عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «مَا مِنْ نَبِيٍّ بَعَثَهُ اللهُ فِي أُمَّةٍ قَبْلِي إِلَّا كَانَ لَهُ مِنْ أُمَّتِهِ حَوَارِيُّونَ، وَأَصْحَابٌ يَأْخُذُونَ بِسُنَّتِهِ وَيَقْتَدُونَ بِأَمْرِهِ، ثُمَّ إِنَّهَا تَخْلُفُ مِنْ بَعْدِهِمْ خُلُوفٌ يَقُولُونَ مَا لَا يَفْعَلُونَ، وَيَفْعَلُونَ مَا لَا يُؤْمَرُونَ، فَمَنْ جَاهَدَهُمْ بِيَدِهِ فَهُوَ مُؤْمِنٌ، وَمَنْ جَاهَدَهُمْ بِلِسَانِهِ فَهُوَ مُؤْمِنٌ، وَمَنْ جَاهَدَهُمْ بِقَلْبِهِ فَهُوَ مُؤْمِنٌ، وَلَيْسَ وَرَاءَ ذَلِكَ مِنَ الْإِيمَانِ حَبَّةُ خَرْدَلٍ».
Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a cikin al'ummarsa kafinni, sai ya kasance akwai Hawariyawa daga al'ummarsa, da sahabban da suke riko da sunnarsa kuma suke koyi da shi, sannan wasu masu sabawa zasu saba a bayansu suna fadin abinda ba sa aikatawa, kuma suna aikata abinda ba'a umarce su ba, wanda ya yakesu da hannunsa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da harshensa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da zuciyarsa to shi muminin ne, kuma babu wani kwatankwacin kwayar komayya na imani bayan hakan".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a wata al'umma kafin shi sai ya kasance yana da tsarkakakku da mataimaka da mayaka masu ikhlasi a cikin al'ummarsa, wadanda suka cancanci kalifanci a bayansa; suna riko da sunnarsa, kuma suna koyi da umarninsa, sannan wasu mutane zasu zo bayan wadancan magabata na garin wadanda babu alheri a cikinsu; suna fadin abinda ba sa aikatawa, kuma suna aikata abinda ba'a umartarsu; wanda ya yakesu da hannunsa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da harshensa to shi muminin ne, wanda ya yakesu da zuciyarsa to shi mumini ne, kuma babu wani imani kwatankwacin kwayar komayya bayan hakan.
Fa’idoji
- Kwadaitarwa akan yakar masu sabawa shari'a da maganganunsu da kuma ayyukansu.
- Rashin yin inkari a zuciya dalili ne akan raunin imani ko tafiyarsa.
- Sawwakewar Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka - ga Annabwa ga wanda zai dauki sakonsu a bayansu.
- Wanda yake son tsira to ya wajaba ya bi tafarkin Annabawa; domin duk wata hanyar da ba hanyarsu ba to halaka ce kuma bata ce.
- Duk lokacin da zamani ya nisanta daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da sahabbansa - Allah Ya yarda da su - sai mutane su bar sunnoni kuma su bi soye-soyen zukatansu, kuma su farar da bidi'o'i.
- Bayanin matakan jihadi, cewa shi da hannu ne ga wanda zai iya canzawa, kamar shuwagabanni da mahukunta da sarakai, haka kuma da magana yana kasancewa ne ta hanyar bayyana gaskiya da kira zuwa gareta, haka kuma da zuciya yana kasancewa ne ta hanyar yin inkarin abin ki da rashin sonsa ko yarda da shi.
- Wajabcin horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ki.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 69) (50).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 276).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص148).
كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (4/ 16).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 209).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «الْإِيمَانُ بِضْعٌ وَسَبْعُونَ -أَوْ بِضْعٌ وَسِتُّونَ- شُعْبَةً، فَأَفْضَلُهَا قَوْلُ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَأَدْنَاهَا إِمَاطَةُ الْأَذَى عَنِ الطَّرِيقِ، وَالْحَيَاءُ شُعْبَةٌ مِنَ الْإِيمَانِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Imani tsagi saba’in- ko Sittin- da wani abu ne, mafi falalarsu faɗin: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, mafi ƙasa kuma kawar da ƙazanta daga hanya. Kunya wani tsagi ce na imani.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana cewar imani rassa ne, kuma halaye ne masu yawa, sun kunshi ayyuka da ƙudurce-ƙudurcen zuciya da maganganu.
Kuma mafi girman ɗabi’un imani da falala shi ne faɗin: "Babu abin bautawa da cancanta sai Allah". Tare da sanin ma’anarta, da kuma aiki da abin da take nunawa na cewa Allah Shi ne abin bauta guda ɗaya, wanda Ya cancanci a bauta masa Shi kaɗai ban da wani ba shi ba.
Kuma mafi ƙarancin ayyukan imani shi ne kawar da duk abin da zai cutar da mutane a kan hanyoyi.
Sannan sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da bayanin cewa kunya tana cikin ɗabi’u na imani, kuma ɗabi’a ce da take zaburarwa a kan yin abu mai kyau da kuma barin mummuna.
Fa’idoji
- Imani matakai ne, wani sashin nasu ya fi wani falala.
- Imani kuma magana ce da kuma aiki da ƙudurin zuci
- Jin kunyar Allah maɗaukaki yana sanyawa kada ya ganka a inda ya hanaka, kada kuma ya rasaka a inda ya umarceka.
- Anbaton adadi ba ya nuna iyakarsu kenan, sai dai yana nuna yawan ayyukan imani ne, domin Larabawa su kan ambaci abu da adadi ba tare da suna nufin kore abin da ba shi ba.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 11) (9).
صحيح مسلم (1/ 63) (35).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين (1/ 154).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 169).
تطريز رياض الصالحين، لفيصل آل مبارك (ص106).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم لهلالي (1/ 205).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: «المُسْلِمُ مَنْ سَلِمَ المُسْلِمُونَ مِنْ لِسَانِهِ وَيَدِهِ، وَالمُهَاجِرُ مَنْ هَجَرَ مَا نَهَى اللَّهُ عَنْهُ».
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa, wanda ya yi hijira shi ne wanda ya kauracewa abinda Allah Ya yi hani daga gare shi ".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa musulmi mai cikakken Musulunci shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa ba ya zaginsu kuma ba ya la'antarsu, ba ya gulmarsu, kuma ba ya tafiya tsakaninsu da kowanne nau'i na nau'ukan cutarwa da harshensa, kuma suka kubuta daga hannunsa ba ya yi musu ta'addanci, ba ya ƙwatar dukiyoyinsu ba tare da wani haƙƙi ba, da makamantan hakan, mai hijira shi ne wanda ya bar abinda Allah - Madaukakin sarki - Ya haramta.
Fa’idoji
- Cikar Musulunci ba ya kasancewa sai da rashin cutar da wasu ta kowanne bangare.
- An kebance harshe da hannu da ambato; Dan yawan kura-kuransu da cutarsu, domin mafi girman sharruka suna bijirowa ne daga garesu.
- Kwadaitarwa akan barin sabo, da lazimtar abinda - Allah Madaukakin sarki - Ya yi umarni da shi.
- Mafificin musulmai shi ne wanda ya sauke haƙƙoƙin Allah - Madaukakin sarki - da haƙƙoƙin musulmai.
- Yin ta'addanci yakan kasance da magana ko da aiki.
- Cikakkiyar hijira ita ce kauracewa abinda Allah - Madaukakin sarki - Ya haramta.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 11) (10).
صحيح مسلم (1/ 65) (40).
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 236).
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 511).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 306).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي سعيد الخُدْريِّ رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «مَنْ رَأَى مِنْكُمْ مُنْكَرًا فَلْيُغَيِّرْهُ بِيَدِهِ، فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِلِسَانِهِ، فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِقَلْبِهِ، وَذَلِكَ أَضْعَفُ الْإِيمَانِ».
