Daga Abdullahi ibnu Busr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum Ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Manzon Allah! Lallai cewa shari'un Musulunci sun yawaita a kanmu, to wace ƙofa ce mai tattarowa zamu yi riƙo da ita? ya ce: «Kada harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambatan Allah». A cikin wata riwayar: Daga hadisin Mu'azu ibnu Jabal - Allah Ya yarda da shi -: Ƙarshen abin da na rabu da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kansa shi ne na ce: Wane aiki ne daga cikin ayyuka ya fi kuma ya fi kusanci zuwa ga Allah? Ya ce: «Ka mutu alhali harshenka yana ɗanye daga ambatan Allah».
Ahmad ne ya ruwaito shi da Tirmizi da Ibnu Majah da kuma Ibnu HibbanDarajaIngantacce ne
Sharhi
Wani mutum ya kai ƙara wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa nafilifilin ibadu sun yi masa yawa har ya gajiya daga yin su saboda rauninsa, sannan ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da shi ga wani aiki mai sauki mai jawo lada mai yawa wanda zai rataya da shi ya yi riƙo da shi.
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya nunar masa harshensa ya zama ɗanye mai motsawa saboda dawwamar ambatan Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - a kowane lokaci da hali; na tasbihi da tahmidi da istigafari da addu'a da makamancin hakan.
Fa’idoji
Falalar dawwama akan ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -.
Daga girman falalar Allah (akwai) sawwaƙe sabubban lada.
Fifikon bayi a rabonsu na ƙofofin aikin lada da alheri.
Yawan ambatan Allah da harshe tasbihi da tahmidi da hailala da kabbara da wanin hakan, tare da dacewar zuciya yana tsayawa matsayin yawa da yawan nafilifilin ayyukan ɗa'a.
Lurarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga masu tambaya da amsawa kowa da abinda ya dace da shi.
Madogara
سنن الترمذي (5/ 318) (3375).
سنن ابن ماجه (4/ 707) (3793).
مسند أحمد (29/ 226) (17680).
جامع العلوم والحكم في شرح خمسين حديثا من جوامع الكلم، لابن رجب الحنبلي (2/ 510).
التحفة الربانية في شرح الأربعين حديثًا النووية، لإسماعيل الأنصاري (ص104).
فتح القوي المتين في شرح الأربعين وتتمة الخمسين، للنووي وابن رجب (ص154).
الأحاديث الأربعون النووية وعليها الشرح الموجز المفيد، لعبد الله بن صالح المحسن (ص93).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com