Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

FALALOLIN ZIKIRI

Hadisai 22

Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, sai dai cewa (Mala'ika) Jibril ya zo min sai ya ba ni labarin cewa Allah - mai girma da ɗaukaka - Yana yi wa mala'iku alfahari da ku

عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ قَالَ: خَرَجَ مُعَاوِيَةُ عَلَى حَلْقَةٍ فِي الْمَسْجِدِ، فَقَالَ: مَا أَجْلَسَكُمْ؟ قَالُوا: جَلَسْنَا نَذْكُرُ اللهَ، قَالَ آللَّهِ مَا أَجْلَسَكُمْ إِلَّا ذَاكَ؟ قَالُوا: وَاللهِ مَا أَجْلَسَنَا إِلَّا ذَاكَ، قَالَ: أَمَا إِنِّي لَمْ أَسْتَحْلِفْكُمْ تُهْمَةً لَكُمْ، وَمَا كَانَ أَحَدٌ بِمَنْزِلَتِي مِنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَقَلَّ عَنْهُ حَدِيثًا مِنِّي: وَإِنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خَرَجَ عَلَى حَلْقَةٍ مِنْ أَصْحَابِهِ، فَقَالَ: «مَا أَجْلَسَكُمْ؟» قَالُوا: جَلَسْنَا نَذْكُرُ اللهَ وَنَحْمَدُهُ عَلَى مَا هَدَانَا لِلْإِسْلَامِ، وَمَنَّ بِهِ عَلَيْنَا، قَالَ: «آللَّهِ مَا أَجْلَسَكُمْ إِلَّا ذَاكَ؟» قَالُوا: وَاللهِ مَا أَجْلَسَنَا إِلَّا ذَاكَ، قَالَ: «أَمَا إِنِّي لَمْ أَسْتَحْلِفْكُمْ تُهْمَةً لَكُمْ، وَلَكِنَّهُ أَتَانِي جِبْرِيلُ فَأَخْبَرَنِي أَنَّ اللهَ عَزَّ وَجَلَّ يُبَاهِي بِكُمُ الْمَلَائِكَةَ».
Daga Abu Sa'id AlKudri ya ce: Mu'awiya ya fito ga wata halƙa a cikin masallaci, sai ya ce: Me ya zaunar da ku? suka ce: Mun zauna muna ambatan Allah, ya ce kun rantse da Allah babu abinda ya zaunar da ku sai hakan? suka ce: Wallahi babu abinda ya zaunar da mu sai hakan, ya ce: Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, kuma babu wani a matsayina daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mafi ƙarancin hadisi daga gareni: Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fito ga wata halƙa daga sahabbansa, sai ya ce; "Me ya zaunar da ku?" suka ce: Mun zauna muna ambatan Allah muna gode masa akan abinda ya shiryar da mu na musulunci, kuma ya yi baiwa da shi garemu, ya ce: "Kun rantse da Allah babu abinda ya zaunar da ku sai hakan? suka ce: Wallahi babu abinda ya zaunar da mu sai hakan, ya ce: "Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, sai dai cewa (Mala'ika) Jibril ya zo min sai ya ba ni labarin cewa Allah - mai girma da ɗaukaka - Yana yi wa mala'iku alfahari da ku".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Mu'awiya Dan Abu Sufyan - Allah Ya yarda da su - ya fito ga wata halƙa a cikin Masallaci, sai ya tambayesu akan wanne abu ne suka taru? sai suka ce: Muna ambatan Allah, sai ya sa suka rantse, Allah Ya yarda da shi - cewa su ba su yi nufin komai da taruwarsu ba sai zikiri, sai suka rantse masa, Sannan ya ce da su: Lallai ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku da kuma kokwanto a gaskiyarku ba, sannan ya bada labari game da matsayinsa ga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma cewa shi babu wani mutum dake da matsayin kusancin sa daga gare shi; dan kasancewar Ummu Habiba 'yar uwarsa ce kuma matar annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ce-, dan kuma kasancewarsa daga marubutan wahayi, tare da hakan to shi mai ƙarancin riwaya ne ga hadisai. Sai ya zantar da su cewa annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fito wata rana daga gidansa, sai ya samesu a zaune a cikin masallaci, suna anbaton Allah suna gode masa akan shiryar da su da ya yi , ya kuma ni’imta su da shi, sai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambaye su ya kuma rantsar da su da irin abinda Mu'awiya - Allah Ya yarda da shi - ya aikata tare sahabban sa. Sannan annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya faɗa musu sababin tambayar sa gare su da kuma rantsar da su da ya yi: Cewa mala'ika Jibrilu - aminci ya tabbata a gare shi - ya zo masa sai ya ba shi labarin cewa Allah - mai girma da ɗaukaka - Yana yi wa mala'iku alfahari da ku, kuma yana bayyanar da falalarku gare su, kuma yana nuna musu kyakkyawan ayyukanku, Yana yabon ku a gurin su.

