عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤمنينَ رضي الله عنها قَالَتْ: كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُعْجِبُهُ التَّيَمُّنُ، فِي تَنَعُّلِهِ، وَتَرَجُّلِهِ، وَطُهُورِهِ، وَفِي شَأْنِهِ كُلِّهِ.
Daga Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance damantawa tana kayatar da shi, a sanya takalminsa, da taje kansa, da tsarkinsa, kai da sha'aninsa duka.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana so kuma yana fifita cewa ya fara da dama a al'amuransa masu dacewa da girmamawa, daga cikin hakan: Ya fara da kafar dama a sanya takalminsa, kuma yana farawa da dama a taje gashin kansa da gemunsa a tajesu da shafa musu mai, a alwalarsa kuma yana gabatar da dama akan hagu daga hannaye da kafafuwa.
Fa’idoji
- Nawawi ya ce: Wannan ka'ida ce tabbatacciya a shari'a, ita ce: cewa abinda ya kasance daga babin giramamawa da daukaka, kamar sanya tufa da wanduna da huffi da shiga masallaci da asuwaki da sanya kwalli, da yanke farce, da rage gashin baki, da taje kai shi ne yi masa kum, da cire gashin hammata, da aske kai, da sallama daga sallah, da wanke gabban alwala, da fita daga bandaki, da ci da sha, da musafaha, da sumbatar (Alhajarul Aswad) bakin dutse, da wanin hakan na abinda yake a cikin ma'anarsa anso damantawa a cikinsa. Amma abinda ya kasance kishiyarsa kamar shiga bandaki, da fita daga masallaci da face majina, da tsarki, da tube tufafi da wanduna da huffi da abinda ke kama da hakan, to an so haguntawa a cikinsa, wannan saboda girmama dama da kuma daukakarta.
- "Damantawa yana kayatar da shi". Ya kunshi: Farawa a cikin ayyuka da hannun dama, da kafar dama, da bangaren dama, da bada abu da dama.
- Nawawi ya ce: Ka sani cewa daga gabban alwala a kwai wadanda ba’a son damantawa a cikinsu; shi ne kunnuwa da tafuka da kundukuki kai za'a tsarkakesu ne karo daya, idan hakan ya wuyata kamar a hakkin mai dungu da makamancinsa; sai a gabatar da dama.
Madogara
صحيح البخاري (1/ 45) (168).
صحيح مسلم (1/ 226) (268).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعن عائشة رضي الله عنها قالت: "كَانَت يَدُ رسُولِ الله -صلَّى الله عليه وسلَّم- اليُمنَى لِطُهُورِهِ وطَعَامِهِ، وكَانَت اليُسْرَى لِخَلاَئِهِ، ومَا كَانَ مِنْ أَذَى".
عن حفصة رضي الله عنها "أَنَّ رَسُولَ الله -صلَّى الله عليه وسلَّم- كَانَ يَجْعَلُ يَمِينَهُ لِطَعَامِهِ وَشَرَابِهِ وَثِيَابِهِ، وَيَجْعَلُ يَسَارَهُ لِمَا سِوَى ذَلِك".
