Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ambaton Allah a kodayaushe

عن عائشة رضي الله عنها قالت: كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَذْكُرُ اللهَ عَلَى كُلِّ أَحْيَانِهِ.
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ambaton Allah a kodayaushe.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Nana A'isha uwar Muminai Allah Ya yarda da ita, tana ba da bayanin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana tsananin kwaɗayi a kan yin ambaton Allah maɗaukaki, kuma ya kasance yana ambaton Allah a kowanne lokaci da kowanne yanayi.

Fa’idoji
  1. Ba a sharɗanta tsarkin ƙaramin hadasi ko babba a ambaton Allah ba.
  2. Dawwamar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a ambaton Allah maɗaukaki.
  3. Kwaɗaitarwa a kan yawaita ambaton Allah maɗaukaki a kowanne lokaci domin koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai a yanayin da aka hana ambaton Allah kamar lokacin biyan buƙata.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 282) (373). صحيح البخاري (1/ 68)، (1/ 129). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، للبسام (1/ 315). فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (1/ 273). مجموع فتاوى ومقالات، لابن باز (26/ 17).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
HUKUNCE-HUKUNCEN ALƘUR'ANI DA MUS'HAFAI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com