Tsallaka zuwa abin da ke ciki
Hadisai tare da sharhi

Lallai ni ba'a aikoni mai yawan tsinuwa ba, kaɗai an aikoni ne dan in zama rahama

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قِيلَ: يَا رَسُولَ اللهِ ادْعُ عَلَى المُشْرِكِينَ قَالَ: «إِنِّي لَمْ أُبْعَثْ لَعَّانًا، وَإِنَّمَا بُعِثْتُ رَحْمَةً».
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Aka ce: Ya Manzon Allah ka yi wa mushrikai mummunar addu'a ya ce: "Lallai ni ba'a aikoni mai yawan tsinuwa ba, kaɗai an aikoni ne dan in zama rahama".
Muslim ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi

An nemi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa mushrikai mummunar addu'a, sai ya ce: Lallai cewa ni ba'a aikoni daga Allah in zama mai yawan tsinuwa ba ina yi wa mutane mummunar addu'a da nisantarwa da kuma korewa daga rahamar Allah sai in yanke su daga alheri, lallai ni ba'a aikoni dan haka ba, kaɗai an aikoni ne dan in zama sababin alheri da kuma rahama ga mutane baki ɗaya, da kuma muminai a keɓance.

Fa’idoji
  1. Cikar ɗabi'unsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  2. Muhimmancin tsaftace harshe daga zagi da tsinuwa dan koyi da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
  3. A cikinsa akwai hani daga tsinuwa.
  4. Kwaɗaitarwa akan jin ƙan mutane.
Madogara

صحيح مسلم (4/ 2006) (2599). المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (6/ 582). البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (40/ 683).

Wannan hadisi a HadeethEnc.com
TSARIN ANNABI

Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com