A kan A’isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: “Hannun Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - shi ne hannun dama don tsarkinsa da abincinsa, kuma hagu na ruwansa ne, kuma babu cutarwa”. A kan Hafsa - Allah ya yarda da ita - "Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana yin rantsuwa game da abincinsa, da abin shansa, da tufafinsa, kuma yana yin hagu"
Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
A’isha - Allah ya yarda da ita - ta bayyana abin da Annabi –sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam - ya kasance yana yin rantsuwa a ciki, da abin da aka yi amfani da hagu, kuma ta ambaci cewa idan aka yi amfani da hagu babu cutarwa a ciki. Kamar tsaftace kai, tsaftace kanka, shakar hanci, kurkurar ruwa, da makamantansu, duk wani abu mai cutarwa, ana biye da hannun hagu, da sauransu. Ana bayar da shi a hannun dama; A karrama ta; Domin daman yafi hagu. Wannan hadisin ya hada da mustahabbancin gabatar da hannun dama ga abin girmamawa, kamar yadda ta ce - yardar Allah ta tabbata a gare ta. Fadin ta: "Zuwa tsarkake shi": yana nufin idan tsarkakewa ya fara da hannun dama, to sai ya fara wanke hannun dama kafin na hagu, da kuma wanke kafar dama a gaban hagu, kuma na kunnuwa, gabobi ne guda, kuma suna cikin kai, don haka yana goge su duka sai dai in zai iya shafawa da hannu daya kawai. Anan zai fara da kunnen dama don larura. Fadin ta: "da abincin sa": wato cin sa. Kuma hannunsa na hagu ya kasance saboda wofinsa: ma'ana, saboda ya shafi tsabtace kai, cin duwatsu da cire datti. Kuma babu wata cutarwa da aka yi, kamar cire tofawa, gamsai, kwarkwata da makamantansu. Hadisin Hafsa ya tabbata daga hadisin A'isha, wanda ya bayyana a cikin bayanin cewa mustahabbi ne a fara da rantsuwa ta hanyar girmamawa, da gabatar da hagu ta hanyar cutarwa da datti. Kalastinja da sabuntawa da makamantansu.
Madogara
رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين، أبو زكريا محيي الدين النووي، تحقيق ماهر الفحل، دار ابن كثير، دمشق، بيروت، الطبعة: الأولى، 1428هـ، 2007م.
سنن أبي داود، سليمان بن الأشعث أبوداود، المحقق: شعَيب الأرنؤوط، محَمَّد كامِل قره بلل، الناشر: دار الرسالة العالمية.
صحيح أبي داود، محمد ناصر الدين الألباني، الناشر: مؤسسة غراس للنشر والتوزيع، الكويت، الطبعة: الأولى، 1423هـ، 2002م.
دليل الفالحين لطرق رياض الصالحين، محمد علي بن البكري بن علان، اعتنى بها: خليل مأمون شيحا، دار المعرفة، بيروت، الطبعة: الرابعة، 1425هـ.
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين، سليم بن عيد الهلالي، دار ابن الجوزي، الدمام، الطبعة: الأولى، 1415هـ.
نزهة المتقين شرح رياض الصالحين، مجموعة من الباحثين، مؤسسة الرسالة، بيروت، الطبعة: الرابعة عشر،1407هـ، 1987م.
شرح رياض الصالحين، محمد بن صالح العثيمين، دار الوطن، الرياض، الطبعة: 1426هـ.
مسند الإمام أحمد بن حنبل، أحمد بن حنبل أبو عبدالله الشيباني، تحقيق: شعيب الأرنؤوط و عادل مرشد، وآخرون، تحت إشراف: عبد الله بن عبد المحسن التركي، مؤسسة الرسالة، الطبعة: الأولى،1421هـ، 2001م.
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَنَسٍ رضي الله عنه: أَنَّ نَفَرًا مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ سَأَلُوا أَزْوَاجَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنْ عَمَلِهِ فِي السِّرِّ؟ فَقَالَ بَعْضُهُمْ: لَا أَتَزَوَّجُ النِّسَاءَ، وَقَالَ بَعْضُهُمْ: لَا آكُلُ اللَّحْمَ، وَقَالَ بَعْضُهُمْ: لَا أَنَامُ عَلَى فِرَاشٍ، فَحَمِدَ اللهَ وَأَثْنَى عَلَيْهِ، فَقَالَ: «مَا بَالُ أَقْوَامٍ قَالُوا كَذَا وَكَذَا؟ لَكِنِّي أُصَلِّي وَأَنَامُ، وَأَصُومُ وَأُفْطِرُ، وَأَتَزَوَّجُ النِّسَاءَ، فَمَنْ رَغِبَ عَنْ سُنَّتِي فَلَيْسَ مِنِّي».
