Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Yankin Imani

Hadisai 7

Ku yi gaggawa da ayyuka (na alheri), wasu fitinu kamar yankin dare ne mai duhu,

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «بَادِرُوا بِالْأَعْمَالِ فِتَنًا كَقِطَعِ اللَّيْلِ الْمُظْلِمِ، يُصْبِحُ الرَّجُلُ مُؤْمِنًا وَيُمْسِي كَافِرًا، أَوْ يُمْسِي مُؤْمِنًا وَيُصْبِحُ كَافِرًا، يَبِيعُ دِينَهُ بِعَرَضٍ مِنَ الدُّنْيَا».
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Ku yi gaggawa da ayyuka (na alheri), wasu fitinu kamar yankin dare ne mai duhu, mutum zai wayi gari yana mumini ya kai yammaci yana kafiri, ko ya yammanta yana mumini ya wayi gari yana kafiri, zai sayar da addininsa da wata haja ta duniya".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da mumini akan gaggawa da yawaita ayyuka na gari kafin wuyatarsu da shagaltuwa daga gare su da zuwan fitinu da shubuhohin da zasu hana aikata su, kuma zasu toshe su, masu duhu ne kamar yankin dare, yana cakuɗe gaskiya da ƙarya a cikinsu, sai banbancewa tsakaninsu ta yi wuya a wurin mutane, saboda tsananinsu mutum zai dinga kaikawo har cewa shi zai wayi gari yana mumini ya yanmanta yana kafiri, kuma ya yanmanta yana mumini ya wayi gari yana kafiri, zai bar addininsa da wani ɗan jin daɗi na duniya mai gushewa.

Fa’idoji
  1. Wajabcin riƙo da addini, da gaggawa a aiki na gari kafin abubuwan da zasu hana su hana.
  2. Nuni zuwa bibiyar fitinu masu ɓatarwa a ƙarshen zamani, kuma cewa duk lokacin da wata fitina ta tafi sai wata fitinar daban ta biyo bayanta.
  3. Idan addinin mutum ya yi rauni kuma ya sauka daga gare shi, saboda al'amuran duniya na dukiya ko waninta, to hakan zai zama sababi a karkacewarsa da barinsa ga addini da binsa tare da fitintinu.
  4. A cikin Hadisin akwai dalili akan cewa ayyuka na gari sababi ne na tsira daga fitintinu.
  5. Fitintinu sun rabu biyu: Fitintinu na shubuhohi, to kuma maganin su shi ne ilimi, da fitintinu na Sha’awa, to kuma maganin su shi ne imani da haƙuri.
  6. A cikin Hadisin akwai nuni zuwa cewa wanda aikinsa ya ƙaranta to fitina zata fi gaggawa zuwa gare shi, kuma wanda aikinsa ya yi yawa to yana kamata kada ya ruɗu da abinda ke tare da shi, kawai ya nemi ƙari.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 110) (118). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 169). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 16). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 122).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Imani kashi sba;in da Tara ne ko kuma kashi Sittin da Tara, mafificinsu shi ne faxin babu wani abun bauta da gaskiya sai Allah, Mafi qanqanta kuma shi ne gusar da cuta ga barin Hanya, kuma kunya wani yanki ne daga cikin Imani

عن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: «الإيمانُ بِضْعٌ وَسَبْعُونَ أو بِضْعٌ وسِتُّونَ شُعْبَةً: فَأَفْضَلُهَا قَوْلُ: لا إله إلا الله، وَأَدْنَاهَا إِمَاطَةُ الأَذَى عَنِ الطَّرِيقِ، وَالحَيَاءُ شُعْبَةٌ مِنَ الإِيمَانِ».
Daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi zuwa ga Manzon Allah: "Imani kashi sba;in da Tara ne ko kuma kashi Sittin da Tara, mafificinsu shi ne faxin babu wani abun bauta da gaskiya sai Allah, Mafi qanqanta kuma shi ne gusar da cuta ga barin Hanya, kuma kunya wani yanki ne daga cikin Imani"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

