Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, haɗi da gode masa. A yini sau ɗari, za a share masa laifukansa ko sun kasance kamar kumfar kogi

عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ قَالَ: سُبْحَانَ اللهِ وَبِحَمْدِهِ، فِي يَوْمٍ مِائَةَ مَرَّةٍ، حُطَّتْ خَطَايَاهُ وَإِنْ كَانَتْ مِثْلَ زَبَدِ الْبَحْرِ».
Daga Abu Hurairah Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Wanda ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah, haɗi da gode masa. A yini sau ɗari, za a share masa laifukansa ko sun kasance kamar kumfar kogi.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Ma’aikin tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin cewa duk wanda a rana ya faɗa sau ɗari: Tsarki ya tabbata ga Allah haɗi da gode masa. an share kurakuransa an kuma gafarta su, ko da suna da yawa misalin farar kunfar nan ce da take saman teku lokacin kaɗawar igiya da ambaliya.

Fa’idoji
  1. Wannan ladan yana samuwa ne ga wanda ya faɗeta a rana a jere ko a rarrabe.
  2. Tasbihi: Tsarkake Allah daga tawaya. Godiya: Siffanta Allah da cika tare da so da kuma girmamawa.
  3. Abin nufi da Hadisin kankare ƙananan zunubai, amma manyan dole sai da an tuba.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 86) (6405). صحيح مسلم (4/ 2071) (2691). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (7/ 535). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 401). فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 470). سبل السلام بشرح بلوغ المرام، للصنعاني (2/ 704).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLIN ZIKIRI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com