Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Tafkina tafiyar wata ne, ruwansa ya fi nono fari, kamshinsa ya fi almiski kanshi

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رضي الله عنهما قَالَ: قالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «حَوْضِي مَسِيرَةُ شَهْرٍ، مَاؤُهُ أَبْيَضُ مِنَ اللَّبَنِ، وَرِيحُهُ أَطْيَبُ مِنَ المِسْكِ، وَكِيزَانُهُ كَنُجُومِ السَّمَاءِ، مَنْ شَرِبَ مِنْهَا فَلاَ يَظْمَأُ أَبَدًا».
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Tafkina tafiyar wata ne, ruwansa ya fi nono fari, kamshinsa ya fi almiski kanshi, kofunansa kamar taurarin sama ne, wanda ya sha daga gare shi ba zai yi kishirwa ba har abada".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari cewa yana da wani tafki a ranar Alkiyama, tsawonsa tafiyar wata ne kuma fadinsama kamar haka ne. Kuma lallai cewa ruwansa ya fi nono tsananin fari. Kuma cewa kamshinsa mai dadi ne ya fi kamshin almiski. Kuma kofinansa tamkar taurarin sama ne a yawansu, Wanda ya sha daga tafkin da wadancan kofinan ba zai yi kishirwa ba har abada.

Fa’idoji
  1. Tafkin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - matattarar ruwa ne mai girma, muminai za su zo masa daga al'ummarsa a ranar lahira.
  2. Samuwar ni'ima ga wanda zai sha daga tafkin ba zai yi kishirwa ba har abada.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 119) (6579)، صحيح مسلم (4/ 1793) (2292)، المفهم (6/91)، فتح الباري (11/472)، التنوير شرح الجامع الصغير (5/387)، فتح المنعم شرح صحيح مسلم (9/125).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
Imani da Ranar Lahira

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com