Jundub ibnu Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali mu muna samari mun kusa balaga, ƙarfafa masu tsananin ƙarfi, sai muka san imani a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kafin mu koyi Alƙur'ani, sannan muka koyi Alƙur'ani, sai imaninmu ya ƙaru da shi.
- Bayanin cewa imani yana ƙaruwa kuma yana raguwa.
- Jeranta abin da ya fi kamata a lokacin tarbiyyar mai tasowa, da kuma kwaɗayi akan cika musu imani.
- Alƙur'ani yana ƙara imani, kuma zuciya tana haskaka da shi, kuma ƙirji yana buɗewa da shi.
سنن ابن ماجه (1/ 42) (61). مشارق الأنوار الوهاجة ومطالع الأسرار البهاجة في شرح سنن الإمام ابن ماجه (2/ 255). مرشد ذوي الحجا والحاجة إلى سنن ابن ماجه والقول المكتفى على سنن المصطفى (1/ 227).