Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Masu kaɗaitawa sun rigaya

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَسِيرُ فِي طَرِيقِ مَكَّةَ، فَمَرَّ عَلَى جَبَلٍ يُقَالُ لَهُ جُمْدَانُ، فَقَالَ: «سِيرُوا هَذَا جُمْدَانُ، سَبَقَ الْمُفَرِّدُونَ» قَالُوا: وَمَا الْمُفَرِّدُونَ يَا رَسُولَ اللهِ؟ قَالَ: «الذَّاكِرُونَ اللهَ كَثِيرًا وَالذَّاكِرَاتُ».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana tafiya a hanyar Makka, sai ya wuce wani dutse ana ce masa Jumdan, sai ya ce: "Ku tafi ! wannan Jumdan ne,Masu kaɗaitawa sun rigaya" Suka ce: Suwaye musu kaɗaitawa ya manzon Allah? ya ce: "Masu ambatan Allah da yawa maza da mata masu ambatan Allah".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana matsayin masu ambatan Allah da yawa, kuma cewa su sun kaɗaita kuma sun riga wasunsu da samun manyan darajoji acikin aljannar ni'ima, kuma ya kamantasu da dutsen Jumdan wanda shi kadai ne babu irinsa a cikin duwatsu.

Fa’idoji
  1. An so yawan zikiri da shagaltuwa da shi, domin rigaya a lahira kawai yana kasancewa ne da yawan ayyukan biyayya, da ikhlasi a cikin ibadu.
  2. Ambatan Allah yana kasancewa ne da harshe kawai, ko da zuciya kawai, ko da harshe da zuciya gaba ɗaya, kuma shi ne mafi girmansu a daraja.
  3. Daga nau’ukan zikiri, (akwai) wuridai na shari'a waɗanda aka ƙayyade su, kamar zikiran safiya da maraice, da bayan sallolin farilla da wasunsu.
  4. Annawawi ya ce: Ka sani cewa falalar zikiri ba ta taƙaita a tasbihi da hailala da tahmidi da kabbara da makamancinsu ba, kai dukkanin mai aiki saboda Allah - Maɗaukakin sarki - na ɗa'a to shi mai ambatan Allah ne - Maɗaukakin sarki - ne.
  5. Ambatan Allah yana daga mafi girman sabubban tabbata a tafarkin Allah, tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Ya ce: {Yaku waɗanda suka yi imani idan kun gamu da wasu jama'a to ku tabbata kuma ku ambaci Allah da yawa wataƙila kwa rabauta} [al-Anfal: 45].
  6. Ta yadda aka kamanta tsakanin masu zikiri da dutsen Jumdan shi ne, kaɗaitaka da warewa; Dutsen Jumdan shi kadai ne a cikin duwatsu, haka nan mai ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -, mai kaɗaituwa shi ne wanda zuciyarsa ta kaɗaita da harshensa da ambatan Ubangijinsa koda ya kasance tsakanin mutane, yana samun debe kewa a lokutan kaɗaitaka, yana damuwa daga yawan cakuɗuwar mutane. Kuma fuskar kamaceceniyar takan zama cewa zikiri sababin tabbata ne zuwa alkairai a duniya da lahira inda matafiyi daga Madina zuwa Makka ya kasance idan ya kai Jumdan ya kasance alamace ta isa Makka, wanda ya kai zuwa gare shi ya kasance ya riga, haka nan mai ambatan Allah - madaukakin sarki - shi ma mai rigayar waninsa ne saboda yawan ambatansa ga Allah - Maɗaukakin sarki -, Allah ne Mafi sani.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2062) (2676). نزهة المتقين، لمجموعة من الباحثين (2/ 983). تيسير الكريم الرحمن في تفسير كلام المنان، لابن سعدي (ص665). بهجة الناظرين، لسليم الهلالي (2/ 510). شرح رياض الصالحين، لابن عثيمين (5/ 516).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLIN ZIKIRI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com