عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «إِنَّ أَثْقَلَ صَلَاةٍ عَلَى الْمُنَافِقِينَ صَلَاةُ الْعِشَاءِ وَصَلَاةُ الْفَجْرِ، وَلَوْ يَعْلَمُونَ مَا فِيهِمَا لَأَتَوْهُمَا وَلَوْ حَبْوًا، وَلَقَدْ هَمَمْتُ أَنْ آمُرَ بِالصَّلَاةِ فَتُقَامَ، ثُمَّ آمُرَ رَجُلًا فَيُصَلِّيَ بِالنَّاسِ، ثُمَّ أَنْطَلِقَ مَعِي بِرِجَالٍ مَعَهُمْ حُزَمٌ مِنْ حَطَبٍ إِلَى قَوْمٍ لَا يَشْهَدُونَ الصَّلَاةَ، فَأُحَرِّقَ عَلَيْهِمْ بُيُوتَهُمْ بِالنَّارِ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai cewa mafi nauyin sallah a kan munafukai (ita ce) sallar Issha'i da sallar Asuba, da sun san abin da ke cikinsu da sun zo musu ko da da jan ciki ne, haƙiƙa na yi niyyar in yi umarni da sallah, sai atsai da ita, sannan in umarci wani mutum ya yi wa mutane sallah, sannan in tafi a tare dani da wasu mazaje a tare da su akwai ɗauri na itatuwa zuwa mutanen da ba sa zuwa sallah, sai na ƙona gidajensu da wuta".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana ba da labari game da munafukai da kasalarsu a kan zuwa sallah, musamman ma sallar Issha'i da Asuba, kuma cewa su da ace suna sanin girman lada da sakamako a halartarsu tare da jama'ar musulmai da sun zo musu ko da da rarrafe ne kamar rarrafen yaro da hannaye da kuma gwiwoyi.
Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi niyyar ya yi umarni a tsai da Sallah, sai ya sanya wani mutumin ya yi wa mutane limanci a maimakonsa, sannan ya tafi tare da shi akwai wanda zai ɗauki ɗauri na itatuwa zuwa mazajen da ba sa zuwa sallar jama'a, sai ya ƙona gidajensu da wuta; sabo da tsananin abin da suka aikata na laifi a hakan, - sai dai bai aikata ba - sabo da abinda ke cikin gidaje na mata da yara da babu-ruwansu da kuma wasunsu cikin masu uzuri waɗanda ba su da wani laifi.
Fa’idoji
- Haɗarin ƙin zuwa sallar jam’i a masallaci.
- Munafukai ba sa nufin komai a ibadarsu sai riya da jiyarwa, ba sa zuwa sallah sai lokacin da mutane suke ganainsu.
- Girman ladan sallar issha'i da Asuba tare da jama'a, kuma cewa su sun cancanci a zo musu ko da da rarrafe ne.
- Kiyaye sallar Issha'i da Asuba kubuta ce daga munafunci, kuma ƙin zuwar musu yana daga siffofin maunafukai.
Madogara
صحيح مسلم (1/ 451) (651).
صحيح البخاري (1/ 132) (657).
الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 88).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص107).
تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 136).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عائشة رضي الله عنها قالت: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «ما أُظُن فُلَانا وفُلَانا يَعْرِفَان من دِيِننَا شَيْئَا».
قال اللَّيث بن سعد أحد رُواة هذا الحديث: هذان الرجلان كانا من المنافقين.
Daga A'isha - Allah ya yarda da ita - ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Ba na zaton haka kuma haka kuma don haka mun san addininmu." Al-Laith bin Saad, daya daga cikin wadanda suka ruwaito wannan hadisin, ya ce: Wadannan mutane biyu munafukai ne.
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
A’isha yardar Allah ta tabbata a gare ta ta fada cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce mata: game da maza biyu kuma ba su san komai ba game da addinin Musulunci. Saboda suna nuna Musulunci da layin kafirci. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ambaci wadannan mutane biyu game da rashi, ba daga gulma da aka hana ba, a'a daga abubuwan da ba makawa. Kar halin da suke ciki ya dimau da wadanda suka jahilci lamarinsu. Kuma suna cewa: "Ba na tunani." Zato a nan: a ma'anar tabbaci; Saboda - addu’ar Allah da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya san munafukai a zahiri ta hanyar Allah ya sanar da su game da su a cikin Surat Bara’a. Wasu daga cikinsu ma sun tsorata. "
Madogara
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي، ط1، دار ابن الجوزي، الدمام، 1415ه.