Fa’idoji
  1. Falalar Mu'awiya - Allah Ya yarda da shi - da kwaɗayin sa akan koyi da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a isar da ilimi.
  2. Halaccin sa a rantse ba tare da tuhuma ba dan faɗakarwa akan muhimmancin alheri.
  3. Falalar majalisan zikiri da ilimi kuma cewa Allah Yana son su kuma Yana yi wa mala'iku alfahari da su.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2075) (2701). نزهة المتقين (2/ 993). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (2/ 522). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (17/ 271).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Shin ba na baku labari da mafificin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a gurin Mamallakinku, mafi ɗaukakarsu a darajojinku

عَنْ أَبِي الدَّرْدَاءِ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَلاَ أُنَبِّئُكُمْ بِخَيْرِ أَعْمَالِكُمْ، وَأَزْكَاهَا عِنْدَ مَلِيكِكُمْ، وَأَرْفَعِهَا فِي دَرَجَاتِكُمْ وَخَيْرٌ لَكُمْ مِنْ إِنْفَاقِ الذَّهَبِ وَالوَرِقِ، وَخَيْرٌ لَكُمْ مِنْ أَنْ تَلْقَوْا عَدُوَّكُمْ فَتَضْرِبُوا أَعْنَاقَهُمْ وَيَضْرِبُوا أَعْنَاقَكُمْ؟» قَالُوا: بَلَى. قَالَ: «ذِكْرُ اللهِ تَعَالَى».
Daga Abu Darda'i - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Shin ba na baku labari da mafificin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a gurin Mamallakinku, mafi ɗaukakarsu a darajojinku kuma mafi alheri agareku daga ciyar da zinari da azirfa, kuma mafi alheri agareku daga ku haɗu da maƙiyanku ku daki wuyan su, suma su daki wuyan ku?" suka ce: Eh. Ya ce: "Ambatan Allah - Maɗaukakin sarki".
Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin kuna son in baku labari ? In sanar da ku da mafificin ayyukanku, kuma mafi ɗaukakarsu, mafi ƙaruwarsu, mafi tsarkinsu, mafi tsaf-tsaf ɗinsu a wurin Allah Mamallaki - Mai girma da ɗaukaka -? kuma mafi ɗaukakarsu a cikin masaukanku a aljanna? kuma mafi alheri gareku daga sadaka da zinare da azirfa? Kuma mafi alheri a gareku daga ku haɗu da kafirai dan yaƙi, sai ku daki wuyansu, su daki wuyanku ? Sahabbai suka ce: Eh, muna son hakan. (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ambatan Allah - Maɗaukakin sarki - a dukkan lokuta da kuma dukkan siffofi da halaye.

