Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Wanda ya ce: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, mulki na sa ne, godiya ta sa ce, Shi mai iko ne a kan komai. Sau goma

عن أبي أيوب رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال: «مَنْ قَالَ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ وَلَهُ الْحَمْدُ وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، عَشْرَ مِرَارٍ كَانَ كَمَنْ أَعْتَقَ أَرْبَعَةَ أَنْفُسٍ مِنْ وَلَدِ إِسْمَاعِيلَ».
Daga Abu Ayyub Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Wanda ya ce: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, mulki na sa ne, godiya ta sa ce, Shi mai iko ne a kan komai. Sau goma . zai kasance kamar wanda ya ‘yanta mutane huɗu daga tsatsan (Annabi) Isma’il.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana ba da labarin cewa duk wanda ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake, ba shi da abonkin tarayya, kuma Shi mai iko ne a kan komai. Ma’ana: Babu abin bauta da cancanta sai Allah Shi kaɗai, ba shi da abonkin tarayya, kuma Shi Maɗaukakin Ya keɓanta da cikakken mulki, wanda ya cancanta da Yabo da kambamawa tare da so da girmamawa banda wanda ba shi ba, kuma Shi mai iko ne babu abin da yake gagarar sa. To, duk wanda ya maimaita wannan zikirin a rana sau goma, to, yana da lada misalin ladan wanda ya gusar da bauta daga bayi huɗu cikin zuriyar [Annabi] Isma’il Ɗan [Annabi] Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gare su, kuma ya keɓance zuriyar [Annabi] Isma’il ne amincin Allah ya tabbata a gare shi domin sun fi waɗanda ba su ba.

Fa’idoji
  1. Falalar wannan zikirin wanda ya ƙunshi kaɗaita Allah maɗaukaki da bauta da mulki da godiya da cikakken iko.
  2. Ana samun ladan wannan zikirin ne idan aka yi shi a jere ko a rarrabe.
Madogara

صحيح البخاري (8/ 86) (6404). صحيح مسلم (4/ 2071) (2693). توضيح الأحكام من بلوغ المرام، للبسام (7/ 533). منحة العلام في شرح بلوغ المرام، لعبد الله الفوزان (10/ 399). فتح ذي الجلال والإكرام، لابن عثيمين (6/ 465). سبل السلام بشرح بلوغ المرام، للصنعاني (2/ 703).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
FALALOLIN ZIKIRI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com