رياض الصالحين، للنووي، ط1، تحقيق: ماهر ياسين الفحل، دار ابن كثير، دمشق، بيروت، 1428هـ.
رياض الصالحين، ط4، تحقيق: عصام هادي، وزارة الأوقاف والشؤون الإسلامية القطرية، دار الريان، بيروت، 1428هـ.
صحيح البخاري، ط1، تحقيق: محمد زهير بن ناصر الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، 1422ه.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين، ط14، مؤسسة الرسالة، 1407هـ.
شرح صحيح البخاري، لابن بطال، تحقيق: أبو تميم ياسر بن إبراهيم، ط2، مكتبة الرشد - السعودية، الرياض، 1423هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي مسعود عقبة بن عمرو الأنصاري البدري رضي الله عنه قال: لما نزلت آية الصدقة كنَّا نُحَامِلُ على ظُهُورِنَا، فجاء رجل فتصدق بشيء كثير، فقالوا: مُراءٍ، وجاء رجل آخر فتصدق بصاع، فقالوا: إن الله لَغَنيٌّ عن صاع هذا!؛ فنزلت: (الذين يلمزون المطوعين من المؤمنين في الصدقات والذين لا يجدون إلا جهدهم).
Lokacin da ayar sadaka ta sauka, muna dauke da bayanmu, sai wani mutum ya zo ya ba da sadaka mai yawa, sai suka ce: Munafunci, sai wani mutum ya zo ya ba da sadaka, sai suka ce: Allah yana rera waka game da wannan Saa '! Don haka sai na yi wahayi: {Wadanda ke ba da agaji daga cikin muminai sadaka.}
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
تطريز رياض الصالحين، فيصل بن عبد العزيز المبارك، تحقيق: عبد العزيز بن عبد الله آل حمد، دار العاصمة للنشر والتوزيع، الرياض، الطبعة: الأولى 1423هـ، 2002م.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين، مؤسسة الرسالة، بيروت، الطبعة: الرابعة عشر 1407هـ، 1987م.
شرح رياض الصالحين، محمد بن صالح العثيمين، مدار الوطن، الرياض، 1426هـ.
صحيح البخاري، محمد بن إسماعيل البخاري الجعفي، تحقيق: محمد زهير الناصر، دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم: محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى 1422هـ.
صحيح مسلم، مسلم بن الحجاج القشيري النيسابوري، تحقيق محمد فؤاد عبد الباقي، دار إحياء التراث العربي، بيروت، الطبعة: 1423هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن محمد بن زيد: أن نَاسًا قالوا لجده عبد الله بن عمر رضي الله عنهما : إنا ندخل على سَلاطِينِنَا فنقول لهم بخلاف ما نتكلم إذا خرجنا من عندهم، قال: كنا نَعُدُّ هذا نفاقا على عهد رسول الله صلى الله عليه وسلم .
Daga Muhammadu Bn Zaid cewa wasu Mutane sunce da kakansa Abdullahi Bn Umar -Allah ya yarda da su- "Mu muna shiga ga Shugabanninmu sau Mu gaya musu Sacanin abunda Muke faca idan muka futo daga Wurinsu, sai ya ce: Mu muna qirga wannan cikin Munafunci a lokacin Manzon Allah SAW"
Buhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
A kan Abdullah bn Omar - Allah ya yarda da su - mutane sun zo gare shi suna cewa: Muna shiga cikin sarakunanmu muna musu magana, amma idan muka bar su sai mu ce ba haka ba, sai ya ce: Mu sunyi la'akari da wannan munafuncin a zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - saboda sun faru Don haka suka yi karya suka ci amanar abin da suka ba da shawara, don haka aikin sarakuna, ministoci, shugabanni da sarakuna wadanda suka shiga cikin sarakunan dole ne su yi magana da al'amarin yadda yake.