- صحيح البخاري، للإمام أبي عبد الله محمد بن إسماعيل البخاري، عناية محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة، الطبعة الأولى، 1422هـ. - صحيح مسلم، للإمام مسلم بن الحجاج، حققه ورقمه محمد فؤاد عبد الباقي، دار عالم الكتب، الرياض، الطبعة الأولى، 1417هـ. - شرح رياض الصالحين، للشيخ محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ. - نزهة المتقين بشرح رياض الصالحين، تأليف مصطفى سعيد الخن، مصطفى البغا، محي الدين مستو، علي الشربجي، محمد أمين لطفي، مؤسسة الرسالة، بيروت، لبنان، الطبعة الرابعة عشر، 1407ه. - بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم بن عيد الهلالي، دار ابن الجوزي، الطبعة الأولى، 1418ه. - دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، المؤلف: محمد علي بن محمد بن علان الصديقي، اعتنى بها: خليل مأمون شيحا، دار المعرفة للطباعة والنشر والتوزيع، بيروت، لبنان، الطبعة: الرابعة، 1425هـ - 2004م. - تطريز رياض الصالحين، تأليف فيصل آل مبارك، تحقيق د. عبد العزيز آل حمد، دار العاصمة، الرياض، الطبعة الأولى، 1423هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi cewa shi ya fada a sha'anin mutane Madina: "Ba mai sonsu sai mumini, kuma babu mai kinsu sai munafiki, wanda ya so su Allah zai so shi, wanda ya ki su Allah Zai ki shi

عَنِ الْبَرَاءِ رضي الله عنه: عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ قَالَ فِي الْأَنْصَارِ: «لَا يُحِبُّهُمْ إِلَّا مُؤْمِنٌ، وَلَا يُبْغِضُهُمْ إِلَّا مُنَافِقٌ، مَنْ أَحَبَّهُمْ أَحَبَّهُ اللهُ وَمَنْ أَبْغَضَهُمْ أَبْغَضَهُ اللهُ».
Daga Al-Barra - Allah Ya yarda da shi -: Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi cewa shi ya fada a sha'anin mutane Madina: "Ba mai sonsu sai mumini, kuma babu mai kinsu sai munafiki, wanda ya so su Allah zai so shi, wanda ya ki su Allah Zai ki shi".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa son mutanen Ansar daga mutanen Madina, alama ce akan cikar imani; wannan dan rigayarsu a taimakon Musulunci da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da kokari akan tarbar musulmai, da bada dukiyoyinsu da rayukansu a tafarkin Allah, kuma cewa kinsu alama ce ta munafunci. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana cewa wanda ya so mutanen Madina Allah Zai so shi, wanda ya ki su Allah Zai ki shi.

Fa’idoji
  1. A cikinsa akwai daraja mai girma ga mutanen Madina, son su alamce akan imani da kubuta daga munafunci.
  2. Son masoya Allah da taimakonsu sababine na samun son Allah ga bawa.
  3. Falalar wadanda suka rigaya na farko a cikin Musulunci.
Madogara

صحيح البخاري (5/ 32) (3783). صحيح مسلم (1/ 85) (75). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 447). تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص257). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (6/ 258). شرح النووي على مسلم (2/ 63). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين (1/ 350).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kana ganin idan na sallaci salloli wadanda aka wajabta, na azimci watan Ramdan, na halatta halal, na haramta haram

عن جابر رضي الله عنه: أَنَّ رَجُلًا سَأَلَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: أَرَأَيْتَ إِذَا صَلَّيْتُ الصَّلَوَاتِ الْمَكْتُوبَاتِ، وَصُمْتُ رَمَضَانَ، وَأَحْلَلْتُ الْحَلَالَ، وَحَرَّمْتُ الْحَرَامَ، وَلَمْ أَزِدْ عَلَى ذَلِكَ شَيْئًا، أَأَدْخُلُ الْجَنَّةَ؟ قَالَ: «نَعَمْ»، قَالَ: وَاللهِ لَا أَزِيدُ عَلَى ذَلِكَ شَيْئًا.
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi -: Lallai wani mutum ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Kana ganin idan na sallaci salloli wadanda aka wajabta, na azimci watan Ramdan, na halatta halal, na haramta haram, ban kara komai akan hakan ba, zan shiga Aljanna? Ya ce : "Eh", ya ce: Na rantse da Allah ba zan kara komai ba akan hakan ba.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya sallaci salloli biyar, wadanda suka wajabta bai kara komai akan su ba na nafilifili, kuma ya azimci watan Ramadan bai yi tadawwa’i ba, ya kudirce halatta halal ya kuma aikata shi, ya kudirce haramta haram ya kuma nisanci ta, to shi zai shiga Aljanna.

