Lokacin rasuwar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai bar dirhami ko dinari ko bawa ko baiwa ko wani abu ba sai farar alfadararsa da makaminsa, da wani filin da ya maida shi sadaka
Daga Amr Ibul Haris ɗan uwan mai dakin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ɗan uwar ummul muminina Juwairiyya Bintul Haris - Allah Ya yarda da su -, ya ce: Lokacin rasuwar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai bar dirhami ko dinari ko bawa ko baiwa ko wani abu ba sai farar alfadararsa da makaminsa, da wani filin da ya maida shi sadaka.
Bukhari ne ya rawaito shiDarajaIngantacce ne
Sharhi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya rasu bai bar dirhamin na azirfaba ko zinari ba, ko bawan da ya mallaka ko baiwar da ya mallaka ko raƙumi ko wani abu na dukiyaba, sai kawai farar alfadararsa wacce yake hawanta, da wani filin da ya bar shi waƙafi a lokacin da yake da lafiya saboda matafiya.
Fa’idoji
Annabawa ba'a gadarsu.
Bayanin abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bari bayan mutuwarsa.
(Annabi) tsira da amincin su tabbata agare shi ya rasu amma bai bar wani abin da yake da kima ba, saboda kyautarsa da kuma ciyarwarsa da kuma kyautatawarsa.
Karmani ya ce: Wakilin suna a cikin faɗinsa (kuma ya sanyata) mai komawa ne ga duka ukun wato alfadarar da makami da fili bawai zuwa filin kawai ba.
Al-Khitn: Ɗan'uwar mata, al-Ukhtani kuma ta ɓangaren mace.
Madogara
صحيح البخاري (4/ 2) (2739).
النهاية في غريب الحديث والأثر (254).
فتح الباري لابن حجر (5/ 360).
عمدة القاري شرح صحيح البخاري (14/ 31).
Kowane hadisi, daraja, sharhi da fa’ida a nan an nuna su daidai yadda HadeethEnc.com ke wallafa su, bisa sharuɗɗansa na sake wallafawa. Darajar ba ta ambaci wanda ya yanke hukuncin ba. Fassarorin da sharhohin na mawallafansu ne, kuma wasu suna bayyana hukunce-hukunce; masu bitar Sabīl ba su duba su ba. Hadisin Larabci shi ne nassin. Tushe: HadeethEnc.com