Madogara
رياض الصالحين للنووي، تحقيق: ماهر الفحل، دار ابن كثير، دمشق، ط1، 2007م.
صحيح البخاري، بترقيم محمد فؤاد عبد الباقي.
نزهة المتقين شرح رياض الصاحين، شرح الدكتور مصطفى الخن وآخرين، مؤسسة الرسالة، ط 1. 1987م.
تطريز رياض الصالحين، لفيصل بن عبد العزيز آل مبارك، تحقيق: عبد العزيز آل حمد، دار العاصمة، ط1، الرياض، 2002م.
دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، لابن علان، دار الكتاب العربي، بيروت.
شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين، مؤسسة ابن عثيمين الخيرية، مدار الوطن للنشر، الرياض، ط1426هـ.
كنوز رياض الصالحين، المجلس العلمي كنوز دار إشبيليا، الرياض، ط1، 2009م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه مرفوعاً: «يكشِف ربُّنا عن ساقِه، فيسجدُ له كلُّ مؤمنٍ ومؤمنةٍ، فيبقى كلُّ مَن كان يسجدُ في الدنيا رياءً وسُمْعةً، فيذهبُ ليسجدَ، فيعودَ ظهرُه طبقًا واحدًا».
Daga Abu Sa;id -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Manzon Allah "Ubangijinmu zai yaye Maqyagyamarsa, sai kowane Mumini yayi sujada a gare shi Mace da Namiji, sai Waxanda suka kasance suna Sujada a Duniya saboda riya da jiyarwa su tsaya, sai su tafi suyi Sujada sai bayansu ya Sandare baki xaya"
Bukhari da Muslim suka Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Madogara
صحيح البخاري، نشر: دار طوق النجاة (مصورة عن السلطانية بإضافة ترقيم محمد فؤاد عبد الباقي)، الطبعة: الأولى، 1422ه.
عمدة القاري شرح صحيح البخاري، لمحمود بن أحمد بن موسى الحنفى بدر الدين العينى، الناشر: دار إحياء التراث العربي – بيروت.
مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، لعلي بن سلطان الملا الهروي القاري، الناشر: دار الفكر، بيروت – لبنان، الطبعة: الأولى، 1422هـ - 2002م.
شرح كتاب التوحيد من صحيح البخاري، لعبد الله بن محمد الغنيمان، الناشر: مكتبة الدار، المدينة المنورة، الطبعة: الأولى، 1405 هـ.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عبد الله بن عمرو بن العاصي رضي الله عنهما قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: «إنَّ أكثرَ مُنافِقي أُمَّتي قُرَّاؤها».
An rawaito daga Abdullahi Bn Amr Bn Al--Aas -Allah ya yarda da su- daga Annabi: Annabi bai Kasance Mai Al-fasha ba ko Mai yada Al-fasha ba, kuma ya kasance yana cewa: "Lallai mafi yawan Munafukan Al-ummata sune Makarantanta"
Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Hadisin ya la’anci masu karatun Alkur’ani wadanda suke amfani da shi daban da sanya shi a wasu wurare, ko kuma haddace Alkur’ani a matsayin mai tsoron Allah don nisantar da zargi daga kansu, kuma ba sa aiki da shi kuma suna imani da akasin haka, kuma cewa su ne mafiya munafinci a cikin wannan al’ummar. Saboda munafuki ya nuna imani da Allah, kuma ya boye ma'asumancin jininsa da kudinsa, da kuma mai karantawa wanda ya nuna ta wurin aikinsa nufin lahira, da yabon mutane da nuna duniya, don haka suka tafi kai tsaye wajen saba wa ciki da bayyane.
Madogara
- مسند الإمام أحمد بن حنبل، تحقيق: شعيب الأرنؤوط - عادل مرشد، وآخرون، نشر: مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى، 1421هـ - 2001م.
- فيض القدير شرح الجامع الصغير، للمناوي، المكتبة التجارية الكبرى – مصر، الطبعة: الأولى.
- سلسلة الأحاديث الصحيحة وشيء من فقهها وفوائدها، تأليف محمد ناصر الدين الألباني، الناشر: مكتبة المعارف للنشر والتوزيع، الرياض، الطبعة: الأولى، لمكتبة المعارف.