Fa’idoji
  1. Cewa dawwama akan ambaton Allah - Maɗaukakin sarki - a zahiri da baɗini yana daga mafi girman kusanci, kuma mafi anfaninsu a wurin Allah - Maɗaukakin sarki -.
  2. Dukkan ayyuka kawai an shara'antasu ne dan tsaida ambaton Allah - Maɗaukkain sarki -, Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: {Ka tsaida sallah dan ambatona}. (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Kaɗai an sanya Dawafi a ɗaki da kuma tsakanin Safa da Marwa, da jifan Jammarat (Shaiɗanu) dan ambatan Allah ne - Maɗaukakin sarki -. Abu Dawud ne da Tirmizi suka fitar da shi.
  3. Izzu ɗan Abdussalam ya faɗa a cikin Kawa'idinsa; Wannan Hadisin yana daga abinda yake nunarwa cewa lada ba ya jerantuwa akan gwargwadan wahala a dukkanin ibadu. Kawai Allah - Maɗaukkain sarki - Zai iya bada lada mai yawa akan aiki ɗan kaɗan sama da yadda zai bada lada akan aiki mai yawa. Lada yana jerantuwa akan banbancin darajoji a matsayi.
  4. AlManawi ya faɗa a cikin Faidil Kadir: Wannan Hadisin za’a ɗauke shi ne akan zikiri ya kasance mafifici ga waɗanda ake magana da su. Da za’a yi magana da wani gwarzo sadauki wanda amfanin musulunci zai samu da shi a cikin yaƙi da an ce da shi yaƙi, ko mawadacin da talakawa za su anfana da dukiyarsa da an ce da shi sadaka, mai iko akan Hajji da an ce da shi Hajji, ko wanda yake da iyaye da an ce da shi yi musu biyayya, da wannan ne za’a haɗa tsakanin Hadisan.
  5. Mafi cikar zikiri abinda harshe ya furta shi tare da Tadabburin zuciya (ma'anoninsa), sannan abinda yake kasancewa da zuciya ita kaɗai kamar tunani, sannan abinda ya kasance da harshe shi kaɗai, a kowanne akwai lada in Allah Ya so - Maɗaukakin sarki -.
  6. Lazimtar musulmi zikiran da suke da lokuta da kuma yanayi kamar zikiran safiya da maraice, da shiga masallaci da gida, da bayan gida da fita daga cikinsu... da wanin hakan zai sanya shi daga masu ambatan Allah da yawa.
Madogara

سنن الترمذي (5/ 389) (3377). سنن ابن ماجه (4/ 705) (3790). مسند أحمد (36/ 33) (21702). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 513). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 985). كنوز رياض الصالحين لمجموعة من الباحثين.

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Masu kaɗaitawa sun rigaya

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَسِيرُ فِي طَرِيقِ مَكَّةَ، فَمَرَّ عَلَى جَبَلٍ يُقَالُ لَهُ جُمْدَانُ، فَقَالَ: «سِيرُوا هَذَا جُمْدَانُ، سَبَقَ الْمُفَرِّدُونَ» قَالُوا: وَمَا الْمُفَرِّدُونَ يَا رَسُولَ اللهِ؟ قَالَ: «الذَّاكِرُونَ اللهَ كَثِيرًا وَالذَّاكِرَاتُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana tafiya a hanyar Makka, sai ya wuce wani dutse ana ce masa Jumdan, sai ya ce: "Ku tafi ! wannan Jumdan ne,Masu kaɗaitawa sun rigaya" Suka ce: Suwaye musu kaɗaitawa ya manzon Allah? ya ce: "Masu ambatan Allah da yawa maza da mata masu ambatan Allah".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana matsayin masu ambatan Allah da yawa, kuma cewa su sun kaɗaita kuma sun riga wasunsu da samun manyan darajoji acikin aljannar ni'ima, kuma ya kamantasu da dutsen Jumdan wanda shi kadai ne babu irinsa a cikin duwatsu.

Fa’idoji
  1. An so yawan zikiri da shagaltuwa da shi, domin rigaya a lahira kawai yana kasancewa ne da yawan ayyukan biyayya, da ikhlasi a cikin ibadu.
  2. Ambatan Allah yana kasancewa ne da harshe kawai, ko da zuciya kawai, ko da harshe da zuciya gaba ɗaya, kuma shi ne mafi girmansu a daraja.
  3. Daga nau’ukan zikiri, (akwai) wuridai na shari'a waɗanda aka ƙayyade su, kamar zikiran safiya da maraice, da bayan sallolin farilla da wasunsu.
  4. Annawawi ya ce: Ka sani cewa falalar zikiri ba ta taƙaita a tasbihi da hailala da tahmidi da kabbara da makamancinsu ba, kai dukkanin mai aiki saboda Allah - Maɗaukakin sarki - na ɗa'a to shi mai ambatan Allah ne - Maɗaukakin sarki - ne.
  5. Ambatan Allah yana daga mafi girman sabubban tabbata a tafarkin Allah, tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Ya ce: {Yaku waɗanda suka yi imani idan kun gamu da wasu jama'a to ku tabbata kuma ku ambaci Allah da yawa wataƙila kwa rabauta} [al-Anfal: 45].
  6. Ta yadda aka kamanta tsakanin masu zikiri da dutsen Jumdan shi ne, kaɗaitaka da warewa; Dutsen Jumdan shi kadai ne a cikin duwatsu, haka nan mai ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -, mai kaɗaituwa shi ne wanda zuciyarsa ta kaɗaita da harshensa da ambatan Ubangijinsa koda ya kasance tsakanin mutane, yana samun debe kewa a lokutan kaɗaitaka, yana damuwa daga yawan cakuɗuwar mutane. Kuma fuskar kamaceceniyar takan zama cewa zikiri sababin tabbata ne zuwa alkairai a duniya da lahira inda matafiyi daga Madina zuwa Makka ya kasance idan ya kai Jumdan ya kasance alamace ta isa Makka, wanda ya kai zuwa gare shi ya kasance ya riga, haka nan mai ambatan Allah - madaukakin sarki - shi ma mai rigayar waninsa ne saboda yawan ambatansa ga Allah - Maɗaukakin sarki -, Allah ne Mafi sani.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2062) (2676). نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (2/ 983). تيسير الكريم الرحمن في تفسير كلام المنان، لابن سعدي (ص665). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (2/ 510). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 516).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Na haɗu da (Annabi) Ibrahim a daren da aka yi Isra'i dani sai ya ce: Ya Muhammad, ka yi wa al'ummarka sallama daga gareni, kuma ka basu labarin cewa aljanna mai daɗin turɓaya ce mai daɗin ruwa ce

