amana ta ƙunshi ɗa'a da bauta da ajiya da bayarwa hannu da hannu da amintarwa.
  3. Rantsuwa bata ƙulluwa sai da Allah - Maɗaukakin sarki - ko da wani suna daga sunayenSa ko wata siffa daga siffofinSa.
  4. AlKhaɗɗabi ya ce: Wannan yana kama da karhancin ya zama saboda cewa shi ya yi umarni a yi rantsuwa da Allah ne da kuma siffofinSa, amana kuwa ba ta daga siffofinSa, kawai ita wani al'amari ce daga aumarninSa, kuma farilla ce daga farillanSa, sai aka hanasu su rantse da ita dan abinda ke cikin hakan na daidaitawa tsakaninta da tsakanin sunayen Allah - Mai girma da ɗaukaka - da kuma siffofinSa.
Madogara

سنن أبي داود (5/ 155) (3253). مسند أحمد (38/ 82) (22980). نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (2/ 1166). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (3/ 201). مشكاة المصابيح، للتبريزي (2/ 1020). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (6/ 452). معالم السنن، للخطابي (4/ 46). سبل السلام، الصنعاني (2/ 550 ).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SHIRKA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com