Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

HUKUNCE-HUKUNCEN ALƘUR'ANI DA MUS'HAFAI

Hadisai 3

Lallai cewa a cikin littafin da Manzon Allah SAW ya rubuta zuwa Amr Bn Hazm lallai cewa kada wanda ya tava Qur'ani sai yana da tsarki

عن عبد الله بن أبي بكر بن حزم، أن في الكتاب الذي كتبه رسول الله صلى الله عليه وسلم لعَمْرو بن حَزْم: «أن لا يَمَسَّ القرآن إلا طَاهر».
Daga Abdullahi Bn Abi bakr Bn Hazm "Lallai cewa a cikin littafin da Manzon Allah SAW ya rubuta zuwa Amr Bn Hazm lallai cewa kada wanda ya tava Qur'ani sai yana da tsarki"
Malik Ya Rawaito shi - Al-Darumi Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara

الموطأ، تأليف: مالك بن أنس الأصبحي، تحقيق: محمد مصطفى الأعظمي ، الناشر: مؤسسة زايد بن سلطان آل نهيان ، الطبعة: الأولى، 1425 هـ. سنن الدارمي، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن الدارمي، تحقيق: حسين سليم أسد الداراني الناشر: دار المغني للنشر والتوزيع، الطبعة: الأولى، 1412 هـ - 2000 م. صحيح الجامع الصغير وزيادته، تأليف: محمد ناصر الدين الألباني، الناشر: المكتب الإسلامي. تسهيل الإلمام بفقه الأحاديث من بلوغ المرام، تأليف: صالح بن فوزان بن عبد الله الفوزان، الطبعة: الأولى، 1427 ه - 2006 م. توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، تأليف: عبد الله بن عبد الرحمن بن صالح البسام، الناشر: مكتبة الأسدي، مكة المكرّمة، الطبعة: الخامِسَة، 1423 هـ - 2003 م. فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام لمحمد بن صالح بن محمد العثيمين، تحقيق: صبحي بن محمد رمضان، وأُم إسراء بنت عرفة، ط1، المكتبة الإسلامية، مصر، 1427هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ambaton Allah a kodayaushe

عن عائشة رضي الله عنها قالت: كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَذْكُرُ اللهَ عَلَى كُلِّ أَحْيَانِهِ.
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ambaton Allah a kodayaushe.
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Nana A'isha uwar Muminai Allah Ya yarda da ita, tana ba da bayanin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana tsananin kwaɗayi a kan yin ambaton Allah maɗaukaki, kuma ya kasance yana ambaton Allah a kowanne lokaci da kowanne yanayi.

Fa’idoji
  1. Ba a sharɗanta tsarkin ƙaramin hadasi ko babba a ambaton Allah ba.
  2. Dawwamar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a ambaton Allah maɗaukaki.
  3. Kwaɗaitarwa a kan yawaita ambaton Allah maɗaukaki a kowanne lokaci domin koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai a yanayin da aka hana ambaton Allah kamar lokacin biyan buƙata.
Madogara

صحيح مسلم (1/ 282) (373). صحيح البخاري (1/ 68)، (1/ 129). توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام، للبسام (1/ 315). فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام، لابن عثيمين (1/ 273). مجموع فتاوى ومقالات، لابن باز (26/ 17).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana karantar da mu Alƙur'ani a kowanne hali muddin dai bai kasance yana da janaba ba

عَنْ عَلِيٍّ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُقْرِئُنَا القُرْآنَ عَلَى كُلِّ حَالٍ مَا لَمْ يَكُنْ جُنُبًا.
Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana karantar da mu Alƙur'ani a kowanne hali muddin dai bai kasance yana da janaba ba.
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana koyar da sahabbansa Alƙur'ani yana karantar da su shi a dukkanin halayensa muddin dai bai kasance yana da janaba ta hanyar jima'i ba.

Fa’idoji
  1. Rashin halaccin karatun Alƙur'ani ga mai janaba har sai ya yi wanka.
  2. Koyarwa a aikace.
Madogara

سنن الترمذي (1/ 214) (146). سنن أبي داود (1/ 164) (229). سنن النسائي (1/ 144) (265). سنن ابن ماجه (1/ 375) (594). مسند أحمد (2/ 61) (627). النهاية في غريب الحديث والأثر (917-167).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com