عَنِ ابْنِ مَسْعُودٍ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَقِيتُ إِبْرَاهِيمَ لَيْلَةَ أُسْرِيَ بِي فَقَالَ: يَا مُحَمَّدُ، أَقْرِئْ أُمَّتَكَ مِنِّي السَّلاَمَ، وَأَخْبِرْهُمْ أَنَّ الجَنَّةَ طَيِّبَةُ التُّرْبَةِ عَذْبَةُ الْمَاءِ، وَأَنَّهَا قِيعَانٌ، وَأَنَّ غِرَاسَهَا سُبْحَانَ اللهِ وَالحَمْدُ لِلَّهِ وَلاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَاللَّهُ أَكْبَرُ».
Daga Ibnu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Na haɗu da (Annabi) Ibrahim a daren da aka yi Isra'i dani sai ya ce: Ya Muhammad, ka yi wa al'ummarka sallama daga gareni, kuma ka basu labarin cewa aljanna mai daɗin turɓaya ce mai daɗin ruwa ce, kuma ita faƙo ce kuma dashenta (shi ne): Subhanallah, (tsarki ya tabbata ga Allah), Alhamdulillah (godiya ta tabbata ga Allah), Lailaha Illallahu, (babu abin bautawa da gaskiya sai Allah), Allahu Akbar (Allah ne Mafi girma)".
Tirmizi ne ya ruwaito shiDarajaHasan ne a baki dayan Riwayoyin sa
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa ya haɗu da (Annabi) Ibrahim badaɗayi - aminci ya tabbata agare shi - a daren Isra'i da Mi'iraji, sai ya ce masa Ya Muhammad; Ka isarwa da al'ummarka sallama daga gareni, kuma ka sanar dasu cewa aljanna mai daɗin turɓaya ce, mai daɗin ruwa ce babu zartsi a acikinsa, kuma aljanna mai faɗi ce madaidaiciya ce babu itatuwa a cikinta, dashenta (shi ne) kalmomi masu tsarki, sune wanzajju na gari: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne Mafi girma, duk lokacin da musulmi ya faɗesu kuma ya maimaita su za'a yi masa dashe a cikin aljanna.

Fa’idoji
  1. Kwaɗaitarwa akan dawwama akan zikiri dan yawaita dashen aljanna.
  2. Falalar al'ummar musulmi; inda (Annabi) Ibrahim - tsira da aminci su tabbata agare shi - ya isar mata da sallama.
  3. Kwaɗaitarwa (Annabi) Ibrahim - aminci ya tabbata agare shi - ga al'ummar (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cikin yawaitawa daga ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -.
  4. Malam al-Ɗaibi ya ce: Aljanna ...?, sannan Allah - Maɗaukakin sarki - Ya samar mata da bishiyoyi da katangu da falalarsa gwargwdan ayyukan masu aiki; kowane mai aiki akwai abinda ya keɓanta da shi saboda aikinsa, sannan cewa Shi - Allah Maɗaukakin sarki - yayin da Ya sawwaƙa masa dan abinda Ya halicce shi saboda shi na aiki dan ya samu lada da hakan sai Ya sanya shi kamar mai dasa waɗancan bishiyoyin.
Madogara