Fa’idoji
  1. Kwadayin musulmi akan aikata farillai da barin abubuwan da aka haramta, da kuma manufarsa ta zama shiga Aljanna.
  2. Muhimmancin aikata halal da kudirce halaccinsa, da kuma haramta haram da kudirce haramcin shi.
  3. Aikata wajibai da barin abubuwan da aka haramta, sababi ne na shiga Aljanna.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 44) (15). جامع العلوم والحكم (1/513). شرح الأربعين النووية للعثيمين (ص: 215). فتح القوي المتين في شرح الأربعين للعباد (ص 77).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) : Alhamdulillah, (wato): godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (fadin) Subhanallah, wato: tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da kasa

عن أبي مالكٍ الأشعريِّ رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «الطُّهُورُ شَطْرُ الْإِيمَانِ، وَالْحَمْدُ لِلهِ تَمْلَأُ الْمِيزَانَ، وَسُبْحَانَ اللهِ وَالْحَمْدُ لِلهِ تَمْلَآنِ -أَوْ تَمْلَأُ- مَا بَيْنَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ، وَالصَّلَاةُ نُورٌ، وَالصَّدَقَةُ بُرْهَانٌ، وَالصَّبْرُ ضِيَاءٌ، وَالْقُرْآنُ حُجَّةٌ لَكَ أَوْ عَلَيْكَ، كُلُّ النَّاسِ يَغْدُو، فَبَايِعٌ نَفْسَهُ فَمُعْتِقُهَا أَوْ مُوبِقُهَا».
Daga Abu Malik Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) : Alhamdulillah, (wato): godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (fadin) Subhanallah, wato: tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da kasa, sallah haske ce, sadaka garkuwa ce, hakuri haskene, Alkur’ani hujjane gareka ko akanka, dukkanin mutane suna wayar gari, akwai mai saida kansa sai ya 'yanto ta ko ya halakar da ita".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari: Cewa tsarki na zahiri yana kasancewa ne da alwala da wanka, kuma sharadi ne a sallah. Kuma cewa fadin: Alhamdulillah, (wato) "Godiya ta tabbata ga Allah yana cika ma'auni", shi ne godiya gare shi - tsarki ya tabbatar maSa - da kuma siffantaShi da siffofin cika, za'a auna su ranar alkiyama sai su cika ma'aunin ayyuka. Kuma fadin: Subhanallah, "Tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah", Shi ne tsarkake Shi daga kowacce tawaya da kuma siffantaShi da cikakken cika wanda yake dacewa da girmanSa, tare da sonSa da girmamaShi suna cika abinda ke tsakanin sammai da kasa. Kuma: "Sallah haske ce’’ ga bawa a cikin zuciyarsa, da fuskarsa, da cikin kabarinsa, da a tashinsa a taron Alkiyama. Kuma: "Sadaka garkuwace" kuma dalili ce akan gaskiyar imanin mumini, da kuma banbancinsa da munafikin da yake hanuwa daga yin ta (ita sadakar) dan kasancewarsa ba ya yin sadaka a lokacin ta. Kuma: "Hakuri haske ne" - Shi ne tsare rai daga firgici da fushi - wani haskene wanda yake da zafi da kuna, kamar hasken rana; domin shi mai wahalane, kuma yana bukatuwa ga dakewar zuciya da tsareta daga abinda take so; mai shi ba zai gushe ba yana mai haskaka , mai shiriya mai zarcewa akan daidai. Shi ne hakuri akan biyayya ga Allah, da kuma barin sabonSa, da kuma hakuri akan masifu da nau'o'in abubuwan ki a duniya. Kuma: 'Alkur’ani hujjane a gareka" ta hanyar Karanta shi da kuma aiki da shi, ko kuma "Hujjane akanka", ta hanyar barinsa ba tare da wani aiki ba, ko karantawa ba. Sannan - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa dukkanin mutane suna tafiya suna fita suna tashi daga barcinsu suna fita daga gidajensu dan ayyukansu mabanbanta, Daga cikinsu akwai mai tabbata akan biyayya ga Allah, sai ya 'yanto kansa daga wuta, daga cikinsu akwai wanda yake kaucewa daga hakan kuma yake afkawa a cikin sabo sai ya halakar da ita ta hanyar shigarta wuta.

