Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

ILIMIN TAJWIDI

Hadisai 4

Ku kawata Muryarku da Qur'ani

عن البراء بن عازب رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «زَيِّنُوا القرآنَ بأصواتِكم».
Daga Al-Barra'a Bn Azib -Allah ya yarda da shi - ya ce Manon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Ku kawata Muryarku da Qur'ani"
Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Abin da ake nufi shi ne kawata Alkur'ani ta hanyar inganta sautukanku yayin karatu, domin magana mai kyau tana kara kyau da kuma kawata ta da murya mai kyau, kuma hikimar hakan ita ce wuce gona da iri a ma'anoni, da kuma sanin abin da ayoyin suka kunsa. na umarni, hani, alkawura da alkawura. Saboda rai a dabi'ance yana son yarda da muryoyi, kuma tunani, tare da kyakkyawar murya, na iya zama mara kyau daga kazanta, don haka tunani ya zama al'umma, kuma idan aka hada shi, abin da ake bukata na girmamawa da sallamawa yana faruwa, kuma abin da ake nufi da inganta murya - a cikin magana - shi ne ci gaban da ke haifar da girmamawa, ba sautukan karin waƙoƙin waƙa da shagala waɗanda ke fitowa daga Limayyadaddun karatu.

Madogara

- سنن أبي داود، تحقيق: محمد محيي الدين عبد الحميد، نشر: المكتبة العصرية، صيدا – بيروت. - السنن الصغرى للنسائي "المجتبى"، تحقيق: عبد الفتاح أبو غدة، نشر: مكتب المطبوعات الإسلامية – حلب، الطبعة: الثانية، 1406ه – 1986م. - مسند الإمام أحمد بن حنبل، تحقيق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى، 1421هـ - 2001م. - سنن ابن ماجه، تحقيق: محمد فؤاد عبد الباقي، نشر: دار إحياء الكتب العربية - فيصل عيسى البابي الحلبي. - صحيح الجامع الصغير وزياداته، للألباني، نشر: المكتب الإسلامي. - شرح كتاب التوحيد من صحيح البخاري، لعبد الله بن محمد الغنيمان، الناشر: مكتبة الدار، المدينة المنورة، الطبعة: الأولى، 1405 هـ. - الميسر في شرح مصابيح السنة, فضل الله بن حسن شهاب الدين التُّورِبِشْتِي, المحقق: د. عبد الحميد هنداوي, مكتبة نزار مصطفى الباز, الطبعة: الثانية، 1429 هـ - 2008 هـ. - شرح سنن النسائي المسمى «ذخيرة العقبى في شرح المجتبى»، المؤلف: محمد بن علي بن آدم الإثيوبي الوَلَّوِي، الناشر: دار المعراج الدولية للنشر - دار آل بروم للنشر والتوزيع, الطبعة الأولى, 1416- 1424. - شرح الطيبي على مشكاة المصابيح المسمى بـ (الكاشف عن حقائق السنن), شرف الدين الحسين بن عبد الله الطيبي, المحقق: د. عبد الحميد هنداوي, الناشر: مكتبة نزار مصطفى الباز - مكة المكرمة - الرياض - الطبعة: الأولى، 1417 هـ - 1997 م. - إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري, أحمد بن محمد بن أبى بكر القسطلاني القتيبي المصري, الناشر: المطبعة الكبرى الأميرية، مصر, الطبعة: السابعة، 1323 هـ.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

sun kasance suna koyan ayoyi goma daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ba sa koyan wasu goman daban har sai sun san abinda ke cikin wadannan na ilimi da aiki

عَنْ أَبِي عَبْدِ الرَّحْمَنِ السُّلَمي رحمه الله قَالَ: حَدَّثَنَا مَنْ كَانَ يُقْرِئُنَا مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُمْ كَانُوا يَقْتَرِئُونَ مِنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَشْرَ آيَاتٍ، فَلَا يَأْخُذُونَ فِي الْعَشْرِ الْأُخْرَى حَتَّى يَعْلَمُوا مَا فِي هَذِهِ مِنَ الْعِلْمِ وَالْعَمَلِ، قَالُوا: فَعَلِمْنَا الْعِلْمَ وَالْعَمَلَ.
Daga Abu Abdurrahman Al-Sulami - Allah ya yi masa rahama - ya ce: Wadanda suka kasance suna karantar damu daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun zantar damu cewa su sun kasance suna koyan ayoyi goma daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ba sa koyan wasu goman daban har sai sun san abinda ke cikin wadannan na ilimi da aiki, suka ce: Sai muka koyi ilimi da aiki.
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaHasan ne
Sharhi

Sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun kasance suna koyo daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ayoyi goma daga Alkur’ani, ba sa cirata zuwa wasu har sai sun san abinda ke cikin wadannan goman na ilimi kuma suna aiki da shi, sai suka koyi ilimi da aiki gaba daya.