سنن الترمذي (5/ 455) (3462). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين لسليم الهلالي (2/ 512). الكاشف عن حقائق السنن (شرح المشكاة)، للطيبي (6/ 1831). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (17/ 186). مشكاة المصابيح، للتبريزي (2/ 716). مرعاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح، للمباركفوري (7/ 476). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (2/ 985).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Babu wasu mutane da suke tashi daga wani wurin zaman da ba sa ambaton Allah a cikinsa, face sun tashi kamar mushen jaki, kuma suna masu asara

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَا مِنْ قَوْمٍ يَقُومُونَ مِنْ مَجْلِسٍ لَا يَذْكُرُونَ اللَّهَ فِيهِ إِلَّا قَامُوا عَنْ مِثْلِ جِيفَةِ حِمَارٍ، وَكَانَ لَهُمْ حَسْرَةً».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu wasu mutane da suke tashi daga wani wurin zaman da ba sa ambaton Allah a cikinsa, face sun tashi kamar mushen jaki, kuma suna masu asara".
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wasu mutanen da zasu zauna a wani wurin zama sannan su tashi ba su anbaci Allah a cikinsa ba sai sun tashi kamar waɗanda suka taru akan mushen jaki ta ɓangaren ɗoyi da ƙazanta; hakan yayin da suka shagalta a cikin zance daga anbatan Allah, sai wurin zaman ya zama hasara a kansu a ranar alƘiyama da kuma tawaya da dana-sanin da zata lazimcesu.

Fa’idoji
  1. Abinda aka ambata na gargaɗi daga rafkana daga ambatan Allah ba mai taƙaituwa bane akan wuraren zama kawai ba, kai yana game wasunsu, alNawawi ya ce: An karhanta ga wanda ya zauna a wani wuri ya bar wurin kafin ya ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinsa.
  2. Hasara mai faruwa garesu a ranar alƘiyama: Ko dai da kufcewar lada da sakamako saboda rashin fa'idantuwa daga lokaci a cikin biyayya ga Allah, kodai da zunubi da uƙuba saboda shagaltuwar lokacin da saɓon Allah.
  3. Wannan tsoratarwar idan wannan rafkanar da abubuwan da aka halatta ne, to ta yaya da wuraren zaman da aka haramta waɗanda a cikinsu akwai giba (yi da wani) da annamimanci da wasunsu?!
Madogara

سنن أبي داود (7/ 221) (4855). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 120). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 654).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Shin yanzu haƙiƙa Allah Bai sanya muku abinda zaku dinga sadaka dashi ba? lallai dukkan tasbihi sadaka ne, dukkan kabbara sadaka ce, dukkan tahmidi sadaka ce, dukkan hailala sadaka ce, horo da aikin alheri sadaka ne, kuma hani daga abin ƙi sadaka ne, a cikin tsokar ɗayanku ma sadaka ne