- التيسير بشرح الجامع الصغير, زين الدين محمد المدعو بعبد الرؤوف بن تاج العارفين بن علي بن زين العابدين الحدادي ثم المناوي, مكتبة الإمام الشافعي – الرياض, الطبعة: الثالثة، 1408هـ - 1988م.
- الفتح الرباني لترتيب مسند الإمام أحمد بن حنبل الشيباني ومعه بلوغ الأماني من أسرار الفتح الرباني, أحمد بن عبد الرحمن بن محمد البنا الساعاتي, دار إحياء التراث العربي, الطبعة: الثانية.
- شرح الطيبي على مشكاة المصابيح المسمى بـ (الكاشف عن حقائق السنن), شرف الدين الحسين بن عبد الله الطيبي, المحقق: د. عبد الحميد هنداوي, الناشر: مكتبة نزار مصطفى الباز، مكة المكرمة - الرياض، الطبعة: الأولى، 1417 هـ - 1997 م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنِ ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: «مَثَلُ الْمُنَافِقِ، كَمَثَلِ الشَّاةِ الْعَائِرَةِ بَيْنَ الْغَنَمَيْنِ تَعِيرُ إِلَى هَذِهِ مَرَّةً وَإِلَى هَذِهِ مَرَّةً».
Daga Dan Umar - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: 'Misalin munafiki, kamar akuya ce mai kaikawo tsakanin turke biyu, tana kaikawo gurin wadannan wani lokaci da kuma zuwa wadancan a wani lokacin".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin halin munafiki kuma shi kamar akuya ce mai kaikawo, ba ta san wanne garke za ta bi ba na tumakai, Tana tafiya zuwa wannan garken wani lokaci, da kuma zuwa wani garken a wani lokacin daban, Su masu dimuwane tasakanin imani da kafirci, su ba sa tare da muminai a zahiri da badini, kuma su ba sa tare da kafirai a zahiri da badini, su dai zahirinsu suna tare da muminai, kuma badininsu suna cikin kokwanto da taraddudi, wani lokaci yana karkata zuwa ga wadannan, wani lokacin kuma zuwa ga wadannan.
Fa’idoji
- Daga shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - buga misali dan kusanto da ma'anoni.
- Bayanin halin munafikai na kaikawo da kokwanto da rashin tabbas.
- Gargadi akan halin munafikai, da kwadaitarwa akan gaskiya da kudirin niyya a kan imani a zahiri da badini.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2146) (2784)، إكمال المعلم بفوائد مسلم (8/ 313)، عمدة القاري شرح صحيح البخاري (16/ 69).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرٍو رضي الله عنهما قال: قال رَسولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَرْبَعٌ مَنْ كُنَّ فِيهِ كَانَ مُنَافِقًا خَالِصًا، وَمَنْ كَانَتْ فِيهِ خَلَّةٌ مِنْهُنَّ كَانَتْ فِيهِ خَلَّةٌ مِنْ نِفَاقٍ حَتَّى يَدَعَهَا: إِذَا حَدَّثَ كَذَبَ، وَإِذَا عَاهَدَ غَدَرَ، وَإِذَا وَعَدَ أَخْلَفَ، وَإِذَا خَاصَمَ فَجَرَ».
Daga Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Abubuwa guda huɗu wanda ya kasance a cikinsa to ya zama munafiki tsantsa, wanda ya kasance a tare da shi akwai wata ɗabi'a daga cikinsu to ya kasance akwai ɗabi'a ta munafunci a tare da shi har sai ya barta:
Idan zai yi magana sai ya yi ƙarya, idan an ƙulla yarjejeniya da shi sai ya yi yaudara, idan ya yi alƙawari sai ya saɓa, idan an yi faɗa da shi sai ya yi fajirci".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargaɗi daga ɗabi'u huɗu idan sun taru a tare da musulmi to ya zama mai tsananin kama da munafukai saboda waɗannan ɗabi'un, wannan ga wanda galibi suka zama a tare da shi akwai waɗannan ɗabi'un, amma wanda suka zama kaɗan to bai shiga cikin su ba, sune:
Na farko: Idan zai yi zance sai ya yi gangancin ƙarya da rashin gaskiya a cikin zancensa.