Daga Abu Sa'id Al-Kudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa: "Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da harshe, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin imani".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin umarni da canza abin ki - wanda shi ne dukkanin abinda Allah da ManzonSa suka hana - gwargwadon iko, Idan ya ga wani abin ki to yana wajaba akansa ya canja shi da hannu idan yana da iko, Idan ya gajiya akan hakan, to ya canja shi da harshensa, ta hanyar hana mai aikatawar, kuma ya bayyana masa cutar hakan, ya kuma shiryar da shi zuwa alheri maimakon wannan sharrin, Idan ya gajiya daga wannan matakin, to ya canja shi da zuciyarsa shi ne ya ki wannan mummunan aikin, kuma ya yi niyyar cewa shi da yana da iko akan canja shi to da ya aikata, canzawa da zuciya shi ne mafi raunin matakan imani a canja abin ki.
Fa’idoji
- Hadisn asali ne a bayanin matakan canza abin ki.
- Umarni da bi sannu-sannu a hani ga abin ki, kowa gwargwadon iyawarsa da ikonsa.
- Hani daga abin ki wani babi ne mai girma a Addini kuma ba ya faduwa akan wani mutum, kuma ana dorawa kowanne musulmi shi gwargwadon ikonsa.
- Umarni da aikin alheri da hani daga abin ki yana daga dabi'un imani, kuma imani yana karuwa yana kuma raguwa.
- Ana sharadantawa a hani daga abin ki: Sanin cewa wannan aikin abin ki ne.
- Ana shardantawa a canja abin ki: Cewa kada wani abin kin mafi girma daga gare shi ya biyo baya.
- Akwai wasu ladubba da sharuddan da yake kamata ga musulmi ya sansu ga hani daga abin ki.
- Hani daga abin ki yana bukatuwa zuwa ga siyasa ta shari'a, kuma da ilimi da basira.
- Rashin inkari da zuciya yana nuni ga raunin imani.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 69).
جامع العلوم والحكم (2/245).
المعين على تفهم الأربعين (ص 393).
شرح الأربعين النووية للعثيمين (ص: 336).
البحر المحيط الثجاج (2/204).
فتح القوي المتين للعباد (ص 116).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنِ ابْنِ مَسْعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: قَالَ رَجُلٌ: يَا رَسُولَ اللهِ، أَنُؤَاخَذُ بِمَا عَمِلْنَا فِي الْجَاهِلِيَّةِ؟ قَالَ: «مَنْ أَحْسَنَ فِي الْإِسْلَامِ لَمْ يُؤَاخَذْ بِمَا عَمِلَ فِي الْجَاهِلِيَّةِ، وَمَنْ أَسَاءَ فِي الْإِسْلَامِ أُخِذَ بِالْأَوَّلِ وَالْآخِرِ».
Daga Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce: Wani mutum ya ce: ya Manzon Allah, shin za'a kamamu da abinda muka aikata a lokacin Jahiliyya? ya ce: "Wanda ya kyautata a Musulunci ba za'a kama shi da abinda ya aikata ba a lokacin Jahiliyya, wanda kuma ya munana a cikin Musulunci za'a kama shi da na farko da na karshe".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana falalar shiga Musulunci. Kuma cewa wanda ya musulunta kuma ya kyautata Musuluncinsa ya zama mai tsarkakewa mai gaskiya, to ba za’a yi masa hisabi da abinda ya aikata na sabo ba a lokacin Jahiliyya, Wanda ya munana a cikin Musulunci, da ya zama munafiki ko ya yi ridda ga Addininsa, za'a yi masa hisabi da abinda ya aikata a cikin kafirci, da kuma abinda ya aikata a cikin Musulunci.
Fa’idoji
- Himmatuwar sahabbai - Allah Ya yarda da su - da kuma tsoronsu daga abinda ke tare da su na ayyukan Jahiliyya (da suka yi a baya).