عَنْ أَبِي ذَرٍّ رضي الله عنه: أَنَّ نَاسًا مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالُوا لِلنَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: يَا رَسُولَ اللهِ، ذَهَبَ أَهْلُ الدُّثُورِ بِالْأُجُورِ، يُصَلُّونَ كَمَا نُصَلِّي، وَيَصُومُونَ كَمَا نَصُومُ، وَيَتَصَدَّقُونَ بِفُضُولِ أَمْوَالِهِمْ، قَالَ: «أَوَلَيْسَ قَدْ جَعَلَ اللهُ لَكُمْ مَا تَصَّدَّقُونَ؟ إِنَّ بِكُلِّ تَسْبِيحَةٍ صَدَقَةً، وَكُلِّ تَكْبِيرَةٍ صَدَقَةً، وَكُلِّ تَحْمِيدَةٍ صَدَقَةً، وَكُلِّ تَهْلِيلَةٍ صَدَقَةً، وَأَمْرٌ بِالْمَعْرُوفِ صَدَقَةٌ، وَنَهْيٌ عَنْ مُنْكَرٍ صَدَقَةٌ، وَفِي بُضْعِ أَحَدِكُمْ صَدَقَةٌ»، قَالُوا: يَا رَسُولَ اللهِ، أَيَأتِي أَحَدُنَا شَهْوَتَهُ وَيَكُونُ لَهُ فِيهَا أَجْرٌ؟ قَالَ: «أَرَأَيْتُمْ لَوْ وَضَعَهَا فِي حَرَامٍ أَكَانَ عَلَيْهِ فِيهَا وِزْرٌ؟ فَكَذَلِكَ إِذَا وَضَعَهَا فِي الْحَلَالِ كَانَ لَهُ أَجْرٌ».
Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - Cewa wasu mutane daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun ce wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya Manzon Allah, masu dukiyoyi sun tafi da ladaddaki, suna yin sallah kamar yadda muke yin sallah, suna azimi kamar yadda muke yin azumi, kuma suna yin sadaka da ragowar dukiyoyinsu, ya ce: "Shin yanzu haƙiƙa Allah Bai sanya muku abinda zaku dinga sadaka dashi ba? lallai dukkan tasbihi sadaka ne, dukkan kabbara sadaka ce, dukkan tahmidi sadaka ce, dukkan hailala sadaka ce, horo da aikin alheri sadaka ne, kuma hani daga abin ƙi sadaka ne, a cikin tsokar ɗayanku ma sadaka ne", Suka ce: Ya Manzon Allah, shin ɗayanmu zai zo wa sha'awarsa kuma ya zama yana da lada a cikinta? ya ce: "Shin kuna ganin da ace zai sanyata a cikin haram shin zai zama a kansa akwai zunubi a cikinsa? to haka nan idan ya sanyata a cikin halal zai zama yana da lada".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wasu daga talakawa cikin sahabbai sun kawo kukan halinsu da talaucinsu ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da rashin sadakarsu da dukiyoyi dan su samu lada mai yawa kamar yadda 'yan uwansu masu dukiya da yawa suka samu kuma dan su aikata alheri kamar su; inda cewa su (masu Hali) suna yin sallah kamar yadda muke yin sallah, kuma suna azimi kamar yadda muke yin azimi, kuma suna yin sadaka da ragowar dukiyoyinsu, mu kuma ba ma yin sadaka! Sa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da su akan abinda suke da iko akansa na sadakoki, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Shin yanzu Allah Bai zamo Ya sanya muku abinda zaku dinga sadaka da shi ba akan kanku?! domin cewa faɗinku: Subhanallah, (Tsarki ya tabbata ga Allah) zai zama ladan sadaka gareku, haka nan faɗin: Allahu Akbar, (Allah ne Mafi girma) sadaka ne, da faɗin: La’ilaha illallahu, (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah) sadaka ne, da (Horo da aikin alheri) sadaka ne, da (Hani daga abin ƙi) sadaka ne, kai a cikin jima'in ɗayanku ma ga matarsa sadaka ne. Sai suka yi mamaki, suka ce: Ya Manzon Allah, shin ɗayanmu zai zo wa sha'awarsa kuma ya zama a cikinta akwai lada?! Ya ce; Shin kuna ganin da ace ya sanyata a cikin haram na zina ko waninsa shin zai zama akansa akwai zunubi? to haka nan idan ya sanyata a cikin halal zai zama yana da lada.

Fa’idoji
  1. Rige-rigen sahabbai akan aikata alheri, da kwaɗayinsu a cikin samun babban lada da falala daga wurin Allah - Maɗaukakin sarki -.
  2. Yawan kofofin ayyukan alheri, kuma su suna ƙunsar dukkan aikin da musulmi ya tashi da shi da niyya ta gari da kuma kyakkyawar manufa.
  3. Sauƙin Musulunci da rangwaminsa, kowane musulmi yana da abinda zai aikata shi dan ya bi Allah da shi.
  4. Nawawi ya ce: A cikin wannan akwai dalili akan cewa abubuwan da aka halatta suna zama ayyukan biyayya da niyyoyi na gaskiya, jima'i yana zama ibada idan ya yi nufin biyan haƙƙin mata da shi, da kuma mu'amalantarta da aikin alheri wanda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi umarni da shi, ko neman ɗa na gari, ko kare kansa ko kare matar da hanasu gaba ɗaya daga kallon haram, ko tinani a cikinsa, ko nufinsa, ko wanin haka daga manufofi na gari.
  5. Buga misalai da ƙiyasi; dan ya zama ya fi bayyana kuma ya fi zama a cikin ran mai sauraro .
Madogara

