Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai ni ina kan tafkina har in kalli wanda zai zo ya iso daga cikinku, za'a rike wasu mutane a kusa da ni, sai in ce: Ya Ubangiji daga gareni ne daga al'ummata ne

عَنْ أَسْمَاءَ بِنْتِ أَبِي بَكْرٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، قَالَتْ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنِّي عَلَى الحَوْضِ حَتَّى أَنْظُرَ مَنْ يَرِدُ عَلَيَّ مِنْكُمْ، وَسَيُؤْخَذُ نَاسٌ دُونِي، فَأَقُولُ: يَا رَبِّ مِنِّي وَمِنْ أُمَّتِي، فَيُقَالُ: هَلْ شَعَرْتَ مَا عَمِلُوا بَعْدَكَ، وَاللَّهِ مَا بَرِحُوا يَرْجِعُونَ عَلَى أَعْقَابِهِمْ».
Daga Asma'u bint AbuBakar - Allah Ya yarda da su - ta ce : Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai ni ina kan tafkina har in kalli wanda zai zo ya iso daga cikinku, za'a rike wasu mutane a kusa da ni, sai in ce: Ya Ubangiji daga gareni ne daga al'ummata ne, sai a ce: Shin ka san abinda suka aikata a bayanka, wallahi ba su gushe ba suna komawa akan digadigensu".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa shi zai kasance a ranar Alkiyama akan tafkinsa dan ya ga wanda zai zo daga al'ummarsa zuwa tafkin, Kuma za'a rike wasu mutane a kusa da shi - aminci ya tabbata agare shi - sai ya ce: Ya Ubangiji daga gareni ne kuma daga al'ummata ne, Sai a ce: Shin ka san abinda suka aikata bayan rabuwarka da su, wallahi ba su gushe ba suna komawa akan bayansu suna yin ridda daga addininsu, su ba sa tare da kai, kuma ba sa cikin al'ummarka.

Fa’idoji
  1. Rahamar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga al'ummarsa da kuma kwadayinsa gare su .
  2. Hadarin sabawa abinda (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake akansa.
  3. Kwadaitarwa akan riko da sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 121) (6593)، صحيح مسلم (4/ 1793) (2292)، عمدة القاري (23/144)، البحر المحيط الثجاج (37/322).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Imani da Ranar Lahira

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com