Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana ba da labari game da munafukai da kasalarsu a kan zuwa sallah, musamman ma sallar Issha'i da Asuba, kuma cewa su da ace suna sanin girman lada da sakamako a halartarsu tare da jama'ar musulmai da sun zo musu ko da da rarrafe ne kamar rarrafen yaro da hannaye da kuma gwiwoyi. Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi niyyar ya yi umarni a tsai da Sallah, sai ya sanya wani mutumin ya yi wa mutane limanci a maimakonsa, sannan ya tafi tare da shi akwai wanda zai ɗauki ɗauri na itatuwa zuwa mazajen da ba sa zuwa sallar jama'a, sai ya ƙona gidajensu da wuta; sabo da tsananin abin da suka aikata na laifi a hakan, - sai dai bai aikata ba - sabo da abinda ke cikin gidaje na mata da yara da babu-ruwansu da kuma wasunsu cikin masu uzuri waɗanda ba su da wani laifi.
- Haɗarin ƙin zuwa sallar jam’i a masallaci.
- Munafukai ba sa nufin komai a ibadarsu sai riya da jiyarwa, ba sa zuwa sallah sai lokacin da mutane suke ganainsu.
- Girman ladan sallar issha'i da Asuba tare da jama'a, kuma cewa su sun cancanci a zo musu ko da da rarrafe ne.
- Kiyaye sallar Issha'i da Asuba kubuta ce daga munafunci, kuma ƙin zuwar musu yana daga siffofin maunafukai.
صحيح مسلم (1/ 451) (651). صحيح البخاري (1/ 132) (657). الإلمام بشرح عمدة الأحكام، لإسماعيل الأنصاري (1/ 88). تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، للبسام (ص107). تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام، لابن عثيمين (1/ 136).