صحيح مسلم (2/ 697) (1006). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 201). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (2/ 161). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (3/ 31). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 150).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Kada harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambatan Allah

عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ بُسْرٍ رضي الله عنه أَنَّ رَجُلاً قَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ إِنَّ شَرَائِعَ الإِسْلاَمِ قَدْ كَثُرَتْ عَلَيَّ، فَأَخْبِرْنِي بِشَيْءٍ أَتَشَبَّثُ بِهِ، قَالَ: «لاَ يَزَالُ لِسَانُكَ رَطْبًا مِنْ ذِكْرِ اللَّهِ».
Daga Abdullahi ɗan Busr - Allah Ya yarda da shi - cewa wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah lallai shari'un musulunci haƙiƙa sun yi mini yawa, ka sanar dani wani abu wanda zan rataya da shi, sai ya ce: "Kada harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambatan Allah".
Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Wani mutum ya kai ƙara wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa nafilifilin ibadu sun yi masa yawa har ya gajiya daga yin su saboda rauninsa, sannan ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da shi ga wani aiki mai sauki mai jawo lada mai yawa wanda zai rataya da shi ya yi riƙo da shi. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya nunar masa harshensa ya zama ɗanye mai motsawa saboda dawwamar ambatan Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - a kowane lokaci da hali; na tasbihi da tahmidi da istigafari da addu'a da makamancin hakan.

Fa’idoji
  1. Falalar dawwama akan ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -.
  2. Daga girman falalar Allah (akwai) sawwaƙe sabubban lada.
  3. Fifikon bayi a rabonsu na ƙofofin aikin lada da alheri.
  4. Yawan ambatan Allah da harshe tasbihi da tahmidi da hailala da kabbara da wanin hakan, tare da dacewar zuciya yana tsayawa matsayin yawa da yawan nafilifilin ayyukan ɗa'a.
  5. Lurarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga masu tambaya da amsawa kowa da abinda ya dace da shi.
Madogara

سنن الترمذي (5/ 388) (3375). سنن ابن ماجه (4/ 707) (3793). مسند أحمد (29/ 226) (17680). جامع العلوم والحكم في شرح خمسين حديثا من جوامع الكلم، لابن رجب الحنبلي (2/ 510). التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، لإسماعيل الأنصاري (ص104). فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، للنووي وابن رجب (ص154). الأحاديث الأربعون النووية وعليها الشرح الموجز المفيد، لعبد الله بن صالح المحسن (ص93).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com

Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari

عن الْأَغَرِّ رضي الله عنه، وَكَانَ مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «يَا أَيُّهَا النَّاسُ تُوبُوا إِلَى اللهِ، فَإِنِّي أَتُوبُ فِي الْيَوْمِ إِلَيْهِ مِائَةَ مَرَّةٍ».
Daga Agar - Allah Ya yarda da shi -, kuma ya kasance daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: Manzon Allah - tsiar da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana umartar mutane da yawaita tuba da istigfari, kuma yana bada labari game da kansa cewa shi yana tuba zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - kuma yana neman gafararSa a yini sama da sau ɗari, alhali haƙiƙa an gafarta masa abinda ya gabatar na zunubinsa da abinda ya jinkirta, a cikin hakan akwai cikar kankan da kai da bauta ga Allah - Maɗaukaki -.