Fa’idoji
  1. Falalar sahabbai - Allah Ya yarda da su - da kwadayinsu akan koyon Alkur’ani .
  2. Koyon Alkur’ani yana kasancewa ne da ilimi da aiki da abinda ke cikinsa, ba kawai da karanta shi da kuma hardace shi ba kawai.
  3. Ilimi yana kasancewa ne kafin fada da aikatawa .
Madogara

مسند أحمد (38/ 466) (23482).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

An tambayi Anas yaya karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake? sai ya ce: «Ya kasance yana yin madda

عَنْ قَتَادَةَ قَالَ: سُئِلَ أَنَسٌ كَيْفَ كَانَتْ قِرَاءَةُ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ؟ فَقَالَ: «كَانَتْ مَدًّا»، ثُمَّ قَرَأَ: {بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ} [الفاتحة: 1] يَمُدُّ بِبِسْمِ اللَّهِ، وَيَمُدُّ بِالرَّحْمَنِ، وَيَمُدُّ بِالرَّحِيمِ.
Daga Ƙatada ya ce: An tambayi Anas yaya karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake? sai ya ce: «Ya kasance yana yin madda», sannan ya karanta: {Bismillahir rahmanir rahim}[al-Fatiha:1] yana yin maddar Bismillah, kuma yana yin maddar Al-Rahman, kuma yana yin maddar Al-Rahim.
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

An tambayi Anas ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - yaya karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - na Alƙur'ani yake? sai ya ce: Ya kasance yana jan sautinsa da karatu ja; yana jan Lami kafin Ha'i na lafazin jalalah, kuma yana jan Mim wanda ke kafin Nun daga Al-Rahman, kuma yana jan Ha'i daga Al-Rahim.

Fa’idoji
  1. Madda ita ce jan haruffan madda waɗanda yake sune: Alif da Wawun da kuma Ya'un, idan sun kasance masu ɗauri kuma kafinsu akwai wasalin da ya dace da su.
  2. Bayanin shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin karatun Alƙur'ani.
  3. Ɗabbaƙawa na ilimi na bayanin kaifiyyar karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  4. Sindi ya ce: Faɗinsa: (Yana jan sautinsa ja), wato yana tsawaita haruffan da suka dace ga tsawaitawa yana neman taimako da su akan Tadabburin ma'anonin Alƙur'ani da tinani da kuma gargaɗar da wanda zai wa'azantu.
  5. Muhimmancin sanin Tajwidi da kuma Ulumul Ƙur'an.
  6. Fahimtar nassosi ana komawa ne ga malamai kawai, kamar yadda aka tambayi Anas - Allah Ya yarda da shi - sai ya bayyanawa mai tambayar.
Madogara

صحيح البخاري (6/ 195) (5046). عمدة القاري (20/55).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Cewa an tambayeta game da karatun Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -

عَنِ ابْنِ أَبِي مُلَيْكَةَ: عَنْ بَعْضِ أَزْوَاجِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ -قَالَ: أَبُو عَامِرٍ، قَالَ نَافِعٌ: أُرَاهَا حَفْصَةَ- أَنَّهَا سُئِلَتْ عَنْ قِرَاءَةِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَتْ: إِنَّكُمْ لَا تَسْتَطِيعُونَهَا قَالَ: فَقِيلَ لَهَا أَخْبِرِينَا بِهَا. قَالَ: فَقَرَأَتْ قِرَاءَةً تَرَسَّلَتْ فِيهَا قَالَ أَبُو عَامِرٍ: قَالَ نَافِعٌ: فَحَكَى لَنَا ابْنُ أَبِي مُلَيْكَةَ {الحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ} [الفاتحة: 2] ثُمَّ قَطَّعَ {الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ} [الفاتحة: 1] ثُمَّ قَطَّعَ {مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ}.
Daga Ibnu Abi Mulaikah: Daga wata daga cikin matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Abu Amir ya ce: Nafi'u Ya ce: Ina zatan Nana Hafsa ce - Cewa an tambayeta game da karatun Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce: Lallai ku ba zaku iya ba, ya ce: Sai aka ce mata bamu labarin yadda karatun yake. Ya ce: Sai ta yi karatun da ta yi a sake, Abu Amir ya ce: Nafi'u ya ce: Sai Ibnu Abi Mulaikah ya hakaito mana {Alhamdu lillahi rabbil Aalamin} [al-Fatiha: 2]. sannan ya yanyanke {Al-rahmanur Rahim} [al-Fatiha: 1] sannan ya yanyanke {Maliki yaumud din}.
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

An tambayi Nana Hafsa uwar muminai - Allah Ya yarda da ita -: Yaya Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake karanra Alƙur'ani? Sai ta ce: Lallai ku ba zaku iya irin nasa ba, sai aka ce mata; Faɗa mana. Nafi'u ya ce sai Ibnu Abi Mulaikah ya karanta karatun da yayi shi a hankali; dan ta hakaito kuma ta kusanto musu da yadda karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ke, sai ya karanta: {Alhamdu lillhi rabbil Aalamin} sannan ya yanyanke karatun, {Arrahmanur rahim}, sannan ya yanyanke karatun, {Maliki yaumid din}.

Fa’idoji
  1. Bayanin shiriyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin karatun Alƙur'ani.
  2. Ɗabbaƙawa na ilimi na bayanin kaifiyyar karatun Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  3. Halaccin yin karatu a hankali kuma hakan ya fi kusanto da Tadabburin ma'anoninsa.
  4. Himmatuwar magabata na gari da Alƙur'ani mai girma da kuma aikin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  5. Muhimmancin sanin Tajwidi da kuma Ulumul Ƙur'an.
Madogara

مسند أحمد (44/ 70) (26470). الفتح الرباني لترتيب مسند أحمد الشيباني (3/237).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com