Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai imani yana tsufa a zukatan dayanku kamar yadda tsohon tufafi yake tsufa, ku roki Allah Ya sabunta imani a cikin zukatanku

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرِو بْنِ الْعَاصِ رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ الْإِيمَانَ لَيَخْلَقُ فِي جَوْفِ أَحَدِكُمْ كَمَا يَخْلَقُ الثَّوْبُ الْخَلِقُ، فَاسْأَلُوا اللَّهَ أَنْ يُجَدِّدَ الْإِيمَانَ فِي قُلُوبِكُمْ».
Daga Abdullahi Dan Amr Dan Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai imani yana tsufa a zukatan dayanku kamar yadda tsohon tufafi yake tsufa, ku roki Allah Ya sabunta imani a cikin zukatanku".
Hakim da Dabrani ne suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa imani yana tsufa a cikin zuciyar musulmi kuma yana rauni kamar sabon tufafin da yake tsufa saboda tsawon amfani da shi. Saboda yankewa a ibada, ko aikata sabo da afkawa a cikin sha'awowi. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da cewa mu roki Allah - Madaukakin sarki - ya sabunta imaninmu, ta hanayar tsayuwa da wajibai da yawan zikiri da istigfari.

Fa’idoji
  1. Kwadaitarwa akan rokon Allah tabbata da sabunta imani a cikin zuciya.
  2. Imani fada ne da aikatawa da kudircewa, yana karuwa da biyayya, kuma yana raguwa da sabo.
Madogara

المستدرك على الصحيحين للحاكم (1/ 45) (5)، المعجم الكبير للطبراني (13/ 36) (84)، النهاية في غريب الحديث والأثر، ص(282)، النهاية (1/316)، فيض القدير (2/323)، التنوير شرح الجامع الصغير (3/434).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ƘARUWAR IMANI DA RAGUWARSA

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com