Fa’idoji
  1. Kowane mutum duk yadda matsayinsa da darajarsa suka kai a imani, to shi yana buƙatuwa zuwa komawa ga Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka -, da cika kansa da tuba, kuma babu wanda ba ya wofinta daga kasawa a tsayuwa da haƙƙin Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka -: (Ku tuba zuwa ga Allah gaba ɗaya yaku muminai).
  2. Tuba a game daidai ne daga aikata abubuwan da aka haramta ne da zunubai ko daga kasawa ne a aikata wajibai.
  3. Ikhlasi a cikin tuba sharaɗi ne akan karbar tuban, wanda ya bar wani zunubi ba dan Allah ba to ba ya kasancewa mai tuba.
  4. AlNawawi ya ce: A kwai sharuɗɗa uku ga tuba: Ya bar aikata saɓo, kuma ya yi nadama akan aikata shi, kuma ya ƙudirci niyya a yanke cewa ba zai koma ba zuwa tamkarta ba har abada, idan saɓon yana rataye ne da ɗan Adam to yana da sharaɗi na huɗu, shi ne: Maida abinda aka zalinta zuwa ga mai shi, ko tabbatar da kuɓuta daga gare shi.
  5. Faɗakarwa akan neman gafarar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ya lazimtar cewa ya kasance dan wasu zunuban da ya aikata su ne, sai dai hakan dan cikar ubudiyyarsa ne da kuma danfaruwa da ambatanSa - tsarki ya tabbatar maSa - da jinsa girman haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki - da kasawar bawa duk aikin da ya aikata a godiyar ni'imominSa, hakan yana daga babin shara'antawa ga al'umma a bayansa ne, zuwa wanin hakan daga hikimomi.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2075) (2702). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 33). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (1/ 97). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (1/ 52).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
8 cikin 22
Hadisai 22
  1. Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, sai dai cewa (Mala'ika) Jibril ya zo min sai ya ba ni labarin cewa Allah - mai girma da ɗaukaka - Yana yi wa mala'iku alfahari da ku
  2. Shin ba na baku labari da mafificin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a gurin Mamallakinku, mafi ɗaukakarsu a darajojinku
  3. Masu kaɗaitawa sun rigaya
  4. Na haɗu da (Annabi) Ibrahim a daren da aka yi Isra'i dani sai ya ce: Ya Muhammad, ka yi wa al'ummarka sallama daga gareni, kuma ka basu labarin cewa aljanna mai daɗin turɓaya ce mai daɗin ruwa ce
  5. Babu wasu mutane da suke tashi daga wani wurin zaman da ba sa ambaton Allah a cikinsa, face sun tashi kamar mushen jaki, kuma suna masu asara
  6. Shin yanzu haƙiƙa Allah Bai sanya muku abinda zaku dinga sadaka dashi ba? lallai dukkan tasbihi sadaka ne, dukkan kabbara sadaka ce, dukkan tahmidi sadaka ce, dukkan hailala sadaka ce, horo da aikin alheri sadaka ne, kuma hani daga abin ƙi sadaka ne, a cikin tsokar ɗayanku ma sadaka ne
  7. Kada harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambatan Allah
  8. Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari
  9. Wani bawa ya aikata wani zunubi, sai ya ce: Ya Allah Ka gafarta min zunubina
  10. Shin ba zan gaya muku abin da nake son fada wa Allah ba? Mafi soyuwa ga magana ga Allah: Tsarki ya tabbata ga Allah da yabo
  11. A kan Abu Hurairah - Allah ya yarda da shi - tare da tashe: "Da wanda raina yake a hannunsa, da ba ku yi zunubi ba, da Allah zai fita daga gare ku, kuma ya zo da mutanen da suka yi zunubi, kuma suna neman gafara daga Allah Madaukaki, kuma zai gafarta musu."
  12. Sauran mutanen kirki babu abin bauta sai Allah kuma tsarki ya tabbata ga Allah, Allah ya fi girma kuma godiya ta tabbata ga Allah kuma babu wani karfi a kusa kuma babu wani karfi sai Allah
  13. Dan Adam bai taba aikata wani aiki ba wanda ai tserar da shi daga Azabar Allah Kamar Ambaton Allah
  14. Wanda ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, haɗi da gode masa. A yini sau ɗari, za a share masa laifukansa ko sun kasance kamar kumfar kogi
  15. Wanda ya ce: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, mulki na sa ne, godiya ta sa ce, Shi mai iko ne a kan komai. Sau goma
  16. "Allah Madaukakin Sarki yana cewa: Ni ina tare da Bawa na ko yaushe ya anbace ni kuma Labbansa suka Motsa saboda ni"
  17. Allah baiyi izini ga Annabi da wani Abu ba kamar yadda yayi izini da ya kawata Muryasa da Qur'ani
  18. Idan ladani ya ce: Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, sai ɗayanku ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma
  19. Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati
  20. Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji shi ka nemi tsarin Allah daga gare shi, ka yi tofi a hagunka sau uku
  21. ‌Wanda ya ce: (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki naSa ne, godiya taSa ce, kuma Shi Mai iko ne a kan dukkan komai) sau ɗari a cikin yini
  22. Kada harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambatan Allah

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com