Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda ya je wurin Ɗan duba (malamin duba) ya tambaye shi wani abu, to, ba za a karɓi Sallarsa ta darare arba’in ba

عن بعض أزواج النبي صلى الله عليه وسلم عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ أَتَى عَرَّافًا فَسَأَلَهُ عَنْ شَيْءٍ لَمْ تُقْبَلْ لَهُ صَلَاةٌ أَرْبَعِينَ لَيْلَةً».
Daga wasu cikin matan Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: Wanda ya je wurin Ɗan duba (malamin duba) ya tambaye shi wani abu, to, ba za a karɓi Sallarsa ta darare arba’in ba.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana tsoratarwa a kan zuwa wurin mai duba -suna ne fitacce na boka, da mai taurari, mai zane a kasa da makamantansu, irin wanda yake kafa dalilin sanin gaibu ta hanyar wasu abubuwa na farko-farkon lamari- zallar tambayarsa a kan wani abu na gaibu, zai haramta masa ladan sallah na kwanaki arba’in, wannan uƙuba ce, a kan wannan laifi, kuma zunubi ne mai girma.

Fa’idoji
  1. Haramcin bokanci, da zuwa wurin boka da kuma tambayarsu gaibu.
  2. Tabbas ana hanawa mutum ladan biyayya don ya zama uƙuba a gare shi a kan aikata laifi.
  3. Yana shiga cikin wannan Hadisin abin ake cewa burji da duba shi, da karanta tafin hannu, da ƙwarya, ko da kuwa leƙawa ne kaɗai, domin duka yana cikin bokanci, kuma yana cikin iƙirarin sanin gaibu.
  4. Idan wannan ya zama sakamakon wanda ya je wurin mai duba, to, ya ya halin shi mai duban.??
  5. Sallar kwanaki arba’in idan ya yi ba ta yi ba, kuma ba zai rama ta ba, saidai babu ladanta.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 1751) (2230). مسند أحمد (27/ 197) (16638). الجديد في شرح كتاب التوحيد، للقرعاوي (ص238). الملخص في شرح كتاب التوحيد، للفوزان (ص213).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SUNAYE DA HUKUNCE-HUKUNCE

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com