عَنْ عَلِيٍّ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُقْرِئُنَا القُرْآنَ عَلَى كُلِّ حَالٍ مَا لَمْ يَكُنْ جُنُبًا.
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana karantar da mu Alƙur'ani a kowanne hali muddin dai bai kasance yana da janaba ba.
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana koyar da sahabbansa Alƙur'ani yana karantar da su shi a dukkanin halayensa muddin dai bai kasance yana da janaba ta hanyar jima'i ba.
Fa’idoji
- Rashin halaccin karatun Alƙur'ani ga mai janaba har sai ya yi wanka.
- Koyarwa a aikace.
Madogara
سنن الترمذي (1/ 214) (146). سنن أبي داود (1/ 164) (229). سنن النسائي (1/ 144) (265). سنن ابن ماجه (1/ 375) (594). مسند أحمد (2/ 61) (627). النهاية في غريب الحديث والأثر (917-167).