Ya Abubakar, me kake zato da mutum biyun da Allah Shi ne na ukunsu
Sarkin muminai Abubakar al-Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - a lokacin hijira: Na kalli digadigan mushrikai alhali su suna tsaye akan kawunanmu a saman kogon Hira alhali mu muna cikinsa, sai na ce: Ya Manzon Allah da a ce ɗayansu zai yi duba zuwa ga digadigansa zai ganmu ƙarƙashin digadigansa, sai ya ce : Ya Abubakar, me kake zato da mutum biyu Allah ne na ukunsu da nasara da kuma taimako, da kiyayewa da kuma daidaita?!
- Darajar Abubakar al-Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - a abokantakarsa da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a hijirarsa da ya yi daga Makkah zuwa Madina, da kuma rabuwa da ya yi da iyalansa da kuma dukiyarsa.
- Tausayin Abubakar al-Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi -, da kuma fagen soyayyarsa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da kuma yadda ya jiye masa tsoro daga maƙiya.
- Wajabcin amincewa Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da nutsuwa ga kiyayewarSa, da kuma kulawarSa bayan yin ƙoƙari a riƙar kiyayewa.
- Kulawar Allah - Maɗaukakin sarki - ga AnnabawanSa da masoyanSa, da kuma kiyayewarSa garesu da nasara, Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: (Lallai ne Mu zamu taimaki Manzanninmu da waɗanda suka yi imani a rayuwar duniya da kuma ranar da masu shaida zasu tsaya).
- Faɗakarwa akan cewa duk wanda ya dogara ga Allah to Ya isar masa, zai taimake shi, kuma zai kiyaye shi.
- Cikar tawakkalin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga Ubangijinsa, kuma cewa shi ne wanda ake dogaro gareShi, kuma ake fawwala al'amari gareShi.
- Gwarzantakar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da kuma yadda yake sa zukata da rayuka nutsuwa.
- Guduwa da Addini dan jin tsoron maƙiyi, da kuma yin riƙo da sabubba.
صحيح البخاري (5/ 4) (3653). صحيح مسلم (4/ 1854) (2381). شرح صحيح مسلم (149/15). فتح الباري (11/7). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (276/2) شرح رياض الصالحين لابن عثيمين (563/1).