Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Babu wasu mutane da suke tashi daga wani wurin zaman da ba sa ambaton Allah a cikinsa, face sun tashi kamar mushen jaki, kuma suna masu asara

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَا مِنْ قَوْمٍ يَقُومُونَ مِنْ مَجْلِسٍ لَا يَذْكُرُونَ اللَّهَ فِيهِ إِلَّا قَامُوا عَنْ مِثْلِ جِيفَةِ حِمَارٍ، وَكَانَ لَهُمْ حَسْرَةً».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu wasu mutane da suke tashi daga wani wurin zaman da ba sa ambaton Allah a cikinsa, face sun tashi kamar mushen jaki, kuma suna masu asara".
Abu Dawud ne Ya Rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wasu mutanen da zasu zauna a wani wurin zama sannan su tashi ba su anbaci Allah a cikinsa ba sai sun tashi kamar waɗanda suka taru akan mushen jaki ta ɓangaren ɗoyi da ƙazanta; hakan yayin da suka shagalta a cikin zance daga anbatan Allah, sai wurin zaman ya zama hasara a kansu a ranar alƘiyama da kuma tawaya da dana-sanin da zata lazimcesu.

Fa’idoji
  1. Abinda aka ambata na gargaɗi daga rafkana daga ambatan Allah ba mai taƙaituwa bane akan wuraren zama kawai ba, kai yana game wasunsu, alNawawi ya ce: An karhanta ga wanda ya zauna a wani wuri ya bar wurin kafin ya ambaci Allah - Maɗaukakin sarki - a cikinsa.
  2. Hasara mai faruwa garesu a ranar alƘiyama: Ko dai da kufcewar lada da sakamako saboda rashin fa'idantuwa daga lokaci a cikin biyayya ga Allah, kodai da zunubi da uƙuba saboda shagaltuwar lokacin da saɓon Allah.
  3. Wannan tsoratarwar idan wannan rafkanar da abubuwan da aka halatta ne, to ta yaya da wuraren zaman da aka haramta waɗanda a cikinsu akwai giba (yi da wani) da annamimanci da wasunsu?!
Madogara

سنن أبي داود (7/ 221) (4855). بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، لسليم الهلالي (2/ 120). نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (1/ 654).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLIN ZIKIRI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com