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -: Cewa wasu mutane daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun tambayi matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da aikinsa a ɓoye? sai sashinsu ya ce: Ba zan auri mata ba, sashinsu kuma ya ce: Ba zan ci nama ba, sashinsu ya ce: Ba zan yi bacci akan shinfiɗa ba, sai ya godewa Allah kuma ya yi yabo gare shi, sai ya ce: "Me ya samu wasu mutane ne sun ce kaza da kaza? sai dai cewa ni ina sallah kuma ina bacci, ina azimi ina buɗe baki, kuma ina auren mata, wanda ya ƙi sunnata to ba ya tare da ni".
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Wasu mutane cikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun zo ɗakunan matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, suna tambaya game da ibadarsa a ɓoye a cikin gidansa, lokacin da aka ba su labari kamar cewa su sunga ƙanƙantarta, sai suka ce: Wane mu daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi- ? haƙiƙa an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa da abinda ya jinkirta, saɓanin wanda bai san faruwar gafara gare shi ba to yana buƙatuwa zuwa kai matuƙa a cikin ibada wataƙila ya sameta. Sannan sashinsu ya ce: Ba zan auri mata ba. Sashinsu kuma ya ce: Ba zan ci nama ba. Sashinsu kuma ya ce: Ba zan yi bacci a kan shinfiɗa ba. Sai hakan ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya yi fushi, ya yi wa mutane huɗuba, sai ya godewa Allah kuma ya yi yabo gare shi ya ce: Menene sha'anin wasu mutane ne sun ce kaza da kaza?! Na rantse da Allah lallai cewa nine mafi tsoronku ga Allah kuma mafi taƙawarku gare shi, sai dai cewa ni ina bacci dan in samu ƙarfi akan tsayuwar (dare), kuma ina buɗe baki dan in samu ƙarfin azimi, kuma ina auren mata, wanda ya bijire daga hanyata kuma ya ga cika a waninta, ya riƙi hanyar wanina to ba ya tare da ni.
Fa’idoji
- Son sahabbai - Allah Ya yarda da su - ga alheri, da kuma kwaɗayinsu a cikinsa da kuma koyi da Annabinsu - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Sauƙin wannan shari'ar da rangwaminta, dan riƙo daga aikin Annabinta - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da kuma shiriyarsa.
- Alheri da albarka (suna) cikin koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da bin halayensa maɗaukaka.
- Tsawatarwa daga tsanantawa kai a cikin ibadu da abinda ba zaka iya ba, kuma wannan yana daga halin 'yan bidi'a.
- Ibnu Hajar ya ce: Riƙo da tsanantawa a cikin ibada yana kaiwa zuwa ƙosawa mai yanke asalin ibadar, kuma lazimtar taƙaituwa akan farillai misali, da barin nafilfili yana kaiwa zuwa fifita hutun sangarcewa, da rashin nishaɗi zuwa ga ibada, kuma mafificin al'amura tsaka-tsaki.
- a cikinsa akwai bibiyar halayen manya dan yin koyi da ayyukansu, kuma cewa shi idan saninsa daga maza ya yi wahala to neman yayewarsa daga mata ya halatta.
- A cikinsa akwai wa'azi da jefa mas'alolin ilimi da bayanin hukunce-hukunce ga mukallafai, da kawar da shubuha daga masu ijtihadi.
- Umarni da sauƙaƙawa a cikin ibada, tare da kiyayewa a kanta da kuma farillai da nafilfili; dan musulmi ya kiyaye haƙƙoƙin waninsa a kansa.
- a cikin hadisin akwai nuni akan falalar aure da kwaɗaitarwa a cikinsa.
Madogara
صحيح البخاري (7/ 2) (5063).
صحيح مسلم (2/ 1020) (1401).
تيسير العلام شرح عمدة الأحكام، لعبد الله البسام (ص566).
خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام، لفيصل آل مبارك (ص282).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا قَالَتْ: مَا أَكَلَ آلُ مُحَمَّدٍ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَكْلَتَيْنِ فِي يَوْمٍ إِلَّا إِحْدَاهُمَا تَمْرٌ.
Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Iyalan (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba su taɓa cin abinci sau biyu a rana ɗaya ba sai ɗayansu ya zama dabino ne.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa iyalan gidan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - basu taɓa cin abinci sau biyu ba a rana ɗaya sai ɗayan ya zama dabino ne.