- Kwadaitarwa akan tabbata akan Musulunci.
- Falalar shiga addinin Musulunci, kuma cewa shi yana kankare ayyukan da suka gabata.
- Wanda ya yi ridda da munafiki za’a yi masa hisabi da dukkanin wani aikin da ya gabatar a lokacin Jahiliyya, haka ma kuma da dukkanin wani zinibin da ya aikata shi a cikin Musulunci.
Madogara
صحيح البخاري (9/ 14) (6921).
صحيح مسلم (1/ 111) (120).
مشارق الأنوار على صحاح الآثار (2/229).
الكواكب الدراري (24/43).
عمدة القاري شرح صحيح البخاري (24/ 76).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قال: جَاءَ نَاسٌ مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَسَأَلُوهُ: إِنَّا نَجِدُ فِي أَنْفُسِنَا مَا يَتَعَاظَمُ أَحَدُنَا أَنْ يَتَكَلَّمَ بِهِ، قَالَ: «وَقَدْ وَجَدْتُمُوهُ؟» قَالُوا: نَعَمْ، قَالَ: «ذَاكَ صَرِيحُ الْإِيمَانِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wasu mutane daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun zo wurisa sai suka tambaye shi: Mu muna ji a cikin zuciyarmu abinda da dayan mu zai fada to da yana da girma, ya ce: "Kuma hakika kun same shi ?" Suka ce: Eh, ya ce: "Wannan shi ne imani baro-baro".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Wasu jama'a daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun zo sai suka tambaye shi game da abinda suke jinsa a cikin zuciyar su na manyan al'amuran da furta su zai girmama akansu saboda muninsu da kuma kyamarsu garesu. Sai tsira da aminci su tabbata agare shi ya ce: Lallai abinda kuke samunsa shi ne imani baro-baro da sakankancewar da zai kaiku ga hana abinda Shaidan yake jefawa acikin zuciya da kuma inkarinku ga furta shi, da girmama hakan acikin zukatan ku, kuma lallai cewa Shaidan ba ya samun dama a cikin zukatanku, sabanin wanda ya samu dama a zuciyarsa kuma bai samu abinda zai tunkude masa hakan ba.
Fa’idoji
- Bayanin raunin Shaidan ga ma'abota imani yayin da bai samu wani iko ba sai wasiwasi kawai.
- Rashin gasgatawa da karbar abinda yake zuwa a rai na wasiwasi, cewa su daga Shaidan ne.
- Wasiwasin Shaidan ba ya cutar da mumini, saidai ya nemi tsarin Allah daga wasiwasinsa, ya kuma hanu daga zarcewa a cikin hakan.
- Shiru ba ya kamata ga musulmi daga abinda yake rikice masa a al'amarin Addininsa, tamabaya game hakan ne ya kamata.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 119) (132)، معالم السنن (4/174)، المفهم للقرطبي (1/344)، شرح النووي على مسلم (2/154)، البحر المحيط الثجاج (3/622).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرِو بْنِ الْعَاصِ رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ الْإِيمَانَ لَيَخْلَقُ فِي جَوْفِ أَحَدِكُمْ كَمَا يَخْلَقُ الثَّوْبُ الْخَلِقُ، فَاسْأَلُوا اللَّهَ أَنْ يُجَدِّدَ الْإِيمَانَ فِي قُلُوبِكُمْ».
Daga Abdullahi Dan Amr Dan Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai imani yana tsufa a zukatan dayanku kamar yadda tsohon tufafi yake tsufa, ku roki Allah Ya sabunta imani a cikin zukatanku".
Hakim da Dabrani ne suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa imani yana tsufa a cikin zuciyar musulmi kuma yana rauni kamar sabon tufafin da yake tsufa saboda tsawon amfani da shi. Saboda yankewa a ibada, ko aikata sabo da afkawa a cikin sha'awowi. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da cewa mu roki Allah - Madaukakin sarki - ya sabunta imaninmu, ta hanayar tsayuwa da wajibai da yawan zikiri da istigfari.
