Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

sun kasance suna koyan ayoyi goma daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ba sa koyan wasu goman daban har sai sun san abinda ke cikin wadannan na ilimi da aiki

عَنْ أَبِي عَبْدِ الرَّحْمَنِ السُّلَمي رحمه الله قَالَ: حَدَّثَنَا مَنْ كَانَ يُقْرِئُنَا مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُمْ كَانُوا يَقْتَرِئُونَ مِنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَشْرَ آيَاتٍ، فَلَا يَأْخُذُونَ فِي الْعَشْرِ الْأُخْرَى حَتَّى يَعْلَمُوا مَا فِي هَذِهِ مِنَ الْعِلْمِ وَالْعَمَلِ، قَالُوا: فَعَلِمْنَا الْعِلْمَ وَالْعَمَلَ.
Daga Abu Abdurrahman Al-Sulami - Allah ya yi masa rahama - ya ce: Wadanda suka kasance suna karantar damu daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun zantar damu cewa su sun kasance suna koyan ayoyi goma daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ba sa koyan wasu goman daban har sai sun san abinda ke cikin wadannan na ilimi da aiki, suka ce: Sai muka koyi ilimi da aiki.
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun kasance suna koyo daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ayoyi goma daga Alkur’ani, ba sa cirata zuwa wasu har sai sun san abinda ke cikin wadannan goman na ilimi kuma suna aiki da shi, sai suka koyi ilimi da aiki gaba daya.

Fa’idoji
  1. Falalar sahabbai - Allah Ya yarda da su - da kwadayinsu akan koyon Alkur’ani .
  2. Koyon Alkur’ani yana kasancewa ne da ilimi da aiki da abinda ke cikinsa, ba kawai da karanta shi da kuma hardace shi ba kawai.
  3. Ilimi yana kasancewa ne kafin fada da aikatawa .
Madogara

مسند أحمد (38/ 466) (23482).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
ILIMIN TAJWIDI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com