Fa’idoji
- Tawali'un Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da iyalan gidansa, sauda yawa a rana ɗaya ma basu samun wani abin da zasu ci sai abinci ɗaya.
- Dabino ya kasance shine mafi sauƙi a wurinsu akan waninsa.
- Falalar gudun duniya da wadatuwa da kaɗan a rayuwa, kuma kasancewarsa yana daga ɗabi'un Annabawa, da kuma tarihin shugaban Manzanni.
- Cin abinci sau biyu a rana ɗaya yana daga cikin al'amuran da aka halatta, kuma hakan yana daga cikin sanannun al'adun larabawa, domin sun kasance a rana ɗaya suna ci ne sau biyu, abincin rana da abincin dare.
Madogara
صحيح البخاري (8/ 97) (6455).
صحيح مسلم (4/ 2282) (2971).
فتح الباري لابن حجر (11/ 292).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا قَالَتْ: مَا شَبِعَ آلُ مُحَمَّدٍ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مُنْذُ قَدِمَ المَدِينَةَ مِنْ طَعَامِ البُرِّ ثَلاَثَ لَيَالٍ تِبَاعًا، حَتَّى قُبِضَ.
Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Iyalan (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - basu taɓa ƙoshi daga abincin alkama a darare uku ajere ba tunda ya zo Madina, har aka karɓi ransa.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa iyalan gidan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - tun lokacin da Annabi ya zo Madina basu taɓa ƙoshi da alkama ba tsawon kwana uku ajere har (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya koma ga Allah.
Fa’idoji
- Bayanin abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake a kansa shi da iyalansa na ƙarancin rayuwa, domin rayuwa (ta haƙiƙa ita ce ) rayuwar lahira.
- Ibnu Hajar ya ce: Abin da yake a bayyane shi ne cewa dalilin rashin ƙoshinsu galibi ya kasance ne saboda ƙarancin abu a wurinsu, akan cewa su sun kasance sukan samu saidai suna fifita wasunsu ne akan kansu.
Madogara
صحيح البخاري (7/ 75) (5416).
صحيح مسلم (4/ 2282) (2970).
المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (7/ 129).
البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (45/ 129).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا قَالَتْ: كَانَ فِرَاشُ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مِنْ أَدَمٍ، وَحَشْوُهُ مِنْ لِيفٍ، وَلِمُسلمٍ: كَانَ وِسَادَةُ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الَّتِي يَتَّكِئُ عَلَيْهَا مِنْ أَدَمٍ حَشْوُهَا لِيفٌ.
Daga Nana A'isha uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Shimfiɗar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance ta jemammiyar fata ce, cikinta kaba ne, a Riwayar Muslim kuma : Matashin kai na Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - wanda yake dogara a kan shi ya kasance na jemammiyar fata ne, cikinta kaba ce.
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta bada labarin cewa shimfiɗar da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake kwanciya a kanta ta kasance an yi ta ne da jemammiyar fata, kuma a cike ta ke da kaba ta dabino, haka ma matashinsa wanda yake kishingiɗa a kansa.
Fa’idoji
- Bayanin abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake a kansa na zuhudu da bijirewa jin daɗin duniya, tare da cewa Allah - tsarki ya tabbatara maSa Ya ɗaukaka - Ya tabbatar masa da hakan inda a ce ya so ya ji daɗin da ita.
- Halaccin mallakar shimfiɗa da matashi, da kuma bacci a kansu dan jin sauƙaƙa yin bacci.
- Yana kamata ga musulmi ya lura da halinsa da kuma rayuwarsa da halin Annabinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, domin cewa shine abin koyi mai kyau, kuma wanda ya bi tafarkinsa ya shiriya kuma ya rabauta a duniya da lahira.
- Kwaɗayi akan yin tanadi domin lahira, kuma mumini ya wadatu da abin da zai taimake shi akan biyayya ga Allah a duniya, kuma kada ya shagalta da neman tara dukiya a duniya, haƙiƙa Allah Ya zargi wasu mutane sai ya ce: {Alfahari (da yawan 'ya'ya da dukiya) ya shagaltar da ku. Har (kuka mutu) kuka ziyarci ƙaburbura} [al-Takasur: 1-2].