Fa’idoji
  1. Tsaki iri biyu ne; Tsarki na zahiri, yana kasancewa ne da yin alwala da wanka, da kuma tsarkin badini yana kasancewa ne da kadaita Allah da imani da aiki na gari.
  2. Muhimmanicin kiyaye sallah, ita ce haske ga bawa a duniya da kuma ranar alkiyama.
  3. Sadaka dalili ce akan gaskiyar imani.
  4. Muhimmancin aiki da Alkur’ani da gasgata shi, dan ya zama hujja a gareka ba akanka ba.
  5. Rai idan ba ka shagaltar da ita da da'a ba, za ta shagaltar da kai da sabo.
  6. Kowanne mutum ba makawa sai ya yi aiki; kodai ya 'yanto ransa da biyayya (ga Allah) ko ya halakar da ita da sabo.
  7. Hakuri yana bukatar juriya da neman lada, kuma acikinsa akwai wahala.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 203) (223)، شرح الأربعين لابن دقيق العيد (ص 84)، شرح الأربعين النووية للعثيمين (ص: 231)، الرياض الزكية شرح الأربعين النووية للخضير (ص 293)، فتح القوي المتين في شرح الأربعين للعباد (ص 79)

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Shin kun san mai Ubangijinku Ya ce?" Suka ce: Allah da Manzonsane mafi sani, ya ce: "Mumini da kafiri sun wayi gari daga bayina

عَنْ زَيْدِ بْنِ خَالِدٍ الجُهَنِيِّ رضي الله عنه أَنَّهُ قَالَ: صَلَّى لَنَا رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ صَلَاةَ الصُّبْحِ بِالْحُدَيْبِيَةِ عَلَى إِثْرِ سَمَاءٍ كَانَتْ مِنَ اللَّيْلَةِ، فَلَمَّا انْصَرَفَ أَقْبَلَ عَلَى النَّاسِ، فَقَالَ: «هَلْ تَدْرُونَ مَاذَا قَالَ رَبُّكُمْ؟» قَالُوا: اللهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: «أَصْبَحَ مِنْ عِبَادِي مُؤْمِنٌ بِي وَكَافِرٌ، فَأَمَّا مَنْ قَالَ: مُطِرْنَا بِفَضْلِ اللهِ وَرَحْمَتِهِ، فَذَلِكَ مُؤْمِنٌ بِي وَكَافِرٌ بِالْكَوْكَبِ، وَأَمَّا مَنْ قَالَ: بِنَوْءِ كَذَا وَكَذَا، فَذَلِكَ كَافِرٌ بِي وَمُؤْمِنٌ بِالْكَوْكَبِ».
Daga Zaidu Dan Khalid AlJuhani - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallar Asuba a Hudaibiyya a bayan (ruwan daya sauka) a wannan daren da ya wuce, lokacin da ya sallame sai ya juya ya fuskanto mutane, ya ce: "Shin kun san mai Ubangijinku Ya ce?" Suka ce: Allah da Manzonsane mafi sani, ya ce: "Mumini da kafiri sun wayi gari daga bayina" Amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da falalar Ubangiji da rahamarSa, to wannan ya yi imani da Ni, kuma ya kafircewa taurari. Amma wanda ya ce: Da tauraro kaza da kaza, to wannan ya kafirce mi Ni kuma ya yi imani da taurari".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi sallar Asuba a Hudaibiyya - ita wata alkaryace kusa da Makka bayan wani ruwa da ya sauka a wannan daren, Lokacin da ya yi sallama ya idar da sallarasa sai ya fuskanto mutane da fuskarsa, sai ya tambayesu: Shin kun san me Ubangijinku - Mai girma da daukaka - Ya ce ? Sai suka amsa masa: Allah da ManzonSane mafi sani. Sai ya ce: Lallai Allah - Madaukakin sarki - Ya bayyana cewa mutane a lokacin saukar ruwa sun kasu gida biyu: Bangare daya sun yi imani da Allah - Madaukakin sarki -, daya bangaren kuma suka kafircewa Allah - Madaukakin sarki -; Amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da falalar Allah da rahamarSa, ya danganta saukar ruwa ga Allah - Madaukakin sarki -; to wannan ya yi imani da Allah Mahalicci Mai jujjuya al'amura a cikin halittarsa , kuma ya kafircewa taurari. To amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da tauraro iri kaza da kaza; to wannan ya kafircewa Allah kuma ya yi imani da taurari, shi karamin kafarcine ta inda ya danganta saukar ruwa ga taurari; kuma Allah bai sanya shi wani sababi na shari'a ba ko na kaddara, Amma wanda ya danganta saukar ruwa da waninsa daga fararrun abubuwa na kasa ga motsin taurari a bullowarsu da faduwarsu yana mai kudire cewa su ne masu aikin na hakika to shi kafirine kafirci babba.