Fa’idoji
- Kwadaitarwa akan rokon Allah tabbata da sabunta imani a cikin zuciya.
- Imani fada ne da aikatawa da kudircewa, yana karuwa da biyayya, kuma yana raguwa da sabo.
Madogara
المستدرك على الصحيحين للحاكم (1/ 45) (5)، المعجم الكبير للطبراني (13/ 36) (84)، النهاية في غريب الحديث والأثر، ص(282)، النهاية (1/316)، فيض القدير (2/323)، التنوير شرح الجامع الصغير (3/434).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنِ الْعَبَّاسِ بْنِ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ رضي الله عنه أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ: «ذَاقَ طَعْمَ الْإِيمَانِ مَنْ رَضِيَ بِاللهِ رَبًّا، وَبِالْإِسْلَامِ دِينًا، وَبِمُحَمَّدٍ رَسُولًا».
Daga Abbas ɗan Abdulmuɗɗalib - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Ya ɗanɗani ɗanɗanon imani wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammadu a matsayin Manzo".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa mumini mai gaskiya a cikin imaninsa wanda zuciyarsa ta nutsu da shi zai samu kuma zai riska a cikin zuciyarsa buɗi da yalwa da farin ciki da zaƙi, da jin daɗin kusanci ga Allah - Maɗaukakin sarki - idan ya yarda da abu uku:
Na farko: Ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, hakan ƙirjinsa ya buɗe ga abinda zai zo masa daga Allah da hukuncin Rububiyyah na raba arzuƙa da halaye, ba zai samu bijirewa ba a cikin zuciyarsa akan wani abu daga hakan, kuma bai nemi wani Ubangiji wanin Allah - Maɗaukakin sarki ba.
Na biyu: Ya yarda da musulunci a matsayin addini, hakan shi ne ƙirjinsa ya buɗe ga abinda musulunci ya ƙunsa na takalif da wajibai, bai tafi zuwa wanin hanyar Musulunci ba.
Na uku: Ya yarda da (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a matsayin Manzo, hakan shi ne ƙirjinsa ya buɗe kuma ya yi farin ciki da dukkan abinda ya zo da shi ba tare da wani kaikawo ko kokwanto ba, bai shiga (wata hanya ba) sai abinda ya dace da shiriyar Manzonsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Fa’idoji
- Imani yana da zaƙi da ɗanɗano da yake zaƙaƙa zukata, kamar yadda zaƙin abinci da abin sha suke zaƙaƙa baki.
- Jiki ba ya samun zaƙin abinci da abin sha sai a lokacin lafiyarsa, to haka nan zuciya idan ta kuɓuta daga cututtukan soye-soyen zuciya masu ɓatarwa da sha'awowi ababen haramtawa, to ya samu zaƙin imani, a duk lokacin da ya samu rashin lafiya da masassara ba zai samu zaƙin imani ba, kai zai iya jin zaƙin abinda a cikinsa akwai halakarsa da son zuciya da saɓo.
- Mutum idan ya yarda da wani al'amari kuma ya so shi to al'amarinsa zai yi sauƙi gare shi, wani abu daga gare shi ba zai yi masa wahala ba, kuma ya yi farin ciki da dukkan abinda ya zo da shi, kuma zuciyarsa ta cakuɗa da walwalarsa, to haka nan mumini idan imani ya shiga zuciyarsa, to sai biyayyar Ubangijinsa ta sauƙaƙa gareshi kuma ransa ya ji daɗi gareta, wahalhalunta ba zasu wahalar da shi ba.
- Ibunl-Kayim ya ce: Wannan Hadisin ya ƙunshi yarda da RububiyyarSa - tsarki ya tabbatar maSa da UluhiyyarSa, da yarda da ManzonSa da jawuwa gareShi, da yarda da addininSa da miƙa wuya gare shi.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 62) (34)، البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (2/ 11)، إكمال المعلم بفوائد مسلم (1/ 270).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com