Madogara
صحيح البخاري (8/ 97) (6456).
صحيح مسلم (3/ 1650) (2082).
البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (34/ 662).
إرشاد الساري لشرح صحيح البخاري (9/ 264).
المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (5/ 403).
النهاية في غريب الحديث والأثر (971).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ عَمْرِو بْنِ الحَارِثِ خَتَنِ رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَخِي أُمِّ المؤمِنين جُوَيْرِيَةَ بِنْتِ الحَارِثِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُم، قَالَ: مَا تَرَكَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عِنْدَ مَوْتِهِ دِرْهَمًا وَلاَ دِينَارًا وَلاَ عَبْدًا وَلاَ أَمَةً وَلاَ شَيْئًا، إِلَّا بَغْلَتَهُ البَيْضَاءَ، وَسِلاَحَهُ، وَأَرْضًا جَعَلَهَا صَدَقَةً.
Daga Amr Ibul Haris ɗan uwan mai dakin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ɗan uwar ummul muminina Juwairiyya Bintul Haris - Allah Ya yarda da su -, ya ce: Lokacin rasuwar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai bar dirhami ko dinari ko bawa ko baiwa ko wani abu ba sai farar alfadararsa da makaminsa, da wani filin da ya maida shi sadaka.
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya rasu bai bar dirhamin na azirfaba ko zinari ba, ko bawan da ya mallaka ko baiwar da ya mallaka ko raƙumi ko wani abu na dukiyaba, sai kawai farar alfadararsa wacce yake hawanta, da wani filin da ya bar shi waƙafi a lokacin da yake da lafiya saboda matafiya.
Fa’idoji
- Annabawa ba'a gadarsu.
- Bayanin abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bari bayan mutuwarsa.
- (Annabi) tsira da amincin su tabbata agare shi ya rasu amma bai bar wani abin da yake da kima ba, saboda kyautarsa da kuma ciyarwarsa da kuma kyautatawarsa.
- Karmani ya ce: Wakilin suna a cikin faɗinsa (kuma ya sanyata) mai komawa ne ga duka ukun wato alfadarar da makami da fili bawai zuwa filin kawai ba.
- Al-Khitn: Ɗan'uwar mata, al-Ukhtani kuma ta ɓangaren mace.
Madogara
صحيح البخاري (4/ 2) (2739).
النهاية في غريب الحديث والأثر (254).
فتح الباري لابن حجر (5/ 360).
عمدة القاري شرح صحيح البخاري (14/ 31).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قِيلَ: يَا رَسُولَ اللهِ ادْعُ عَلَى المُشْرِكِينَ قَالَ: «إِنِّي لَمْ أُبْعَثْ لَعَّانًا، وَإِنَّمَا بُعِثْتُ رَحْمَةً».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Aka ce: Ya Manzon Allah ka yi wa mushrikai mummunar addu'a ya ce: "Lallai ni ba'a aikoni mai yawan tsinuwa ba, kaɗai an aikoni ne dan in zama rahama".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
An nemi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa mushrikai mummunar addu'a, sai ya ce: Lallai cewa ni ba'a aikoni daga Allah in zama mai yawan tsinuwa ba ina yi wa mutane mummunar addu'a da nisantarwa da kuma korewa daga rahamar Allah sai in yanke su daga alheri, lallai ni ba'a aikoni dan haka ba, kaɗai an aikoni ne dan in zama sababin alheri da kuma rahama ga mutane baki ɗaya, da kuma muminai a keɓance.
Fa’idoji
- Cikar ɗabi'unsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- Muhimmancin tsaftace harshe daga zagi da tsinuwa dan koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
- A cikinsa akwai hani daga tsinuwa.
- Kwaɗaitarwa akan jin ƙan mutane.
Madogara
صحيح مسلم (4/ 2006) (2599).
المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (6/ 582).
البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (40/ 683).
Wannan hadisi a HadeethEnc.comKowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com