Fa’idoji
  1. Anso fadin: An yi mana ruwa da falalar Allah da rahamarSa bayan saukar ruwa.
  2. Wanda ya danganta ni'imar saukar ruwa da wasunsu ga taurari a halitta da samarwa to shi kafirine kafirci babba, idan ya danganta shi akan cewa shi wani sababi ne to shi kafirine kafirci karami domin cewa shi ba sababi ne na shari'a ko na gani ba.
  3. Lallai ni'ima tana kasancewa sababi na kafirci idan an butulce, kuma tana zama sababi na imani idan an gode.
  4. Hani akan fadin: "An yi mana ruwa da tauraro kaza da kaza", koda an nufi lokaci; dan toshe kafar shirka.
  5. Wajabcin damfarar zuciya ga Allah - Madaukakin sarki - a jawo ni'imomi da tunkude bala’o’i.
Madogara

صحيح البخاري (1/ 169) (846)، صحيح مسلم (1/ 83) (71)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (2/ 484)، المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (1/ 260).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Lallai ni ina kan tafkina har in kalli wanda zai zo ya iso daga cikinku, za'a rike wasu mutane a kusa da ni, sai in ce: Ya Ubangiji daga gareni ne daga al'ummata ne

عَنْ أَسْمَاءَ بِنْتِ أَبِي بَكْرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، قَالَتْ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنِّي عَلَى الحَوْضِ حَتَّى أَنْظُرَ مَنْ يَرِدُ عَلَيَّ مِنْكُمْ، وَسَيُؤْخَذُ نَاسٌ دُونِي، فَأَقُولُ: يَا رَبِّ مِنِّي وَمِنْ أُمَّتِي، فَيُقَالُ: هَلْ شَعَرْتَ مَا عَمِلُوا بَعْدَكَ، وَاللَّهِ مَا بَرِحُوا يَرْجِعُونَ عَلَى أَعْقَابِهِمْ».
Daga Asma'u bint AbuBakar - Allah Ya yarda da su - ta ce : Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai ni ina kan tafkina har in kalli wanda zai zo ya iso daga cikinku, za'a rike wasu mutane a kusa da ni, sai in ce: Ya Ubangiji daga gareni ne daga al'ummata ne, sai a ce: Shin ka san abinda suka aikata a bayanka, wallahi ba su gushe ba suna komawa akan digadigensu".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa shi zai kasance a ranar Alkiyama akan tafkinsa dan ya ga wanda zai zo daga al'ummarsa zuwa tafkin, Kuma za'a rike wasu mutane a kusa da shi - aminci ya tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Ubangiji daga gareni ne kuma daga al'ummata ne, Sai a ce: Shin ka san abinda suka aikata bayan rabuwarka da su, wallahi ba su gushe ba suna komawa akan bayansu suna yin ridda daga addininsu, su ba sa tare da kai, kuma ba sa cikin al'ummarka.

Fa’idoji
  1. Rahamar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa da kuma kwadayinsa gare su .
  2. Hadarin sabawa abinda (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake akansa.
  3. Kwadaitarwa akan riko da sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 121) (6593)، صحيح مسلم (4/ 1793) (2292)، عمدة القاري (23/144)، البحر المحيط الثجاج (37/322).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com