Na biyu: Idan aka yi yarjejeniya da shi ba zai cika ba, kuma ya yaudari abokinsa.
Na uku: Idan ya yi alƙawari ba zai cika shi ba kuma sai ya saɓa shi.
Na huɗu: Idan aka yi faɗa da shi kuma ya yi rigima tare da wani sai husumarsa ta zama mai tsanani, kuma ya bauɗe daga gaskiya, ya yi dabarar a kin karbar gaskiya da ɓata ta, kuma ya faɗi ɓata da ƙarya.
Domin munafunci shi ne bayyanar da sabanin abinda aka ɓoye, wannan ma'anar samammiya ce a tare da mai waɗannan ɗabi'un, kuma munafuncinsa ya zama a cikin haƙƙin wanda ya zantar da shi, kuma ya yi masa alƙawari, ya amince masa, ya yi husuma da shi, ya yi yarjejeniya da shi cikin mutane, ba wai cewa shi munafuki ne a cikin musulunci ba sai ya bayyanar da shi alhali shi yana ɓoye kafirci, wanda ya kasance a cikinsa akwai wata ɗabi'a daga waɗannan ɗabi'un; to a cikinsa akwai siffa ta munafunci har sai ya barta.
Fa’idoji
- Bayanin sashin almomin munafuki dan tsoratarwa da gargaɗarwa daga afkawa a cikinsu.
- Abin nufi daga Hadisin: Cewa waɗannan ɗabi'un sune ɗabi'un munafunci, kuma mai su mai kama da muanfukai ne a cikin waɗannan ɗabi'un, kuma mai ɗabi'antuwa ne da ɗabi'unsu, ba dan cewa shi munafuki ne mai bayyanar da musulunci ya ɓoye kafirci ba, an ce wannan abin ɗauka ne ga wanda waɗannan ɗabi'un suka rinjaye shi kuma ya yi sakaci da su, ya wulaƙantar da al'amarinsu; wanda ya zama kamar hakan to ya zama mai ɓatacciyar aƙida a galibi.
- Ghazali ya ce: Asalin addini mai taƙaituwa ne a cikin abubuwa uku: Faɗa, da aikatawa, da niyya. Sai ya faɗakar akan ɓacin magana da ƙarya, da kuma ɓacin aiki da ha'inci, da kuma ɓacin niyya da saɓawa alkawari; domin cewa saɓa alƙawari ba ya kawo cikas sai dai idan ƙudirin niyyar akansa ya kasance mai gwamuwa da alƙawari, amma da ya kasance mai ƙudirin niyya da gaske sai wani abu mai hanawa ya bijiro masa ko wani ra'ayi ya bayyana gare shi to wannan ba'a samu surar munafunci daga gare shi ba.
- Munafunci nau'i biyu ne: Munafunci na aƙida, yana fitar da mai shi daga imani, shi ne bayyanar da Musulunci da ɓoye kafirci. Da munafunci na aiki, shi ne kamanceceniya da munafukai a cikin ɗabi'unsu, wannan ba ya fitar da mai shi daga imani, sai dai cewa shi babban laifi ne daga manyan laifuka.
- Ibnu Hajar ya ce: Haƙiƙa malamai sun haɗu akan cewa wanda ya zama mai gaskiya a zuciyarsa da harshansa, kuma ya aikata waɗannan ɗabi'un ba'a yi masa hukunci da kafirci, kuma shi ba munafukin da za'a dawwamar a cikin wuta bane.
- Nawawi ya ce: Wasu jama'a daga malamai sun ce: Abin nufi munafukan da sun kasance a zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai suka zantar da imaninsu, kuma suka yi ƙarya, kuma aka amince musu akan addininsu sai suka yi ha'inci, kuma suka yi alƙawari a cikin al'amarin addini suka taimake shi sai suka saɓa, kuma suka fajircewa abokanan husumarsu.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 16) (34)، صحيح مسلم (1/ 78) (58)، المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (1/ 250)، بهجة قلوب الأبرار (ص 26)، البحر المحيط الثجاج (2/370).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com