Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

‌Ya Abubakar, me kake zato da mutum biyun da Allah Shi ne na ukunsu

عَنْ أَبِي بَكْرٍ الصِّدِّيقَ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: نَظَرْتُ إِلَى أَقْدَامِ الْمُشْرِكِينَ عَلَى رُءُوسِنَا وَنَحْنُ فِي الْغَارِ، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ لَوْ أَنَّ أَحَدَهُمْ نَظَرَ إِلَى قَدَمَيْهِ أَبْصَرَنَا تَحْتَ قَدَمَيْهِ، فَقَالَ: «يَا أَبَا بَكْرٍ، مَا ظَنُّكَ بِاثْنَيْنِ اللهُ ثَالِثُهُمَا».
Daga Abubakar al-Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kalli digadigan mushrikai akan kawunanmu alhali mu muna cikin kogo, sai na ce: Ya Manzon Allah da a ce ɗayansu zai kalii digadigansa zai ganmu a ƙarƙashin digadigansa, sai ya ce: «‌Ya Abubakar, me kake zato da mutum biyun da Allah Shi ne na ukunsu».
Bukhari da Muslim ne suka rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

Sarkin muminai Abubakar al-Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - a lokacin hijira: Na kalli digadigan mushrikai alhali su suna tsaye akan kawunanmu a saman kogon Hira alhali mu muna cikinsa, sai na ce: Ya Manzon Allah da a ce ɗayansu zai yi duba zuwa ga digadigansa zai ganmu ƙarƙashin digadigansa, sai ya ce : Ya Abubakar, me kake zato da mutum biyu Allah ne na ukunsu da nasara da kuma taimako, da kiyayewa da kuma daidaita?!

Fa’idoji
  1. Darajar Abubakar al-Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - a abokantakarsa da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a hijirarsa da ya yi daga Makkah zuwa Madina, da kuma rabuwa da ya yi da iyalansa da kuma dukiyarsa.
  2. Tausayin Abubakar al-Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi -, da kuma fagen soyayyarsa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da kuma yadda ya jiye masa tsoro daga maƙiya.
  3. Wajabcin amincewa Allah - Mai girma da ɗaukaka -, da nutsuwa ga kiyayewarSa, da kuma kulawarSa bayan yin ƙoƙari a riƙar kiyayewa.
  4. Kulawar Allah - Maɗaukakin sarki - ga AnnabawanSa da masoyanSa, da kuma kiyayewarSa garesu da nasara, Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: (Lallai ne Mu zamu taimaki Manzanninmu da waɗanda suka yi imani a rayuwar duniya da kuma ranar da masu shaida zasu tsaya).
  5. Faɗakarwa akan cewa duk wanda ya dogara ga Allah to Ya isar masa, zai taimake shi, kuma zai kiyaye shi.
  6. Cikar tawakkalin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga Ubangijinsa, kuma cewa shi ne wanda ake dogaro gareShi, kuma ake fawwala al'amari gareShi.
  7. Gwarzantakar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da kuma yadda yake sa zukata da rayuka nutsuwa.
  8. Guduwa da Addini dan jin tsoron maƙiyi, da kuma yin riƙo da sabubba.
Madogara

صحيح البخاري (5/ 4) (3653). صحيح مسلم (4/ 1854) (2381). شرح صحيح مسلم (149/15). فتح الباري (11/7). كنوز رياض الصالحين، لمجموعة من الباحثين (276/2) شرح رياض الصالحين لابن عثيمين (563/1).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
SIRA DA TARIHI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com